Rahotanni daga jihar Kaduna suna bayyana cewa gamayyar wasu jiga-jigan jam’iyyar APC tare da hadakar gamayyar wasu jiga-jigan yan siyasa daga Kaduna sun dunkule waje daya domin kayar da Gwamna mai ci a jihar, Nasir El-Rufai a 2019
Hausa Times ta ruwaito gamayyar jiga-jigan yan siyasar sun gudanar da taron sirri yau Alhamis a Abuja domin tattauna batun.
Wani da ya shaida taron, Nura Unman ya shaidawa Hausa Times cewa yan siyasar sun kafa kwamiti mai karfi da zai yi nazari domin ya fito da dan takara gogagge da zai iya kayar da Gwamnan a zaben 2019.
Hausa Times ta kuma ruwaito daga cikin manyan wadanda ake tunanin zasu yi tasiri idan sukayi takara da mista El-Rufai sun hada da Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, da Sanata Othman Hunkuyi da Isah Ashiru
Sai dai bayanai sunce ba lallai a tsaida kodaya daga cikinsu ba, domin ana iya dauko wani na daban da zai samu karbuwa ga Al’ummar jihar don a samu a cimma burin hana El-Rufai zarcewa
Gamayyar yan siyasar Kaduna dake adawa da Gwamnan
Wani da ya shaida zaman ya shaidawa Hausa Times cewa ‘Wani daga cikin wadancen da aka lissafo suyi takara ya fito karara yace shi bai ma damu da takarar ba, babban burinshi shine a kawar da El-Rufai a mulki a 2019.
Gwamna El-Rufai dai na fuskantar adawa daga yan siyasar jiharsa ciki har da yan cikin jam’iyyarsa ta APC har takai ga sun bayyana janyewa daga Gwamnatinsa a inda suka kafa APC Akida da ‘Kaduna Restoration Group’ da dai sauransu, har wasu daga cikinsu suna da nasanin mara masa baya yaci zabe a 2015, wasunsu kuma har suna bawa Al’ummar jihar hakuri bisa tallata masu shi da sukayi a 2015 din.
Gwamna El-Rufai dai yayi kaurin suna wajen aiwatar da manufofi da kudurori a jihar Kaduna wadanda ke jawo masa bakin jini amma kuma baya nuna damuwa akai, cikin kudurorin da ya kawo na baya bayan nan shine batun korar malaman firamare fiye da dubu 20 da suka kasa cin jarabawar gwaji.
Kodayke dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya goyi bayansa a wannan shiri to amma batu korar malamain yana tayar da kura.
Ansha yada rade-radin cewa Gwamnan a 2015 yace ba zai sake yin takara ba domin ‘jahili ke maimaita aji’
El-rufai yace batun korar malamai ba ja da baya
Sai dai a kwanakin baya ne Gwamnan ya fito karara ya bayyana aniyarsa ta neman zarcewa, a inda a wajen hirar kai tsaye da yan jaridu a gidan Gwamnatin jihar aka jiyo Gwamnan na cewa ‘Shugaba Buhari zai tsaya takara a 2019 saboda haka shugaban kasar ya bukaceshi shima ya fito takarar Gwamnan Kaduna karo na Biyu a zaben 2019
Malamai suna zanga zangar nuna adawa da shirin Gwamnati na korarsu
Sai dai a zamansu na yau gamayyar yan siyasar wadanda suka hada har da yan sauran jam’iyyun adawa sun sha alwashin dunkulewa su marawa duk dan takarar da Kwamitin nasu ya tsayar takara domin su hana mista El-Rufai zarcewa a zaben 2019
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment