Buhari Ya Yabawa Mabiya Darikar Tijjaniyya Kan Zaman Lafiya - NewsHausa NewsHausa: Buhari Ya Yabawa Mabiya Darikar Tijjaniyya Kan Zaman Lafiya

Pages

LATEST POSTS

Saturday, 25 November 2017

Buhari Ya Yabawa Mabiya Darikar Tijjaniyya Kan Zaman Lafiya



Shugaba Muhammad Buhari ya yabawa mabiya darikar Tijjaniya kan yadda suke tafiyar da harkokinsu cikin lumana da zaman lafiya inda ya nemi hadin kansu wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Buhari ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da Shugaban Kungiyar Tijjaniya ta Duniya, Sheikh Muhammad Kabir ya ziyarce a fadarsa da ke Abuja inda ya nuna cewa darikar Tijjaniya ba ta da alaka da wata kungiyar ta'addanci sannan kuma tana da sassaucin ra'ayi game da harkokin addini.

Da yake nasa jawabin, Khalifa Muhammad Kabir ya ce su ziyarci Nijeriya don halartar bikin Mauludin wannan shekara inda ya yabawa Shugaba Buhari kan yadda ya samar da hadin kai a tsakanin addinan kasar nan.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment