Dan Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Rasu Sakamakon Daba Masa Wuka Da Matarsa Ta Yi A cikin Hotuna - NewsHausa NewsHausa: Dan Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Rasu Sakamakon Daba Masa Wuka Da Matarsa Ta Yi A cikin Hotuna

Pages

LATEST POSTS

Sunday 19 November 2017

Dan Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Rasu Sakamakon Daba Masa Wuka Da Matarsa Ta Yi A cikin Hotuna



Dan gidan tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Bilyaminu Halliru Bello ya gamu da ajalinsa a daren jiya Asabar sakamakon daba masa wuka da matarsa Maryam Sanda ta yi. Bayan ta ci karo da sakon da wata ta turo masa a waya.

Maryam wadda 'ya ce ga tsohuwar shugabar bankin Aso, Hajiya Maimuna, ta dabawa mijin nata wuka har kusan sau uku ne a baya sannan kuma ta yi masa rauni da wukar a mazakutarsa.

Lamarin wanda ya faru a gidan ma'auratan dake Maitama a Abuja, rahotanni sun nuna cewa yanzu haka Maryam tana tsare a sashen binciken manyan laifuka na rundunar 'yan sandan Abuja.
Ga hotunan margayi Bilyaminu da matarsa:-





Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment