HAUSAWA na cewa rana ba ta karya, sai dai uwar diya ta ji kunya. Allah cikin ikon Sa Ya nuna mana ranar da fitacciyar jaruma Hauwa Maina ba ta ji kunya, wato ranar auren babbar diyar ta, Maryam Bukar Hassan.
An dauren Maryam da Umar Ahmad a ranar Juma'a, 25 ga Agusta, 2017 a wani masallaci mai suna An-Nur da ke Abuja, bayan an idar da sallar Juma'a. An daura auren a kan sadaki N50,000.
Da misalin karfe 2:00 na rana kuma an yi wani gagarumin biki, wanda ake kira da suna lancin, a wani kayataccen wuri mai suna A-Class Park & Events Centre da ke Titin Kashim Ibrahim, a Maitama, Abuja.
Tun kafin ranar, mahaifiyar amarya ta shirya bikin ranar al'ada (Cultural Day), wanda aka yi a ranar Asabar, 19 ga Agusta a wani dakin taro mai suna Ceremonial Canopy da ke Rimi Drive, Unguwar Rimi, Kaduna.
An fara bikin da misalin karfe 5:30 na yamma. Mawaki El-Bash Muhammad shi ne kadai mawakin da ya halarci bikin. Wannan ne ya ba shi damar cin karen sa babu babbaka.
Wani abin mamaki shi ne duk da ya ke Hauwa Maina fitacciya ce a industiri, amma 'yan fim da yawa ba su halarci bikin ba, sai kalilan.
Wadanda su ka halarta sun hada da Ali Nuhu, Fatima Lamaj, A'isha ZIAU da mijin ta Yusuf Maina, sai Ibrahim Danguzuri, Abubakar Hunter, Mudassiru Barumi, A.A. Rasheed Kabala da Karima Dikko.
A wurin, wakilin mu ya ji wata furodusa ta na fadin, “Inda Ali Nuhu ya bambanta da sauran kenan.” Ta ce tun kafin ranar bikin ya ke kira ya na tambaya yaushe bikin? Kuma sai ga shi ya cika alkawari.
An tashi daga bikin da misalin karfe 9:00 na dare.
. Kawayen Hauwa Maina su na yi mata liki
Haka kuma a ranar Lahadi, 20 ga Agusta, an yi bikin ranar iyaye mata (Mothers Day) wanda aka yi a babban dakin taro na Ahmadu Bello Sardauna Memorial Foundation da ke Titin Race, daura da Dandalin Murtala, Kaduna.
An fara bikin da misalin karfe 7:00 na yamma. A nan ma mawaki El-Bash Muhammad ne ya baje kolin sa.
Iyayen amarya da na ango sun cashe, an kuma ci an sha. Ita ma mahaifiyar amarya ba a bar ta a baya ba, domin kuwa ta rangada wa 'yar tata wakar bankwana da yaren su na Babur. Ta na fara rera wakar, sai kuma ta fashe da kuka. Nan da nan 'yar ta zo ta na lallashin ta.
An tashi daga bikin da misalin karfe 10:00 na dare.
Tuni dai Maryam ta tare a gidan mijin ta.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment