Dalilin da ya sa har yanzu ba mu yafewa Rahama Sadau ba – MOPPAN - NewsHausa NewsHausa: Dalilin da ya sa har yanzu ba mu yafewa Rahama Sadau ba – MOPPAN

Pages

LATEST POSTS

Sunday 19 November 2017

Dalilin da ya sa har yanzu ba mu yafewa Rahama Sadau ba – MOPPAN


Kungiyar masu shirya fina finai ta kasa sashin jihar Kano MOPPAN, ta bayyana hujjar ta na kin yafewa jaruma Rahama Sadau har yanzu duk kuwa da cewa ta aiaka da wasikar ban hakuri bisa laifin da ta aikata da ya kai har ga korar nata.

Sakataren kungiyar, Salisu Mohammed ya bayyana cewa har yanzu basu samu zama sun tattauna akanal’amarin jarumar ba.

A cewar sa laifin da Rahama ta aikata ba karami bane saboda haka bazasyi gaggawan yafe mat aba saboda kawai ta rubuta wasikar neman afuwa.
Wani jami’in kungiyar daban da ba a bayyana suna shi ba ya ce ba lallai ne kungiyar ta yafewa Sadau ba.

A cewar shi “Ta fadi abubuwa da dama, har sai da ta karyata cewa mun dakatar da ita. Ba ni da tabbacin za a bari ta kara dawowa Kannywood”
Ya ci gaba da cewa “Ta sha cewa ita ta ci gaba da rayuwar ta, toh dalilin me ya sa a yanzu ta ke son dawowa? Ba mu son lalataccen kyau daya ya lalata sauran”

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment