Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai yiwu a ce malamin da ya kasa cin jarrabawar dalibinsa ya ci gaba da koyar da dalibin ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wani babban taro kan ilimi wanda aka yi a Abuja ranar Litinin.
A watan da ya gabata ne dai gwamnatin jihar Kaduna ta yi wa malaman jarrabawa irin ta 'yan aji hudu na firamare.
An dai yi wa malamai fiye da 33,000 jarrabawar, amma kamar yadda gwamnati ta ce, kaso biyu bisa uku na malaman ba su iya samun kashi 75 cikin 100 ba, bayan da sakamakon jarrabawar ya fito.
Shugaba Buharin ya ba da labarin yadda ya yi karatu lokacin da yake maraya.
"Na kasance maraya lokacin da nake yaro, har yanzu na yi amannar cewa duk abin da na yi a rayuwa ya ginu ne daga rayuwata a makarantar kwana.
"Na yi shekara tara a makarantar kwana, shekara uku a firamare, shida a sakandare," in ji shi.
Ya ci gaba da cewa: "A wadancan shekarun, malamai suna daukar dalibansu tamkar 'ya'yansu. Idan ka yi daidai za su fada maka, idan ma ka yi ba daidai ba kuma za ka sha na jaki."
Buhari ya ce bayan da ya kammala makaranta da gangan ya ki ya yi aikin gwamnati, ya shiga aikin soja.
"Na taba jin wani dan Najeriya wanda nake girmamawa, ya ce bayan ya samu horo a Najeriya da kuma Amurka, ya koma makarantar firamaren don ya ba da gudunmuwa. Amma sai ya kasa bambancewa tsakanin dalibai, yara da kuma malamai.
"Abin da el-Rufa'i yake kokarin yi yanzu, daidai yake da abin da wancan mutumin ya fada min shekara 10 da ta gabata. Ba zai yiwu a ce malamin da ya kasa cin jarrabawar dalibinsa ya ci gaba da koyar da dalibin ba. "
Batun korar malaman da gwamna el_Rufa'i ya yi ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a NAjeriya, inda wasu da dama ke nuna goyon bayansu kan hakan, wasu kuma ke ganin bai dace a raba mutane da hanyar samun abincinsu ba.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment