Sabbin Bayani Sun Bayyana Game Da Kashe Bilyamin Da Matarsa Ta Yi - NewsHausa NewsHausa: Sabbin Bayani Sun Bayyana Game Da Kashe Bilyamin Da Matarsa Ta Yi

Pages

LATEST POSTS

Monday, 20 November 2017

Sabbin Bayani Sun Bayyana Game Da Kashe Bilyamin Da Matarsa Ta Yi



Daga Muhammad Ismail Ali

Wani abokin marigayi Bilyamin Muhammed Bello, wanda ya gamu da ajalinsa a hannun matarsa Maryam Sanda a daren Asabar 18 ga watan Nuwamba, Habib Gajam ya bayyana yadda lamarin ya auku.

Majiyarmu ta ruwaito Gajam yana fadin cewa bai taba ganin tashin hankali a rayuwarsa ba tare da rashin kunya irin wanda ya gani a kisan Bilyaminu.

Gajam yace rikicin ya samo asali ne da misalin karfe 9 zuwa 10 na daren Asabar, a gidan ma’auratan, inda Maryam ta bukaci Bilyamin ya sake ta, idan ba haka kuma zata yanke masa mazakuta, wanda hakan ya sa abokinsa Ibrahim Aliero shiga tsakaninsu har sau hudu, a lokacin da Maryam tayi yunkurin caka masa wuka.

Ganin yadda lamarin ke neman yin kamari,  hakan yasa Ibrahim Aliero kiran wani kawun Maryam, mai suna Auta, sa’annan ya kira wani dan uwan Bilyamin, mai suna Abba, don su zo su shiga tsakanin ma’auratan.

Ana cikin zaman jiransu, sai Maryam ta fasa kwalban gyada, ta taso ma Bilyamin zata kashe shi da kwalbar, amma sai Bilyamin ya rike hannuwanta, har ya ji ciwo a hannusa, sannan kuma ta cije shi a yatsan hannu.

Ba da dadewa ba sai Kawunta Auta ya iso gidan, inda ya ja hankalinsu, tare da yi musu nasiha, nan take dukkaninsu suka amince masa da zasu zauna lafiya, daga nan yayi tafiyarsa, inda shima Ibrahim ya raka Bilyamin zuwa wani shagon magani, aka duba masa hannunsa da Maryam ta cije shi, sa’annan suka garzaya ATM ya cira kudi, don biyan kudin gyaran motar Matar tasa.

Sai da misalin karfe 11 na dare suka koma gida, inda Ibrahim ya cigaba da zama da ma’auratan har zuwa karfe 12 na dare, yana basu hakuri tare da tausan su, daga nan ya tashi ya nufi gida.

Kwatsam da misalin karfe 2 na ranar Lahadi, sai aka gayyace su zuwa asibitin Maitama, inda Bilya ke kwance rai kwafai mutu kwafai, jini ta ko ina, ga saran wuka a kirjinsa, kafada, cinya, da shaidan hakori a cikinsa.

Gajam yace Maryam ta amsa laifinta a Asibiti, amma da aka je Caji Ofis sai labari ya sha bam bam, inda yace Maryam tace ita ba ita ta kashe Bilyamin ba, a sanadiyyar fadar da suka yi ne ya yanke da tukunyar shisha, wanda hakan ne ya yi sanadiyyan mutuwarsa.

Da aka je gidan su, inda lamarin ya auku, kamar yadda kwamishinan 'Yan sanda ya umarta, sai aka tarar dad akin a share tsaf tsaf, ta wanke jinin daya zuba, ta yar da makamin da tayi amfani dasu, sannan ta fasa tukunyar shishan da tukunyar fulawan dake dakin.

A yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin.

Ku kasance da hausaloaded.com domin jin tabbacen yadda al'amari ya kasance

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment