Yanzu Aka Fara Kashe Maza Ga Dalilaina Kamar hakar inji Fauziya Suleman - NewsHausa NewsHausa: Yanzu Aka Fara Kashe Maza Ga Dalilaina Kamar hakar inji Fauziya Suleman

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 22 November 2017

Yanzu Aka Fara Kashe Maza Ga Dalilaina Kamar hakar inji Fauziya Suleman


Idan har al'umma da manyan mu za su ci gaba da satar kudin talakawa suna ciyar da yayansu da biyan karatunsu suna barin talakawa da yunwa yanzu aka fara. Idan har neman auranmu hausawa bai sauya daga yanda muke barin kudi da nuna tsiraici da aure don abin duniya ba yanxu aka fara.

  Idan mata ba su tarbiyya me kyau ba suka fifita ilimin zamani da samun tarbiyya daga iyayan da ba su san tarbiyya ba sai son yaya ba yanxu aka fara.  Idan masu kudi da talakawanmu ba su koma kan tafarkin koyarwa Manzon Allah ba yanxu aka fara.  Idan mamanmu ba su yadda cewar karin aure umarnin Allah ba ne su koyi halattaccen kishi irin na matan sahabbai ba yanzu aka fara.  

Idan har mamanmu ba su daina chatting din banza da Matan banza da sunan wayewa da nuna tsiraicin Juna ba yanzu aka fara. 

 Idan har mata ba su guji duba wayoyin mazan su ba, su kuma mazan ba su ji Tsoron Allah gurin yin chatting da abin da Allah ya haramta musu don suna takamar ana cewa kar mata su taba wayar su ba yanzu aka fara. 

Allah ya shiryemu da zuri'armu ya sauya mana tinanin akan wanda muke yanzu na fifita wayewar bature fiye da addininmu.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment