Dalilin da yasa yin wasan Hausa da yaren turanci keda muhimanci - jaruma Fati SU - NewsHausa NewsHausa: Dalilin da yasa yin wasan Hausa da yaren turanci keda muhimanci - jaruma Fati SU

Pages

LATEST POSTS

Saturday, 25 November 2017

Dalilin da yasa yin wasan Hausa da yaren turanci keda muhimanci - jaruma Fati SU


Jarumar wasan Hausa Fati SU ta ce shawarar da abokan sana'ar ta suka yanke na yin shiri da yaran turanci abu ne mai muhimmanci kuma tayi maraba da hakan.

Fati ta bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da gidan jaridar Premiumtimes ranar Asabar.

Fati ta ce "Na san ba wai turanci muka iya sosai ba amma idan muna yi shiri da turanci hakan zai bamu damar govewa da yaren ".
Da take yin tsokaci a kan rata ta fuskar kayan aiki da kamfanin shirya fina-finai na kudu da yayi wa kamfanin Kannywood, ta ce "Eh haka ne amma mu ma fa yanzu muna kokari kuma yin fina-finai cikin harshen turanci zai kara sada mu da manyan kamfanoni da suka fi mu gogewa kuma mu ma jaruman mu zasu fara samun kyauta daga kungiyoyin shirya fina-finai ta kasa".

Fati ta bayyana cewar su 'yan koyo ne da suke son kara fadada yada al'adar bahaushe ta hanyar yin shiri da yaren turanci. Yin hakan ma zai kara mana magoya daga dukkan kabilu daga fadin Najeriya.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment