Malamin addinin ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai wa BBC a ofishinmu da ke Landan ranar Alhamis
.
Ya ce ya fuskanci cewa an bar iyaye mata a baya kuma ba a cika mayar da hankali a kan wa'azin mata ba, a cewarsa.
Ya ce "ko da an yi wa'azi a kan matan, yawanci bai wuce a ce an rataye wata a wuta ba ko kuma malamancin haka, maimakon a tsaya a koyar da su koyarwar addinin Musulunci da kuma yadda za su bauta wa Allah Ubangiji Madaukakin Sarki."
Sheikh Kabiru Gombe ya ce wa'azantar da mace ko ilmantar da ita ya fi muhimmanci a kan na namiji, "domin ita mace makaranta ce guda saboda ita uwa ce kuma ita ce mai tarbiyantar da yara."
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment