Daga Hamisu Nasidi Baban Awwab
Kiran ya fito ne daga Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatissunnah ta tarayyar Naijeriya Shiekh Abdullahi Bala lau a wata tattaunawa ta musamman da yayi da Gidan rediyon BBC Hausa a birnin London.
Sheikh Bala Lau yayi kira ga hukumomi da su Gaggauta Hukunta matar nan mai suna Maryam da ake zargin ta kashe mijinta Bilyaminu in har an sameta da laifin.
Sheikh Lau yace yin hukunci da tabbatar da adalci ne kadai zai kawo karshen irin wannan mummunan lamari a tsakanin mutane.
A nasa bangaren Babban Sakataren kungiyar ta Izala sheikh Kabiru Haruna Gombe ya ja hankalin mata akan suji tsoron Allah su kuma yarda da hukuncin da Allah Yayi na cewa Namiji ya Auri mata hudu in zai iya rikesu bisa ga adalci.
Ya kara da cewa in har irin wannan mummunan lamari ya cigaba da faruwa toh karshe matan ne zasu fada cikin matsala domin mazaje zasu dena auren su. Ita kuma mace Allah yayi tane domin ta jingina sannan ne zata samu rayuwa mai kyau.
Malaman sun kai ziyara kasashen Turai ne domin amsa gayyatar Da'awa domin gudanar Da'awa.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment