Fim din na Shu'uma na koya darasi ne kan mummunar makomar miyagun mutane.
A hirarta da Nasidi Adamu Yahaya , Fati ta ce tana matukar son taka rawa a matsayin "muguwa" a fina-finai.
"Na fi so na fito a matsayin muguwa saboda na fadakar da mutane irin illar mugunta da son rai.
"Ka san yawancin jarumai sun fi son fitowa a matsayin masu kirki, amma ina ganin hakan ba ya aikewa da sako kai tsaye kamar jarumi mugu, wanda ake nuna karshensa bai yi kyau ba", in ji jarumar.
Fati, wacce ta soma fitowa a fina-finan Kannywood a shekarar 2010, ta kara da cewa "Na fito a fina-finan mugunta irinsu Shu'uma da Sai Na Auri Zango da Baya Da Kura da Basma da sauransu".
A cewarta, fim din Basma ne ya fi ba ta wahala "saboda yarinyar da aka hada ni fim da ita, wacce ba ta wuce shekara bakwai ba, shi ne fim dinta na farko, don haka idan na kai mata mangari ko naushi takan ji kamar da gaske ne sai ta tsorata.
"Don haka sai da aka rika sake daukar fim din sau da dama kafin a gama shi".
Jarumar, haifafiyar jihar Bauchi, ta bukaci masu kira a gare ta ta yi aure da su yi mata addu'a, tana mai cewa "idan Allah ya nufa sai ka ga an yi, don haka lokaci muke jira. Amma ina da wanda zan aura".
Fati Abubakar ta ce tana so a hada ta fim da ubangidanta Adam A. Zango da kuma Jamila Umar (Nagudu) saboda suna burge ta "kuma hankalina a kwance yake idan ina tare da su".
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment