Yanda wannan budurwar ta ja ra'ayin wani musulmi ya koma addinin kirista - NewsHausa NewsHausa: Yanda wannan budurwar ta ja ra'ayin wani musulmi ya koma addinin kirista

Pages

LATEST POSTS

Sunday 26 November 2017

Yanda wannan budurwar ta ja ra'ayin wani musulmi ya koma addinin kirista

Yanda wannan zankadediyar budurwar ta ja ra'ayin wani musulmi ya koma addinin kirista


Wannan budurwar me suna Caramella Mou tayi ikirarin cewa wai ta mayar da wani musulmi kirista, tace mutumin yana tukin motar hayane, suka hadu har ta samu nasarar jan ra'ayinshi yabar addinin shi na musulunci zuwa addinin kiristanci.

Ta kara da cewa ya mata alkawarin ranar Lahadi zaije coci kuma zai taimaka a gina cocin.


Ta kuma ce akwai mutane da yawa da suke cikin bata kuma suna bukatar wanda zai iya jajircewa ya gaya musu gaskiya.
A karshe tayi kira ga 'yan uwanta mabiya addinin kiristanci da su mike tsaye domin aikin da ya kamata ace sunayi kenan (na mayar yiwa mutane wa'azi dan su koma addinin kiristancin).



Tun bayan data wallafa wannan labarai nata a dandalin sada zumunta da muhawara na Twitter, sai labarin nata ya dauki hankalin mutane akayi ta mayar da martani kala-kala.

DAN ALLAH TURA WANNAN LABARIN A FACEBOOK KO WHATSAPP

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment