Premium Times ta ruwaito kashi biyu bisa ukun Malaman sun fadi jarabawar, wato kimanin 22,000 kenan daga cikin Malamai 33,000 dake koyarwa a kafatanin Makarantun Firamarin jihar Kaduna.
Da wannan ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya sha alwashin sallamarsu daga aiki, tare da diban wasu sabbi guda 25,000 da suka dace, don koyar da daliban jihar Kaduna.
Sai a wani mataki na taimaka ma wadanda za’a sallama, shugaban hukumar ilimin bai daya, SUBEB,Nasiru Umar ya bayyana a ranar Lahadi 5 ga watan Nuwamba cewa Malaman na da damar neman a sake maka jarabawar tasu.
Haka zalika shugaban na SUBEB, yace daga cikin Malaman da za’a sallama, duk wanda ya kwashe sama da shekaru biyar yana aiki, toh za’a bashi damar yin ritaya daga aiki, don ya mori kudaden da duk ma’aikaci mai ritaya zai mora, amma duk masu kasa da shekaru biyar basu da wannan dama, sallama ce kawai.
Bugu da kari, an baiwa dukkanin wadanda abin ya shafa damar sake neman aiki, cikin Malamai 25,000 da za’a dauka, kuma wadanda suka fadi za’a sanar dasu wata uku kafin lokacin barin aiki,kamar yadda majiyar NAIJ.com ta jiyo shugaban SUBEB yana fadi.
Sa’annan ya shawarci duk wanda basu gamsu da sakamakon jarabawar da suka yi ba, dasu je gaban kwamitin dake sake makin jarabawar, don su tabbatar da an yi musu adalci.
“Zuwa yanzu, mun samu masu takardun neman aikin Malantar guda 13,000 a ofishin SUBEB, wasu kuma sun aika takardunsu zuwa ofisoshin kananan hukumomin su. ba zamu dinga raba aikin Malanta ba kamar yadda ake yi a baya ba.” Inji Nasiru.
A cewar SUBEB, duk wasu masu ruwa da tsaki a harkar Ilimi sun sa hannu cikin wannan jarabawa da aka shirya, kamar su kungiyar malaman ta kasa, hukumar shirya jarabawar WAEC da NECO, Jami’ar jihar Kaduna, don haka ya koka kan yadda wasu ke neman siyasantar da lamarin.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment