October 2017 - NewsHausa NewsHausa: October 2017

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 31 October 2017

Wata Sabuwa Soyayya Ba Tabbas Ya bashi kyautar mota bayan yayi ma matarsa ciki

Wani dan Nijeriya ya bada ƙyautar mota ga wani dan ƙasar Afrika ta kudu bayan yayi wa matar sa ciki.

A bisa labarin da wana kafar yada labarai dake kasar afrika ta kudu , dan Njeriyan mai suna John yace fushin mijin ya sauka bayan ya bashi kyautar katafaren motar.

"Na san abun da na aikata ba daidai bane amma naji dadi da ya amshi kyautar da na bashi. Ya yarda cewa matar sa wanda take budurwata tana dauke da juna biyu kuma zata haifar mu da yaro"

"Yana dauke da facin rai amma da na mika masa kyuatar sai ya huce" inji John.
Wata yar uwan matar da aka yi ciki ta nuna facin ran ta ga mijin wanda ya amshi kyuatar motar kerar Marcedez benz G-wagon.

"Yan Nijeriya baza su taba daukan mazan mu da daraja. Ta yaya mutum zai amshi kyuata daga wanda yayi ma matar sa ciki? hakika zai kara aikata hakan kuma ya kara siya ma dakikin miji sabon mota. Gaskiya ya bata mun ra i" tace.
Shidai mijin wanda ke tsakiyar kwamacalar yayi tsokaci game da lamarin inda yace sun daidaita ne cikin aminci.

"Kira na da sakarai bai dace ba, hakikani gaskiya baza mu iya sauya abun da ya faru, mun tattauna ne a matsayin mu na maza domin samun matsaya.
"na yafe mai, tun ba yau ba nake mafarkin samun irin wannan motar kuma gashi ya zo mun a sauwake.

"Za'a haifi yaron kuma zan kula da shi tamkar nawa amma idan uban yana son daukan shi zuwa kasar sa Nijeriya ba zan hana shi ba. Zan cigaba da kula da matata domin ina mai matukar son ta. Ni dai ba zan rabu da ita ba domin ta samu juna biyu, ba haka aure yake ba" yace.

VIDEO HIGHLIGHTS: AS Roma 3-0 Chelsea (UEFA Champions League)

Stephan El Shaarawy’s first-half brace set Roma on the way to a resounding 3-0 win over Chelsea that displaced their visitors at the top of Champions League Group C.

Antonio Conte’s reigning Premier League champions would have secured a last-16 spot with a win but that appeared a tall order from the moment El Shaarawy opened the scoring after 39 seconds.

Download Highlights

Fim:- Download Complete Mijin Yarinya Fim 1 &2 And 3 & 4 Lastest Hausa Fim 2017

Saukar da wannan sabon shirin fim mai suna "mijin yarinya" wanda a gaskia ni kalli wannan video kuma ya burgeni sosai wanda ya samu shahaharren yan wasa tsofaffi da kuma yara jaruman da a cikin wannan fim sune kamar haka

Maryam yahya

Bashar na yaya

Aminu shariff momo

Shamsu Dan iya

D.s

Wanda ya bada umurmin shirin shine Ali Gumzak (sak)



Mijin Rarinya 1 and 2


Download Video Now

Mijij Yarinya 3 and 4

Download Video Now

Abin da Buhari ya shaida wa shugabannin APC

Ranar Talatar yau ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Shugabannnin Kwamitin Zartaswa na jam’iyyar APC jawabi dangane da abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar.
Ga cikakken jawabin da ya yi musu nan PREMIUM TIMES HAUSA ta fassara wa masu karatun ta:

FASSARAR JAWABIN SHUGABA MUHAMMADU BUHARI A TARON SHUGABANNIN KWAMITIN ZARTASWA NA JAM’IYYAR APC, A RANAR TALATA, A ABUJA

Bayan Gaisuwa,
Bari na fara da yi wa kowa lale marhabin da zuwa wannan muhimmin taro na shugabannin zartaswar jam’iyyar mu.
Sannan kuma ina mai yin godiya gare ku saboda addu’o’in da ku ka rika yi min da fatan alherin da ku ke yi min, wanda Allah cikin ikon sa ya amsa addu’o’in ku ta hanyar dawo min da lafiya ta, har na murmure.

Zan kuma mika gaisuwa da godiya ta ga shugabannin jam’iyya dangane da jajircewar da su ka yi wajen taimaka wa tafiyar gwamnatin mu a lokacin da na yi dogon hutun jinya.
Bari na fara da yin dan bayani kan shugabancin jam’iyyar mu, a bisa jagorancin Mai Girma Chief John Oyegun. Na yi aiki tare da shi, inda muka kusanci juna tun a cikin 1984 zuwa 1985. Abin farin ciki a nan, sai kaddara ta sake hada mu tare mu na shugabanci yaunzu a wannan kasa.

Ina mika godiya ga Cif John Oyegun da ma’aikatan da ke karkashin sa, bisa kokarin su na gudanar da kyakkyawan jagorancin jam’iyya a cikin shekaru biyu da rabi.

Tilas ne kuma na yaba wa shugabannin Majalisar Tarayya, a karkashin shugabancin Mai Girma Sanata Bukola Saraki da Mai Girma Kakakin Majalisa Yakubu Dogara. Tilas ba zan manta da hadin kan da na samu daga Majalisar Tarayya ba, ciki kuwa har daga bangaren masu adawa, wadanda su ka tanne zuciyar su daga nuna adawa mai dalili ko maras dalili, su ka bada gudummawa domin ci gaban kasa.

Godiya ta musamman ga Gwamnonin Jihohi wadanda su ka fuskanci babban kalubalen tabbatar da hadin kan al’ummar kasar nan. Wannan ya faru ne a daidai lokacin da haka kawai wasu su ka fito da hayaniyar siyasar da ta haifar da rikici saboda wasu munanan mafufofin su.
A dan kwarya-kwaryan jawabin da na yi a taron masu ruwa da tsaki da ya gudana jiya, na bayyana dalla-dalla wasu abubuwa na ci gaba da gwamnatin mu ta samar a bisa turbar daftarin alkawurran da jam’iyyar mu ta daukar wa jama’a a rubuce, da mu ka ce za mu gudanar musu idan mu ka yi nasara.

Za mu iya bugun kirji mu yi tutiya da irin gagarimar nasarar da mu ka samar a cikin shekaru biyu, a kan Boko Haram, Neja Delta, Wadatar Man Fetur, Karin Lantarki, Asusun Bai-daya, Harkokin Noma da Takin Zamani, da kuma uwa-uba jaddada cewa ba za mu laminci cin hanci da rashawa a kasar nan ba. Duk mun san da cewa yanzu dai an samu CANJI.
A yanzu dai daraja da martabar Najeriya ta nunka za mu, iya cewa kusan har ninki hudu.
Amma kuma duk da haka ba za mu shantake ba, saboda ina sane da babban kalubalen da ke gaban mu.

A shekarar da ta gabata na shaida muku cewa zan sake nada Mambobin Hukumomin Gwamnati. Ina matukar ba ku hakurin rashin samun damar yin haka, sakamakon wasu dalilai.
Wasu daga cikin mahalarta taron nan na sane da cewa an umarce ni tun a cikin 2015 da na yi wannan aikin sabbin nade-naden, to amma sai muka fuskanci tsaiko daga wasu kwamitoci masu yawa, domin a tabbatar an samu daidaito wajen yin nade-naden da nufin a tabbatar kowane yanki na kasar nan ya zamu wakilci daidai yadda ya dace.
A daya bangare kuma, ina sane da cewa mgoya bayan mu sun kagara su ga an yi wadannan nade-naden. Da yardar Allah za mu yi hakan nan ba da dadewa wa. Musamman ma ga shi a yanzu tattalin arziki na samun inganci, za mu samu halin kulawa da dukkan wadanda za a nada a dukkan hukumomin.

Haka nan kuma za a kara yawan ministoci domin a kara yawan hannayen daukar jinkar Gwamnatin Tarayya, ta yadda za a kara samun masu sabbin hikimomi da fasahar inganta al’amurran gwamnati.
Ina kara godiya a gare ku, dangane da jajircewar ku wajen sadaukarwa ga jam’iyyar mu kuma ina mai tunatar da ku cewa mu na kara bukatar karin kaimi daga gare ku nan da wattani masu zuwa. Ina fatan za mu ci gaba da dogaro da ku.

Idan mu ka ci gaba da tafiya a tsintsiya-madaurinki-daya, mu ka kau da kai daga rigingimu marasa tushe, dalili ko makama, to tabbas za mu kai ga nasarar CANJI a cikin kasar nan.
Ina yi muku fatan alheri.

Yan Matan Kannywood Ya Zamo Tilas Mu Ceci Kan Mu Da Kan Mu, Inji Wasila Isma'i

SHUGABAR kungiyar ’yan fim mata wadanda su ka yi aure, Hajiya Wasila Isma’il, ta bayyana cewa tilas ne matan industiri das u ka yi aure su kula da kan su ta fuskar tarbiyya, su taimaki kan su da kan su, domin kuwa duk abin da ’yan bayan su su ka yi, to zai iya shafar su.
Ta fadi haka ne a wani kwarya-kwaryan taro da kungiyar tasu ta gudanar a Kano kwanan nan.

Sun yi taron ne kamar yadda su ka saba yi a duk shekara, wanda su ka hada shi da shagalin bikin Babbar Sallah. Hakan ya bai wa fitattun jarumai mata da su ka dade ba su ga juna ba damar halartar taron.

Matan sun yi taron a ranar Litinin, 4 ga Satumba, 2017 a wani wajen shakatawa mai suna Green Park da ke Titin Ahmadu Bello a cikin garin Kano.
Tun da farko da ta ke jawabi a wajen, Wasila Isma’il ta bayyana matukar farin cikin ta a game da yadda mata ’yan fim su ka amsa gayyatar su da aka yi. A cewar ta, duk da cewar an yi taro har sau uku a baya, amma babu wani taro da jama'a su ka taru kamar wannan din.
“Haka alama ce da ke nuna manufar mu ta kafa wannan kungiya mai amfani ce, shi ya sa mata su ka amsa gayyatar da mu ka yi masu,” inji ta.

Ta ci gaba da cewa, “A farkon wannan kungiya, mun kafa ta ne don mata ’yan fim da su ka yi aure, ta yadda za mu rinka taimaka wa junan mu, to amma daga baya sai mu ka duba, akwai mata ’yan fim da su ka yi aure kuma auren nasu ya mutu, kuma su na bukatar taimako, don haka ne mu ka buda kungiyar ta zama ta matan aure da su ke gidan mijin su da kuma wadanda auren su ya mutu.

“Don haka ne a wannan taron za ku ga akwai mata da yawa da auren su ya mutu, kuma sun halarci wannan taron. Mun amince mu hadu mu yi tafiya da su, ta haka ne za mu san wadanda su ke da matsaloli kuma mu san hanyar da za mu bi mu tallafa masu, domin mun gano akwai da dama da aka sake su aka bar masu kula da yara.
“Wasu kuma mazajen su ne su ka rasu su ka bar su da yara, don haka akwai bukatar a tallafa masu.

“A yanzu a halin da ake ciki, mu ’yan fim mu na bukatar mu hada kan mu domin mu magance matsalar da ta ke damun matan da su ke cikin harkar fim saboda yadda ake kallon ’yan fim din, domin kada mu rika ganin mun yi aure mun bar harkar, to duk abin da na bayan mu su ka yi to zai shafe mu.
“Kamar maganar da ake yi na cewar ’yan fim ba sa zaman aure, to ni ga ni shekara ta goma sha biyar da aure ina tare da miji na, don haka maganar ’yan fim ba sa zaman aure ba gaskiya ba ne. Mutuwar aure idan ta zo a ko’ina ma ana yi, ba sai ’yan fim ba.”
Daga karshe, Wasila, wadda matar darakta Al-Amin Ciroma ce, ta yi kira ga mata ’yan fim da su ci gaba da kiyaye mutuncin su a duk inda su ka samu kan su.
Ita ma da ta ke jawabi, tsohuwar jaruma Saima Mohammed Raga ta kalubalanci wadanda su ke cewa ’yan fim ’yan iska ne, ta ce wannan ba gaskiya ba ne, domin idan mutum ya so lalacewa ba sai ya shigo harkar fim ba.

“Don haka mu sana’a mu ke yi, ba iskanci ba. Duk da ba za mu ce dukkan mu mutanen kirki ba ne, amma bai kamata a rinka yi mana kudin goro ba,” inji ta.

An dai yi jawabai da dama a wajen, sannan kuma an ware lokacin nishadantar da mahalarta taron inda aka tuna baya wajen saka tsofaffin wakokin finafinan jaruman da su ka hau wakar su na bin ta. Fati Mohammed ita ta hau wakar ‘Sangaya’, Rasheeda Adamu Abdullahi ta hau wakar fim din ‘Sa’a’, kuma duk da yake yanzu ta yi nauyi amma hakan bai hana ta yin rawa da juyi ba; Mansura Isah an saka mata wakar bikin su da Sani Danja.

A karshen taron, an cimma matsayar cewa za a samar da tallafi ga iyalan ’yan fim da su ka rasu, irin su Jamila Haruna, Hajiya Amina Garba (Mama Dumba), da sauran su.

Jarumar kannywood Aisha Tsamiya Za Ta Yi Karatu a Jami'ar NOUN



Ba mu yin Health Technology, inji jami'ar

Fitacciyar jaruma A'isha Aliyu (Tsamiya) ta bayyana cewa ta samu gurbin karo karatu a Budaddiyar Jami'ar Njeriya, wato National Open University of Nigeria (NOUN).
A wata hira da aka yi da ita a gidan talbijin na Arewa24, jarumar ta bayyana cewar za ta karanta kwas din 'Health Technology' ne.

A amsar wata tambaya da mai gabatar da shirin "Kundin Kanbywood", wato Aminu A. Shariff (Momoh), ya yi mata, A'isha ta ce, "Yanzu na samu admission a Open University... Ina so in karanci Health Technology."

To amma mujallar Fim ta gano cewa ba a yin wannan kwas din a jami'ar.
Daraktan Watsa Labarai na jami'ar, Malam Ibrahim Sheme, ya fada wa mujallar Fim cewa, "Health Technology bai cikin jerin kwasakwasan da wannan jami'ar ke gudanarwa. Amma kwas din da jami'ar ke yi wanda ya kusanci abin da A'isha Tsamiya ke so ta karanta shi ne 'Public Health'."

Daraktan ya ce ya ji dadin kudirin A'isha na zurfafa karatun ta, musamman a NOUN. Ya ce yin hakan ya nuna cewa ita mace ce mai hazaka tare da kokarin inganta rayuwar ta.
Ya ba ta shawarar cewa ya kamata ta zabi kwas din da jami'ar ke gudanarwa, kuma an lissafa su a gidan yanar jami'ar, wato www.nouedu.net.

Sheme ya yi kira ga sauran 'yan fim da su yi kokari su je jami'ar Open University domin su zurfafa karatun su. Ya ce karatu a NOUN ba sai sun bar ayyukan da ke gaban su ba, domin shi karatun daga ko'ina mutum ya ke zai iya yin sa.

"Ba sai mutum ya tafi aji ba yadda ake yi a sauran jami'o'i," inji shi. "Haka kuma akwai rage kashe kudi fiye da na sauran manyan makarantu."

Ita dai NOUN, ta na daga cikin manyan jami'o'in Gwamnatin Tarayya. Daliban ta sun fi na kowace jami'a yawa a duk fadin Afrika ta Yamma, ba ma Nijeriya kadai ba.

Monday 30 October 2017

Taƙaittacen Tarihin Sabuwar Jarumar kannywood Balkisu Abdullahi



Da farko dai za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatu.

BILKISU ABDULLAHI: To, assalamu alaikum. Ni dai suna na Bilkisu Abdullahi, kuma ni a garin Legas aka haife ni a shekarar 1993. Can na yi karatu na na firamare da sakandire, kuma daga baya na dawo Kano.

Harkar fim ce ta dawo da ke Kano?

A’a, ba harkar fim ce ta dawo da ni ba. Ni mahaifi na dan Kano ne, to kuma Allah Ya yi masa rasuwa, mahaifiya ta na auren wani mijin daban, don haka sai na dawo wajen dangin uba na da zama.

Ita mahaifiyar ki ’yar ina ce?

BILKISU: To ita mahaifiya ta Bafulatanar Yola ce ta Jihar Adamawa, amma dai yanzu ta na zaman aure a Legas. Tun baban mu ya na raye a can ta ke. To da ya rasu ma a can ta kara yin aure.

To yaya aka yi ki ka samu kan ki a harkar fim? Da man ki na sha’awa ko sai da ki ka zo Kano?

BILKISU: E, gaskiya da man ina sha’awa, don ina kallon finafinan Hausa tun ban kai ga haka ba kuma ina sha’awar abin, ya na burge ni sosai. Sai dai a lokacin ina ganin ba zan iya ba saboda ban san yadda zan hadu da masu yi ba, kuma ga shi ina karama.

Ta yaya aka yi ki ka samu kan ki a harkar fim?

Bilkisu: ni dai ba zan iya cewa ga lokacin ba sai dai na ce a cikin ’yan watannin nan na shigo, don ban dade da shigowa ba. Kuma dan’uwa na ne ya kawo ni ya gabatar da ni, daga nan aka kawo ni wajen Baba karami kuma a lokacin ya fara sa ni a cikin fim din sa mai suna ‘Dakin Duhu’, kuma shi ne fim din da na fara yi. Amma dai a yanzu an fara kira na ana sanar da ni finafinan za a yi kuma zan fito a ciki.

Wanne matsayi ki ka taka a fim din?

BILKISU: Na fito ne a matsayin kanwar jarumar fim din, sai mu ka hadu da wani saurayi a cikin A-daidaita-sahu, ya ce na ba shi lamba ta, na ce ai na fi karfin ajin sa, daga baya sai na gano mai kudi ne, sai kuma na zo ina yin da-na-sani.

Ba ki samu matsala a gida ba da ki ka shiga harkar fim?

BILKISU: Gaskiya babu wata matsala da na samu, don ita mahaifiya ta ma ta na son fim. Kuma duk wani abu da ake fada ma a kan ’yan fim ni da na zo ban gani ba.

 Kafin ki shigo harkar fim ki na jin labarin ’yan fim ne, kuma ko da kin gan su ma sai dai gani daga nesa. Yanzu da ki ka hadu da su ki ka gan su, yaya ki ka ji?

BILKISU: Gaskiya na ji dadi sosai. Da, ina ganin abin ma kamar a mafarki, na ga Ali Nuhu da Adam A. Zango duk mun yi magana da su; amma yadda ake ta bada labarin su na da girman kai ni ban gani ba. Mun yi magana da su sosai.

Ke sabuwar jaruma ce. Da a baya zama ki ke yi kawai ki na kallon fim a yanzu da ki ka fara yaya ki ka ji yadda harkar ta ke?

BILKISU: To, (dariya) gaskiya ’yan fim su na kokari domin ban san haka abin ya ke ba sai da na zo na fara sai na ji ashe wahala ake sha sosai. Don lokacin da na fara sai da gaba na ya fadi, na ji kamar ba zan iya ba, amma dai da na daure na sa wa zuciya ta zan iya sai na ci gaba.

Amma dai a yanzu kin yi gogewar da za ki iya fitowa a kowanne fim?

BILKISU: E to, ka san abin sai a hankali amma dai na san zan kokarta. Sai nan gaba zan iya wannan bugun kirjin. Ka san ni bakuwa ce.

Wanne irin buri ki ke da shi a game da harkar fim?

BILKISU: Ni dai buri na shi ne na zama babbar jaruma yadda duniya za ta san ni. Kuma ina fatan Allah Ya sa na gama da harkar fim lafiya.

Daga karshe ko ki na da wani sako?

BILKISU: Sakon da na ke da shi shi ne godiya ce ga ubangida na, Abdullahi Sani Abdullahi (Baba Karami) domin shi ne ya fara saka ni a fim kuma a yanzu a kamfanin sa na ke.

Nicki Minaj flaunts her hourglass figure in pink suede bodysuit (photos)

34-year-old rapper Nicki Minaj put her hourglass figure on display while posing seductively in pink suede and black leather bodysuits during a secret photoshoot. More photos below.


Sunday 29 October 2017

Saboda Adam A Zango Na Shigo Nigeriya Kuma na Fara Fim Inji Amina Muhammad Amal



Ki gabatar wa da makaranta kanki.

Sunana Amina Muhammadu, daga ƙasar Kamaru na zo Nijeriya. Na yi karatuna tun daga furamare har sakandire a Kamaru, duk cikin harshen Faransanci. Daga bisani na halarci wata tsangaya da ake koyar da Turanci a can Kamarun, na koya cikin wata uku. Yanzu ina jin yare huɗu, Fulfulde, Hausa, Faransanci da kuma Turanci. Wannan shi dai a taƙaice.

Ta yaya aka yi kika zo Nijeriya?

To, lokacin da nake Kamaru ina kallon finafinan Hausa, kuma ina jin daɗin yadda ake nuna al’adar Hausa. Na koyi abubuwa da yawa dalilin fim ɗin Hausa, tun daga kan sanya sutura irin su; atamfa, abaya, leshi da sauran su. Haka zalika, salon maganganun da ake amfani da su, suna matuƙar birge ni. Don nakan kwaikwayi abubuwa da dama.
Jarumin da nake matuƙar ƙauna shi ne Adam A Zango, saboda shi na baro Kamaru na zo Nijeriya. Na daɗe ina mafarkin yin ido biyu da shi, nagode Allah da ban mutu ba sai da Ya cika min burina na ganin Zango, har na yi fim da shi.

Da ma saboda fim kika zo?

Eh to, kai tsaya ba zan ce saboda fim na zo ba, na zo ne saboda in ga Adam A. Zango, sai bayan mun haɗu na ji ina sha’awar fitowa a fim. Kuma, dalilin fitowa ta fim ɗin shi ne, ƙalubalen da na gamu da shi kafin iyayena su yarda su bar ni yana da yawa. Amma dai sun ƙyale ni, tun da sun fahimci abin da nake so kenan. Saboda haka, ta ya ya zan gamsar da su cewa na haɗu da shi, shi ne in yi fim ɗin da zan kai musu su gani. Hatta ƙawayena ta hanyar fim zasu yarda na gan shi.
Tsoron da iyayena suka riƙa ji bai wuce yadda ba ni da kowa a Nijeriya ba, ba su san hannun wanda zan faɗa ba. Sai na nuna musu cewar Adam A. Zango yana da kirki kuma zai kula ni, duk ban taɓa haɗuwa da shi ba, na yi iya bakin ƙoƙarina wajen gamsar da su; duk da ina matsayin mace, zan kiyaye mutuncina har in dawo gida. Na faɗa musu duk da ban ga shi ba, ballantana in san halayensa na zahiri, amma na san Inn Shaa Allah zai karɓe ni hannu biyu-biyu.

Wane ƙalubale kika haɗu da shi a hanya?

Taɓ! Gaskiya na sha wahala ba ƙarama ba, domin mota na biyo ba a jirgi na zo ba. Na shigo Nijeriya ne ta jihar Ribas, na kwana a Kalaba, saboda matsalar tsaro da ake fama da ita a Arewa Maso Gabashin Nijeriya.

Da gari ya waye na samu motar Abuja, sannan na shigo Kaduna.
Lokacin da na zo Arewa ban san kowa ba, ga shi ba na jin Hausa, ba kuma kowa ne yake cin Turanci ba. Da ma iyayena sun bani kuɗi isassu kafin na taho, saboda haka na kama otel a Kaduna na zauna, na fara tunanin ta inda zan fara.
Lokacin da yunwa ta kama ni, na sa aka kawo min abinci, sai da na yi kuka har kaina ya yi ciwo, don ban taɓa cin irin abincin ba; shinkafa da wake ce.
Amma yanzu na saba.

Yadda kuwa aka yi na san Adam yana Kaduna shi ne, kullum a waƙoƙinsa yana yawan faɗar garin Kaduna a matsayin inda yake tinƙaho da shi, shi yasa kai tsaye na nufin can.
A hankali na haɗu da wani Guyson, wanda yaronsa ne, sai ya ga hotonsa a wayata, sai ya ce na san shi ne, sai na ba shi labarin yadda aka yi na zo Nijeriya.
Daga bisani sai na haɗu da Habu Sarki, wanda kusan amini ne a wajen Zango, shi ya kula ni, ya ɗauke ni tamkar ƙanwarsa ta jini, har Allah ya sa na haɗu da Adam A. Zango.
Haƙiƙa ba zan manta da gudunmuwar Habu Sarki gare ni ba, ya taimake ni sosai, shi ne kallo a matsayin ubangidana.

Ta yaya kika fara fim, kuma kin yin fim ya kai nawa?

Lokacin da zan fara fim na gami da matsaloli da yawa, na farko ba na jin Hausa, kuma fim ɗin nan da Hausa ake yi.

Saboda haka sai da na shafe wata shida ina koyon harshen Hausa.
Haƙiƙa na yi farin ciki ƙwarai kuma ina alfahari da finafinai Kannywood, ga shi dalilinsa na koyi harshe da al’adun wani gari da ba nawa ba.
Da aka zo za a fara fim ɗin, sai aka ji hausata ba ta gama zama gangariya ba, sai aka ƙara min wasu watannin.

Cikin ikon Allah na koyi harshen Hausa, na yi fim ɗin na farko mai suna AMAL.
Bayan shi na yi finafinai guda biyu, Hisabi da Matan Aure.

Har ila yau, lokacin da za a yi min fim ɗin da yawa suna cewa rol ɗin bai dace da ni ba, to kuma sadda aka ɗora min kyamara sai tsoro ya mamaye ni, sai da aka yi da gaske, domin ana so in yi, tukun na zage aka yi aikin da ni.

Dama kuma an faɗa min, kusan duk waɗanda suka Kannywood da farko sai sun fuskanci wannan matsalar, amma a hankali sai ta zama tarihi.

Mun Dauko daga: fimhausa

Kadan Ya Rage A Dambace Tsakanin Abida Muhammad Da Rasheeda Mai Sa'a

DUK da cewar taron kungiyar mata masu aure ’yan fim da aka yi a Kano kwanan nan an yi shi an gama lafiya, sai dai kadan ya rage a dambace tsakanin Abida Mohammed da Rasheeda Adamu Abdullahi. A gaskiya, ba don shiga tsakani da aka yi ba, aka shawon kan su, to da kyar da tuni labari ya canza.

Lamarin dai ya auku ne bayan an tashi daga taron. A daidai lokacin da mutane su ke fitowa daga wajen, sai kawai aka ji hayaniya ta kaure tsakanin jaruman biyu, wadanda a can baya aminan juna ne da ko barci ba ya raba su.

Babu dai wata cikakkiyar magana a game da abin da ya hada su fada a wajen, amma dai a lokacin da Rasheeda ta ke fitowa daga dakin taron an ji ta ta na fada tare da yarfar da habaici ba tare da an san ko da wa ta ke ba. Amma fitowar Abida da kuma yadda su ka shiga fada wa juna bakaken maganganu shi ne ya sa aka fahimci inda maganar Rasheeda ta dosa.

Sun shafe tsawon kusan minti 30 su na ta cacar baki da gori da tonon silili a tsakanin su, har ma da kokarin kai wa juna duka. Abida ce ta fi zakewa a wajen kai dukan, ana ta rirrike ta, yayin da ita kuma Rasheeda aka yi kokarin saka ta a motar ta. Hakan bai sa Abida ta janye kudirin ta na kai wa Rasheeda duka ba.

Jama'a sun cika wajen, ciki har da masu wucewa, su ka tsaya su na kallo. Abin dai babu tsari, sai wanda ya gani!

An samu shawo kan fadan ne a lokacin da Saima Mohammed ta fito daga dakin taron, ta ga abin da ya ke faruwa, don haka ta je ta shiga tsakin su. Ganin girman ta ne ya sa Rasheeda ta ja motar ta, ta bar wajen, yayin da ita kuma Abida aka janye ta da karfin tsiya.

Mun dauko daga: FIM

Daga Bikin Nadin Fati Nijar Da Rashida Mai Sa'a Sarauta A Jihar Neja (kalli Hotuna)



A jiya mun ruwaito cewa an kaddamar da bikin nadin Rashida Adam da Fati Nijer.

Wannan hotuna ne daga bikin bada Sarautar wanda aka gudanar da shi a jiya Juma'a, a Dandalin UK Bello dake dake Minna babban birnin jihar Neja, kungiyar masu shirya finafinai na Arewa reshen jihar Neja ce ta ba su sarautar, inda aka baiwa Fati Nijar Sarautar Gimbiyar Arewa, ita kuma Rashida aka bata Sarautar Wakiliyar Arewa.





Ƙungiyar Izala Ta Tara Kuɗi Sama Da Milyan 95 Ta Hanyar Sadakar Fatun Layyar Da Ta Gabata

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Ga jadawali fatun da aka samu a kowace jiha da kudin da aka saida fatun, tare da kuɗaɗen da shugabannin JIBWIS tun daga matakin ƙasan ƙasa, har zuwa saman sama,  suka bada a ƙalla 1000 wanda za'a baiwa duk wanda ya bada nasa resit.

MASU KARATU KU TAYA MU DUBAWA, WACE JIHA CE TA YI NA ƊAYA, NA BIYU DA NA UKU. SANNAN
WACE JIHA CE TA YI NA BAYA?

1.Kaduna
Adadin Fatu, 25,534
Adadin Kudin Fatu, ₦12,744,500
Adadin Kudin Resitai ₦350,000.
Jimmilla ₦13,094,500

2.Katsina
Adadin Fatu 15,566
Adadin kudin fata₦11,767,350
Adadin kudin resitai₦198,500        
Jimilla ₦11,965,850

3.Zamfara
Adadin Fatu 13,847    
Adadin kudin fatu ₦10,193,800    
Jimilla ₦10,193.800

4.Sokoto
Adadin fatu 12,054
Adadin kudin fatu  ₦9,646,100
Adadin kudin resitai  ₦61,300          
Jimilla ₦9,707,400

5.Niger
Adadin fatu 12,480
Adadin kudin fatu ₦6,489,000
Adadin kudin resitai ₦272,125  
Jimilla ₦6,761,125

6.Jigawa      
Adadin fatu 6,410
Adadin kudin fatu
Adadin kudin resitai
₦5,011,300
Jimilla ₦5,011,300

7.Kebbi
Adadin fatu 6,784
Adadin kudin fatu
₦4,902,850
Adadin kudin resitai
₦234,000
Jimilla ₦5,136,850

8.Bauchi
Adadin fatu 7,142        
Adadin kudin fatu ₦4,579,700      
Adadin kudin resitai
₦178,500
Jimilla  ₦4,758,200

9.Kano
Adadin fatu 5,538
₦4,393,400      
Adadin kudin fatu ₦141,600
Adadin kudin resitai ₦4,535,000

10.Taraba            
Adadin fatu 6,886              
Adadin kudin fatu ₦4,270,000      
Adadin kudin resitai ₦129,000          
Jimilla ₦4,399,000

11.Gombe
Adadin fatu 5,086    
Adadin kudin fatu ₦3,882,250              
Jimilla ₦3,882,250

12.Adamawa        
Adadin fatu 3,767  
Adadin kudin fatu ₦2,631,400        
Adadin kudin kudin resitai ₦88,000            
Jimilla ₦2,719,400

13.Nasarawa        
Adadin fatu 5,003    
Adadin kudin fatu ₦2,589,900        
Adadin kudin resitai ₦102,000          
Jimilla  ₦2,691,900

14.Plateau            
Adadin fatu 4,510  
Adadin kudin fatu ₦2,092,560        
Adadin kudin resitai ₦80,500          
Jimilla ₦2,173,060

15.Abuja              
Adadin fatu 3,352    
Adadin kudin fatu ₦1,600,700        
Adadin adadin kudin resitai ₦195,000          
Jimilla ₦1,795,700  

16.Yobe                  
Adadin fatu 1,668      
Adadin kudin fatu ₦1,600,000        
Jimilla  ₦1,600,000  

17.Lagos      
Adadin fatu 2,277    
Adadin kudin fatu ₦1,184,850        
Adadin kudin resitai ₦150,000          
Jimilla ₦1,334,850  

18.Kogi  
Adadin fatu 1,526      
Adadin kudin fatu ₦688,000          
Adadin kudin resitai ₦115,225          
Jimilla  ₦803,225.

19.Borno          
Adadin fatu 1,648  
Adadin kudin fatu 616,800  Adadin kudin resitai ₦44,400            
Jimilla ₦661,200  

20.Benue                
Adadin fatu 795  
Adadin kudin fatu
₦437,950            
Adadin reaitai ₦51,900             Jimilla ₦489,850

21.Oyo                    
Adadin fatu 1064              
Adadin kudin fatu  ₦318,700            
Adadin kudin resitai ₦58,600            
Jimilla ₦377,300

22.Kwara                  
Adadin fatu 701                
Adadin kudin fatu  271,700
Adadin kudin resitai ₦26,400            
Jimilla ₦298,100  

23.Ogun                  
Adadin fatu 270                
Adadin kudin fatu  ₦114,000                    
Jimilla ₦114,000  

24.Delta            
Adadin kudin fatu ₦84,000
Adadin kudin resitai ₦8,000               jimilla ₦92,000  

25.Edo                    
Adadin fatu 200    
Adadin kudin fatu ₦80,000
Adadin kudin resitai ₦19,300            
Jimilla ₦99,300  

26.Rivers        
Adadin fatu 190    
Adadin kudin fatu 61,100  
Adadin kudin reaitai ₦143,500            
Jimillah ₦204,600  

27.Osun                    
Adadin fatu 86                  
Adadin kudin fatu  ₦45,150
Jimilla ₦45,150  

28.Cross River                  
Adadin kudin fatu ₦28,550
Jimilla ₦28,550  

29.Ebonyi                  
Adadin fatu 34                  
Adadin kudin fatu ₦25,000
Adadin kudin resitai ₦500
Jimilla ₦25,500  

30.Abia        
Adadin fatu 43                  
Adadin kudin fatu ₦16,300
Jimilla ₦16,300.

31.Ekiti
Adadin fatu 28                  
Adadin kudin fatu ₦10,400
Jimilla ₦10,400  

32.Enugu                  
Adadin fatu 6,000    
Adadin kudin fatu ₦13,000
Jimillah ₦19,000  

33.Akwa Ibom        
Adadin kudin fatu ₦46,500
 
34.Bayelsa                          
Adadin kudin resitai 2,000
Adadin kudin fatu ₦39,000             Jimilla ₦41,000  

35.Imo                      
                                                       36.Anambra            
                                                                                 
37.Ondo                                    

JIMLA.                                     Kudin da aka sayar da fatun layya na bana 1438, 2017 an samu ₦92,388,610.      

Kudin da aka samu cikin shugabannin JIBWIS a faɗin kasa ta hanyar masu taimkawa ana basu resit₦2,743,550    

Idan an dunkule lissafin kudin da aka samu bana shine ₦95,132,160.00
(Miliyon casa'in da biyar, da da dubu ɗari uku, da Naira ɗari da sittin kacal.

NB. Jihohin Imo da Anambra sun kasance cikin fitinar rikicin kabilanci a dai dai wannan lokaci, Don haka basuda natsuwar tattara alkalumma na fatun laiya da gudummuwar kudi daga al'ummarsu.

Mun samu takardan bayanan ne a wajen taron Majalisar Ƙoli ta JIBWIS, wanda ta gabatar a katsina ta hannun sakataren kwamitin fatun Malam Muhammad Jameel Maharaz

Saturday 28 October 2017

Jami'ar Danfodiyo Ta Sake Samar Da MaCe A Matsayin Farfesa Ta Biyu A sokoto

DAGA MUKHTAR HALIRU TAMBUWAL SOKOTO

Jihar Sokoto ta kai ga Farfesa  mace wadda kuma ita ce mace  ta biyu a jihar a matsayin mace farsesoshi.

Farfesa  Sa'adiyya Omar wadda ta yi karatunta na furamari a Dandago da ke Kano a shekarar 1960 zuwa 1964, ta kuma yi makarantar gaba ga furamari a makarantar 'yan mata ta shekara a 1964-67, sai makarantar "yan mata ta Gwamnati dake Dala, Kano a 1967-1972.

Sannan ta yi digirin farko a fannin ilimin koyarwa na Hausa a jamiar Bayero a 1977. Ta yi hidimar kasa 1977-78, sannan ta yi digiri na biyu a fannin Hausa a jami'ar SOAS da ke Landan a 1984, sai digirin digirgin a jami'ar Danfodiyo ta Sokoto a 2010.

Farfesa Sa'adiyya Omar, ta rike wasu mukamai a jami'ar Usmanu dan Fodiyo da suka hada da: Daraktan Cibiyar Nazarin Hausa  a 2013-17, mamba a kwamitin zartarwa na jami'ar, da sauransu, ta kuma yi zama a wasu kwamitocin da suka hada Shugabantar kwamitin Amintattu na musabakar Al-kur'ani Mai girma ta kasa Wadda jami'ar take shiryar daga shekarar 2013 Zuwa yau, kwamitin kula da Gidajen Dalibbai, kwamitin shiryar jarabawar Dalibbai, Kwamitin shirya bikin Yaye dalibban jami'a, da sauran kwamitoci.

Haka kuma ta bada gudunmawa cikin wasu kwamitoci daban daban wadan da ba na cikin jami'ar ba da suka hada da :Kwamitin bincike kan cin zarafin yara a manyan makarantun, na kwalejin ilimi ta tarayya da ke Gusau, Jihar Zamfara., Wasu kwamitoci a makarantinnen Yan mata ta Nana, da ke Sokoto, Ta Sarkin Musulmi Bello ta ke Sokoto, Tana cikin Kwamitin da Gwamnatin jihar Sokoto ta kafa dan Kula da Gidan marayu mallakar jihar, kwamitin lamurran mata a matakin kasa da ke legos a shekarar 1991, Mamba a kwamitin Amintattu na hukumar mata ta jihar Sokoto a shekarar 1991.

Shehiyar malamar ta Tayiwa Addini da Al-ummah hidimomi a wurare Dabandaban da suka hada da : Shugabar kungiyoyin Tarayyar mata musulmi ta kasa (Fomwan)  a shekarar 1993 zuwa 1997,Amirar Fomwan reshen jihar Sokoto a 1985 zuwa 1992, Amirar Kungiyar  Mata musulmi (MSO)  reshen Jihar Sokoto a shekarar 1997 zuwa 2000,Jni da sauran su.

Farfesar, ta yi dinbin rubuce rubuce da makaloli masu yawan Gaske da suka hada da : Rubuta Littafin Fasahar Mazan Jiya, wanda ke Nazari akan Rayuwa da Wakokin Malam Mu'azu Hadeja, Littafin Modibbo Kilo ( Diya ce ga Nana Asmau Yar Shehu Usmanu bn Fodiyo) Mai bayanin Rayuwar ta da Ayukkanta. Wani  littafin da ta rubuta shine :Yan taron Nana Asmau diyar Dan Fodiyo .(Dalibban ta) Mai bayani a kan Tasirin da Taskance Wakokin Su. Tare da littafin Malammai Mata na Daular Usmaniyya a karni na 19 da 20.
Akwai sauran littafai da ta rubuta da wasu da ke tafe da wadanda take akan rubutawa tare da dinbin mukaloli daban daban da ta gabatar ciki da wajen kasar nan.

Farfesa Saadiyya, ta yi tafiye tafiye a wasu kasashe da suka hada da : Saudiyya, Ingila, Masar, Sudan, Nijar, Athens-Greece, Astoria, Malaysia, China da sauran su.

Farfesa tana da Yara biyar da jikoki da dama, Margayi Dr. Omar Bello Dan masarautar sokoto kuma jinin Shehu Usmanu Dan Fodiyo shine baban yaran na ta.

Muna yiwa farfesa fatar Alheri da samun Nasarori a rayuwar ta da Gamawa lafiya.  Amin.

'Yan PDP ne rabin gwamnatin Buhari – Hameed Ali

Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya Kanar Hameed Ali ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kasa cika alkawurran da ta yi wa al'ummar kasar na kawo sauyi.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi lokacin kaddamar da wani sabon ofishin kungiyar goyon bayan Shugaba Buhari wato (Buhari Support Organisation BSO) a Abuja ranar Juma'a, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Kungiyar BSO ita ce babbar kungiyar da ta kunshi sauran kungiyoyi da suka shige wa shugaban gaban wajen yakin neman zaben shekarar 2015.


"A yanzu, zan iya cewa muna da 'ya'yan jam'iyyar PDP kaso 50 cikin 100 a cikin gwamnatinmu. Ta yaya za a ci gaba da wannan nauyin a kanmu? Ta yaya za mu iya cimma abin da muke fata da wannan nauyin," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: "A yanzu 'yan PDP ne suke ba da umarnin abin da za a yi. Wannan ne abin da ya kamata mu yaka. Za mu yi yaki don kwato hakkinmu da kuma kyawawan manufofin gwamnatinmu."

Hakazalika ya ce lokaci ya yi da za su farka daga bacci don samar wa kasar makoma ta gari.
Sai dai ya ce "Shugaba Buhari ba shi da wata matsala don yana abin da ya dace ne."
Har ila yau ya ce "wadanda suka yi aiki tukuru wajen ganin gwamnatin canji ta kai ga nasara ba a saka musu ba tukuna."

Daga nan ya ce "wajibi ne kungiyar BSO ta tashi tsaye wajen ganin ta jagoranci sabon yakin kawo shugabanci nagari. Dole ne mu yi haka don gyara sunanmu da kuma sunan shugaban kasa da abin da yake yi."
"Shugabanmu yana yin abin da ya dace kuma wajibi ne mu ba shi goyon bayan da yake bukata," in ji shi.

A Yanzu Kam A Masana'antar kannywood babu wanda Tayi kyau Aisha Tsamiya (kalli Hotuna)


Wadannan sababbin hotuna ne da jaruma aisha aliyu tsamiya  ta sanya a shafinta na instagram wanda suke nuna yanzu kam ta sha gaba duk wata 'yar fim da kyau.

Ga hotunan kamar haka:-







Mi zaku ce a kan hakan?

Friday 27 October 2017

Honarable Gudaji Kazaure ya caccaki shugaba Buhari a kaikaice



Fitaccen dan majalisar wakillan nan na Najeriya mai wakiltar mazabar Kazaure, Roni, 'Yankwashi da kuma Gwiwa dukkan su a jihar Jigawa dake a Arewa maso yammacin Najeriya mai suna Honarable Muhammad Gudaji Kazaure ya caccaki shugaba Buhari a kaikaice.

Shahararren dan majalisar dai ya yi wannan caccakar ne a yayin da yake tsokaci a zauren na majalisar game da sabon tsarin nan na gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari din da ke fitar da doyar da aka noma zuwa kasashen ketare.

NAIJ.com dai ta samu cewa ta yake tsokacin, Alhaji Gudaji Kazaure ya nuna rashin dubara da kuma sanin ya kamata daga bangaren gwamnatin game da wannan tsarin inda yace shi baiga yadda za'ayi talaka ya mori wannan irin bahagon tsarin ba na fitar da kayan abinci zuwa kasashen waje sannan kuma an hana shigowa da shi.

Dan majalisar daga karshe sai ya jawo hankanin shugabannin majalisar yan uwansa da ma sauran shugabannin kasar a dukkan matakan mulki da su duba wannan matsala domin kawo gyara.

VIDEO: B.O.C – Maestro (Official Video)

Boc Madaki Is Back Again With Another Another Hit Video Tittled Maestro Which directed By Dickson GiftedHand Academy Download And Share Your Thougts


DOWNLOAD VIDEO

Audio X Video: Dicsa – Banda Lafiya (Directed By Ib_jika)

Sadeeq sani sadeeq popularly known as “Dicsa Neh” i s a Kaduna state born and rai sed bilingual rapper and performer. He made him self know n few year s back in and around the Northern.

state s w ith hi s debut single ‘Ana Ruan Kudi” and hi s energetic stage vibe. To take it to a w hole another level he i s here w ith yet another sma sh joint ‘Banda Lafia’ hich the video a s shot and directed by IB Jika

Enjoy
Click here to Download the Audio

DOWNLOAD MP3 HERE

Click on the link below to download the video

DOWNLOAD VIDEO HERE

Music: DeeZell Ft. Korede Bello – Aisha

Saukar da sabuwar wakar Manya manyan jarumai mawakan arewa Deezell ft korede bello the tittle name of song is Aisha



Download Audio Now

Sani musa Danja shahararren Jarumin Kannywood ya zama jakadan majalisar dinkin duniya


Anyi taro kaddamar dashi da sauran shahararren yan wasan fannin nishdantarwa a garin Abuja

Fittaccen dan wassan kwaikwayo kuma mawaki Sani Danja ya samun sabon mukami a majalisar dinkin duniya inda aka nada shi a matsayin jakada a fannin kafa manufa ta samun cigaban zamani (SDGs) ta majalisar.

Anyi taron kaddamar da jarumai a garin Abuja ranar laraba 25 ga watan octoba yayin da ake bikin nuna farin ciki zagoyowar ranar majalisar dinkin duniya.

Danja wanda aka fi sani da 'sarkin nishadi na arewa' ya shahara a fadin Nijeriya bisa ga rawan da yake taka wa a harkar nishadantarwa.

Wannan sabon daukaka yana cikin jerin jakadanci da ya samu daga kamfanin Glo, Rotary, gidauniyar save the children, western loto da sauran su.

Banda Sani Danja sauran jaruman kannywood da suka samu mukamin jakadanci na majalisar dinkin duniya akwai Yakubu Muhammed da Uzee Usman.

A cikin manyan baki da suka halarci taron akwai Ministan wassannin da ayyukan matasa Solomon Dalung da babban mataimakin shugaban kasa a kan SDGs Princess Adejoke Orelope-Adefulire.

Sauran jaruman Nijeriya da suka samu matsayin sun hada da mawaki Tuface, Sunny Ade, Omotola jalade Ekehinde, Chigurl, Teju babyface, Alibaba da Zdon Paporella.

Video:- Maganin ciwon Hawan Jini Da siga da ciwon Siga Dr Abdallah usman G/kaya


Wannan bidiyo yana dauke da bayyanin ciwon siga da ciwon hawan jini wanda al'umma ke fama da shi kuma an tabbatar da hakan.
Saukar da wannan bidiyo da bai wuce 3mb data domin ka amfana da amfanar da al'umma.

Download Video Now

Daga Darulfatawa.com


Ana Hasashen Tafi kowace Jarumar kannywood Iya style Na Hotuto Amina Amal (kalli Hotuna)

Sababbin sabuwar jaruma Amina amal masu zafi wanda wannan wani sabon style ne na hoto wanda a kannywood itave ta fara wannan


Babban Director Hausa fim na kannywood Ali Gumzak ya samu karuwar 'ya Halimatu sadiya

Alhamdulillah nasamu karuwa da HALIMATUS SADIYYA ina rokon ALLAH ya albarkaci rayuwarta yabamu ikon bata tarbiyya.

Thursday 26 October 2017

KuzonMu Kalli Safara ƙayataccen Shiri in Ali Nuhu

Daga instagram din jarumin

@Regranned from @dahiru_a_k_nassarawa -  @Regrann from @realabmaishadda -  Za'a Fara Nuna Wannan kayataccen shirin a ranar 3 ga watan November In Shaa ALLAH A Film House Cinema Kano dake ADO BAYERO MALL A Cikin Shoprite.  maza ku garzayo mazan ku, da matan ku domin kashe kwarkwatar idanun ku

Shiryawa @isaaisa10
Bada Umarnin @aleegumzak SAK
Cc @realalinuhu @aashariff @abba_el_mustapha @isaaisa10 @aleegumzak - #regrann - #regrann

Ali Nuhu Dalilin da yasa na karfafa gwiwan Rahama sadau wajen bada hakuri

Jarumin yace Rahama ta yarda da bada hakurin ba tare da an tilasta mata hakazalika tayi hakan bayan ta gane cewa tayi kuskure kuma yayi ikirari cewa shi dan Adam ajizi ne wanda baya rabuwa da yin kuskure


Fitaccen jarumin kuma mai tauraro Ali Nuhu shine kashin bayan kokon bara da jaruma Rahama Sadau tayi na neman gafara bisa ga abun da ya faru a baya wanda yayi sanadiyar korarta daga farfajiyar kannywood.

A rahoton da jaridar Dailytrust ta fitar Ali Nuhu yace jarumar ta bada hakuri bayan ta gane cewa tayi kuskure, yayi ikirari cewa dan Adam ajizi ne wanda baya rabuwa da aikata kuskure.

" A matsayin mu na manya a masana'antar, ya zama dole mu wayar da kan kananan jarumai na dandalin, shiyasa na karfafa mata gwiwa wajen bada hakuri"

"Yana da kyau idan mutum ya gane kurakuran shi ya bada hakuri. Rahama tayi kokari da ta bada hakuri kuma ta dau alkawari cewa baza ta kara aikata kuskuren ba. Ta aika wa kungiyar MOPPAN wasikar neman gafara wanda na san membobin kungiyar suna tattaunawa akai" Inji Ali Nuhu.
Ita dai Rahama Sadau ta fito fili ta baiwa jama'a hakuri bisa ga kuskuren da tayi wanda yasa aka koreta daga dandalin kannywood.
Tayi hakan ne yayin data ziyarci gidan rediyo na
Rahama Fm dake jihar Kano cikin wani shiri mai suna "ku karkade kunnuwan ku".

Motar Gwamna Fayose Ta Kimanin Naira Milyan 44 Ta Kama Da Wuta A jihar Legas


Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito motar wadda kirar G-Wagon Marsandi ce, ta kai naira miliyan 44, ta kama da wuta ne akan hanyar ta na zuwa filin tashi da saukan jiragen na jihar Legas.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa a lokacin faruwar wutar gwamnan ba ya motar, kamar yadda Kakakin gwamnan jihar wato  Lere Olayinka ya bayyana.

Rahotanni sun tabbatar Ba wanda  ya samu rauni, Sannan ba'a san  musabbabin faruwar gobarar va.

Daga Sani Twoeffect Yawuri

Nasiha Zuwa Ga ‘Yan Gani Kashe Ni Buhari -Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi


Assalamu Alaikum
Annabi-tsira da ammincin Allah sutabbata agareshi yace: “Addini nasiha ne. Sai muka ce: ga wa Ya manzon Allah? Sai yace: zuwa ga Allah da Kuma zuwa ga littafinSa da Kuma zuwa ga manzonSa da Kuma zuwa ga shugabanin Musulmi da talakkawansu”.

In kun lura da lafazin Manzon Allah -alaihis salam- a karshen cewa yayi: ” da Kuma zuwa ga shugabanin Musulmi da talakkawansu” ba cewa yayi: ” da Kuma zuwa ga shugabanin Musulmi da Kuma zuwa talakkawansu” ba. Watau Sai Ya dunkulesu gaba daya da nasiha. Wannan fasahar Magana wadda tana daga cikin muijizojin Annabi ta kunshi halin yiwa shugabannin Musulmi da talakkawansu nasiha gaba dayansu ko dai-dai kunsu. Duka sunna ne.
Nashihar da na yiwa Gen. Buhari na kacewansa daya daga cikin shugabanin Musulmi tare da mabiyansa gaba daya ne karkashin Wannan hadisi.

Amma yanzu, a Wannan nasihar na kebe daga cikin mabiyansa ‘yan gamu a kashe ne kawai.
Daga farko in kiransu da suji tsoron Allah da ranar da zaa tadasu ranar tashin alkiyama. Ranar da kowace rai cewa takeyi: “Raina Raina ni kadai”. A ranar za a barka sai kai sai ayyukanka na kwarai da muyagu. A ranar da Shima Gen. Buhari zai tashi Yana cewa: “Raina Raina Ya Ubangijina” A ranar da Allah zai masa hisabi game da ayyunkansa na ibadarsa da Kuma shugabancinsa na Jinin mutane da dukiyarsu da addininsu da sauran hakkokin mutane da kekan shugabanni.

A wancan karon na mulkinsa na farko akwai malaman da suka yi mishi nasiha game da yadda Ya tafiyar da mulkinsa domin shine wajibin malami ba tare da Jin tsoron kowaba sai Allah.
To a yanzu kai ka fito kana zage zage da habaici da bacin rai domin an yi masa nasihar da tafi mashi alheri duniya da lahirassa domin wani kwadayin duniya da kake neman wanda zai ceceka daga azabar Allah ta duniya domin sabonka zuwa ga Allah da fasikancika, ka mance da shi Allah Har kana zagin malami domin baida irin raayinka.  To kayi sauri ka tuba zuwa ga Allah ka nemi afuwar duk wanda ka cutar.
Dalilin yin Wannan nasihar kuwa shine ku ‘yan Gani kashe ni  – kun gurbata akidarku da tawwakkali akan mahaluki ba akan Allan da Ya mallaki komeba. Allah Yace:

Surah Al-Anaam, Ayah ta 17:
(kuma Idan Allah Ya shafeka da wata cuta to babu mai kwaranyewa gareta sai Shi)
Wallahi indan kayi imanin cewa musibar da muka fada cikinta babu mai gyarata sai Buhari kayi shirka. Shin in kura tana maganin zawo tayima kanta mana. Baku ganin yadda Shi kanshi Buhari ya kasa ba kansa mulkin kasan nan domin mulki na Allah ne Har kace : Sai Buhari!
Kuna son ku halaka kank ku halakashi. Kusa masa gururi azucciyarsa. Bawan Allan nan Ya fito yace: Na gaji bazan sake menan shugabancin Kasarnan ba. Amma domin fitinarku kunsa Shi ya fito gaban jamaa ya karyata kansa ya nuna MA jamaa cewa shugabannin musulmi da aka sanu da gaskiya da rike Amana basu da banbanci yanzu da masu yin karya domin neman mulki.

Kuma kun fito Kuna zagin Mai mishi nasiha domin kare maslaha ta alumma da tashi.
Mai makon kubarshi a nuna masa yadda zaiyi kaffaran kurakuransa na baya wanda suna daga cikin sababin jefamu cikin wannan musiba Sai gashi kun fito Yan kanzagi kuna son ku hanashi istigfari domin Sai wanda yayi ikirari dayiwa Allah laifi yake neman gafarassa da menam afwa ga mutanen da yaci zarafin su ya wulakantasu da ukuba Bata shariar Allah ba.
Juyin mulkin da suka yi ba sabo bane Kwai wurrin dokar kasa Kai sabo NE ga Allah. Tunda anyi kuskure kaffarassa shine ya tabbata yaga an dawo da wanda zai hada kan kasa domin shi ne awla. Watau matukar babu kwanciyar hankali babu mulki balle adalci. Kuduba yadda kasahen musulmi suka fada cikin musibu.  Kamar Iraqi da siriya da libiya da Egypt da Somali da yamen. Shin haka kuke son Nigeria tazama?

To haka akeso a wargazamu. Kamar yadda akayi anfani da Boko Haram aka halaka kasar borno haka akeso ayi anfani daku a wargaza mu mu dake yamma. Kunga DE Boko Haram sunfiku ikirari Mai manufa do min su sun labe da sunan Allah ne da sunnan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa.   Amma ku Yan gani akashen mutunne. To wallahi kuyi hattara. Zaazo ayi anfani da ku Bayan an harzukaku a maida ku Kamar Yan taadah Yan Boko Haram masu tada fitina masu tada zaune tsaye.

Ina kiranku da ku sa hankali da natsuwa da basira kukai zucciya nesa Kuma kada kuyi mamakin malamin da adalarsa bata gushe ba in yace kuyi wani abu game da siyasar wannan kasar. Wallahi tallahi ba kusan duk abinda ke kasa ba. Kuma ita siyasa asalinta ta malamai ce ba jahilai ba. Sune ahl aqdi Wal halli. Sune Allah yaba hurumin zaban wanda suka dace da lura da zarafi. Ba Yan banga ba da Yan gamu akashen. Saboda haka musake Jin jahilin da zai hana malamai sa bakinsu acikin harakar siyasa.
Saboda haka kada kayadda kayi fada ko zagi ko kisa domin Buhari ko wani Dan siyasa. Zagin musulmi fasikanci ne Kuma yakinsa kafircine.  Kuma duk wanda ya yi kisa ko yafito aka kashe shi domin siyasar wani mutum ya halaka a wutar jahannama -Allah Ya kare mu daga ita.
Allah Ya shiryar damu Ya hada kanmu zuwa ga alheri da abinda Ya keso. Kuma Ya nisantar damu daga dukkan fitinar karshen zamani. Amin. WA sallallahu ‘Ala nabiyina Muhammad wa ‘Ala Alihi wa sahbihi wa sallam.

Daga Daily Nigerian Hausa

Jaruma Umma Shehu, wanda ta zama topic na tattaunawa bada jimawa ba, ta mika sakon jinjimawa ga Ali Nuhu.



A shafin ta na Instagram, ta bayyana jarumin a matsayin mai son mutum da gaskiya. Ga abun da take cewa:

"kaga masuyi domin Allah inada hujjojin da yasa nai wannan maganar hujja na

 (1) shine zai dauko ki/ka lokacin dakai bakowa bane yamaida ka wani hujja na

 (2) bayayi dan kasoshi saidai yayi maka domin allah hujja na

 (3) shine zai daukeka a matsayin yaronsa yanuna maka yadda ake neman arziki yasa aimaka ya kuma yimaka harsai ya tabbata yayimaka yadda zaka taimaki kanka ka taimaki wani saiya tabbatar katsaya da kafafunka guda biyu duk da haka bazai barka ba zai cigaba da taimakonka ba dole yaita ganin chigaba ba saboda shine mutum na farko dayake son cigaban yaransa dan duk wanda zai zauna a inuwarsa to wallahi sai yayi alfahari dashi saboda yaransa sune abun kwatance a idon duniya saboda babu yaransa wanda bai tsaya da kafarsa ba dan haka nima ina rokan allah yabamu zuciya irin tasa amin akwai wanda yakeda ja akan maganar da nafada kafadi alkhairi kokai shiru."

Aisha Buhari Uwargidan shugaban kasa ta mayar da martani bisa ga zargin da dan majalisa yayi

Dan majalisar dattawa yayi zargin cewa sufeton yan sanda ya baiwa uwargidan shugaban kasa motoci biyu don amfanin kanta.

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta musanta zargin da sanata Isa Misau yayi na cewa babban sufeton yan sanda ya bata motoci biyu domin amfanin ita kadai.

Sanata Misau yayi wannan zargin ranar laraba yayin da ya gabatar da kanshi a gaban kwamiti masu binciken zargin da yake yi kan sufeton yan sandan Nijeriya.

Matar shugaban kasa ta mayar masa da martani ranar alhamis a shafin ta na twitter inda ta rubuta
"Har yanzu ina amfani da motoci mallakar kaina".

Tun ba yau ba dan majlisar ke zargin sufeto janar
Ibrahim Idris da aikata abubuwa da suka sabawa tsarin hukumar yan sanda.

Dalilin zargin da yayi gwamnatin tarayya ta maka shi kotu bisa ga zargin cin fuska ga babban sufeton.

Wata sabuwa!!! Babban sufeton yan sanda ya baiwa uwargidan shugaban ƙasa motoci biyu - inji Sanata Misau

Dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Bauchi Isa Misau ya kara zargin sufeto janar na yan sanda Ibrahim Idris da siyan motoci biyu ma uwargidan shugaban ƙasa Aisha Buhari.

Dan majalisar yayi wannan zargin yayin da yake amsa tambayoyi daga kwamitin bincike akan zargin da yayi ma sufeton yan sanda ranar laraba 25 ga wata.

"har yanzu ina da takardar kwangilar da shi IG ya sallamar wa kotu, inda Uwargidan shugaban kasa ta hanyar babban jami'in mai tsaron ta ya bukaci motoci kerar Toyota Hiace da Sienna jeep. A ranar da mai tsaron uwargidan ya rubuta bukatar shine IG ya sa hannu na a bada motocin. wannan baya daga cikin tsari domin idan muka duba yanda tsarin hukumar babu inda aka ce a baiwa matar shugaban kasa motoci biyu" sanatan ya fada ma kwamitin bincike.

Tsohon jami'in hukumar ya kara jaddada cewa ana amfani da alfarma wajen kara mukamin wasu jami'an hukumar domin wasu da basu cancanci samun karin matsayi alhali akwai na gaban su sun samu.
yayi ikirari da sabon mukaddashin kwamishnan yan sanda na jihar Legas Edgal Imohimi ya samun matsayin domin shi abokin gwamnan jihar ne ba tare da an lura cewa akwai wadanda suka fi shi cancanta.

Misau ya kara zargin sufeto Ibrahim Idris da bada kwangilar biliyan biyu (N2 Billion) ga kamfani mai siyar da motocin Peugeot domin samun motoci kerer Toyota.
Bugu da kari sanatan yace an sauya ainihin ranar aje aiki na sufeton yan sanda domin ba haka yake a da baya ba.

Tun ba yau ba sanatan yake zargin Ibrahim da wasu laifuffuka wanda yayi sanadiyar kai karar shi ga kotu daga gwamnatin tarayya inda take zargin shi da cin fuska.

Wednesday 25 October 2017

DA DUMIDUMINSA An Kashe Matar Shekau A Wani Hari Da Sojoji Suka Kaiwa 'Yan Boko Haram A Borno


Rundunar sojojin saman Nijeriya a yau Laraba ta sanar da cewa tana da tabbacin cewa matar shugaban Boko Haram, Malam Firdausi tana daga cikin wadanda suka mutu a yayin harin sama da sojoji suka kai mafakar 'yan Boko Haram din dake yankin Durwawa a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Daraktan yada labarai na rundunar sojojin saman, Air Commondore Olatokunbo Adesanya, shi ya tabbatar da hakan a yau a Abuja.

Kamar yadda Adesanya ya bayyana, Firdausi ta wakilici mijinta Shekau ne a wani taro na 'yan ta'addan a wurin da sojojin suka kai farmakin.