A tattaunawar ta da PREMIUM TIMES HAUSA Mansura ta fadi abinda ta keyi dai na fitowa a fina-finan Hausa.
Mansura ta ce tun bayan aurenta da shahararren jarumi Sani Danja ta mai da hankalinta ga auren da gina gidan ta.
“Ban taba sha’awar yin wani abu ba tun bayan aure na da masoyi na Sani Danja da ya wuce in ga gidan aurena na cikin natsuwa da kwanciyar hankali, wato kula da ita da duba ‘ya’ya na da miji na. Yanzu ‘ya’yan mu hudu ka ga sai kuma Alhamdulillah. Sai dai yanzu da na kafa gidauniyar ‘Todays Life Foundation domin taimakawa marasa galihu.”
“Yanzu na kafa wata gidauniya mai suna ‘Todays Life Foundation’. Ita wannan gidauniya na kafa ta nedon taimakawa marasa karfi, matan da suka rasa mazajen su da kuma yara kanana. Na yi haka ne domin bada gudunmuwa ta ga mutane da ke cikin halin kakanikayi.
Mansura ta ce gidauniyar ta na samun kudaden ta ne ta hanyar tallafi da kyauta da ta ke samu.
“ Gidauniyar ‘Todays Life Foundation’ na samun kudaden ta ne ta hanyar tallafi da kyauta daga ‘yan uwa da abokan arziki. Sannan kuma mijina ma ya na mara mini baya akan haka.”
Jarumar ta ce wannan kungiya na ta zai ci gaba da taimakawa talakawa da marasa galihu ba a Kano ba kawai har ma da wasu jihohin kasar nan.
“ Yanzu haka muna zazzagayawa jihohi dabam-dabam domin taimaka wa mutane marasa galihu. Kwanannan muka dawo daga wasu garuruwa a jihar Kaduna sannan kuma za mu tafi wasu a jihar Neja domin ci gaba da wannan aiki da muke yi.
Da PREMIUM TIMES HAUSA ta tambaye ta game da rayuwa a gidan aure, Mansurah ta ce babu abin da za ta ce sa Hamdala domin Allah ya bata miji nagari mai son ta.
“ Ni dai sai in yi ta yi ma Allah godiya domin ya bani miji nagari mai sona. Shekara 10 kenan da yin aure amma kullum sai dai inji son sa ya karu mini ba dai ya ragu ba. Ko da sabani muka samu wallahi za ka ga kamar ba haka ba.
“Kullum addu’ar sa gareni shine in zama mata salaha mai tsoron Allah. Yana bani duk wata kula da nike bukata da ‘ya’ya na sannan kuma mai tausayi ne sosai. Ni dai zan iya cewa Sani Danja kamar Jini ne yanzu a jijiyoyi na. Yadda nake son sa haka yake sona da ‘ya’yan mu.
Da aka tambayeta ko akwai wani abu da take ganin bata cimma ba lokacin da take harkar fim Mansura tace “ Babu wani abu da ni ke tunanain ban samu ba a fim. Ta harkar fim na gina gida na, na siya motar kai na, na tafia iakin Haji sannan karshe kuma na auri Jarumi, toh me ya rage, ai sai hamdala ko.”
Bayan haka Kuma tace it ace ‘yar wasan fim mace ta farko da ta iya hada hotuna tun a wancan lokacin.
“ Ni tun farko daman na shiga farfajiyar fina-finai a matsayin mai hada hotuna ne wato Bidiyo Edita sai daga baya na fara shiga fim.” Inji Mansurah.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment