Shirin fim na farko da jarumar masana'antar shirya fina-finan hausa ta kannywood Rahama Sadau ta dauki nauyin fitarwa ya amshi lambar yabo a gasar City people Award na 2017.
"Rariya" tayi fiko akan "Yar fim" "Mansoor" , "Dan kuka" da "Zinaru" wajen zama mafificin fim daga masana'antar kannywood na bana.
A gasar City people awards wanda aka gabatar a garin Legas 8 ga watan Octoba manyan jaruman kannywood da dama sun amshi lambobin yabo game da irin rawan da suka taka wajen fitar da fitattun fina-finai bana.
An gabatar da shirin "Rariya" 26 ga watan Yuni a garin Kano da Abuja kuma tun da aka gabatar da ita ta samu haskawa a jihohi da dama a Arewacin
Nijeriya .
Nijeriya .
Shirin wanda Yaseen Auwal ya bada umarni na bada labarin wasu yan matan jami'a da irin rayuwar da suke yi a makaranta.
"Rariya" ya siffanta irin sauyi na zamani da aka samu na kayan sawa da ake yayi, da irin na'urorin zamani da ake kawance dashi har ma da rayuwar karya da wasu dalibai keyi a makaranta.
Jarumai masu tauraro da suka haska a cikin shirin sun hada da Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Hafsat Idris, Fati Washa, Maryam Booth da sauran su.
Za'a sako "Rariya" ga DVD nan ba da jimawa ba.
Za'a sako "Rariya" ga DVD nan ba da jimawa ba.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment