Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta bayyana dalilin ta na kafa gidauniyar 'Todays life Foundation' - NewsHausa NewsHausa: Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta bayyana dalilin ta na kafa gidauniyar 'Todays life Foundation'

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 25 October 2017

Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta bayyana dalilin ta na kafa gidauniyar 'Todays life Foundation'



- Ta ce tausayi yara dake gararamba a gari ne yasa ta kafa wannan gidauniya

- Ta kuma ce tana taimaka wa yara marasa galihu da mata da mazajen su suka rasu

Tsohuwar jaruma wacce ta shahara a dandalin Kannywood a lokacin baya, Mansurah Ish, ta fayyace dalilan da suka sanya ta kafa gidauniyar “Todays life Foundation”

A cewar Mansura ta kasance mai tausayi da ganin halin da wasu mutane ke shiga musamman abin da ya shafi rashin abin da za su ci ma kawai hakan ya sanya ta kafa gidauniyar domin ta bayar da nata gudunmuwar sannan kuma ta tallafawa yara dake yawo a gari ta hanyar taimakawa iyayen su da su kansu a sa su makaranta.

“Na kafa wannan gidauniya domin tallafa wa marasa karfi, matan da suka rasa mazajen su da kuma yara kanana. Na yi haka ne domin bada gudunmuwa ta ga mutane da ke cikin mawuyacin hali."


Mansura ta ce gidauniyar ta na samun kudaden ta ne ta hanyar tallafi da kyauta da ta ke samu.

Jarumar ta ce wannan gidauniya na ta zai ci gaba da taimakawa talakawa da marasa galihu ba a Kano ba kwai har ma da wasu jihohin kasar nan.



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment