Za A Fara Nuna Fim Ɗin Tarihin Shehu Ɗan Fodiyo A Bauchi - NewsHausa NewsHausa: Za A Fara Nuna Fim Ɗin Tarihin Shehu Ɗan Fodiyo A Bauchi

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 17 October 2017

Za A Fara Nuna Fim Ɗin Tarihin Shehu Ɗan Fodiyo A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Shahararen kamfanin nan mai suna I.M Production ya shirya tsaf domin fara nuna gami da kaddamar da wani gagarumin fim na tarihin mujaddadi Shehu Usmanu Bn Fodiyo wanda aka shafe tsawon shekaru sama da 14 ana faɗi tashin samar da shi, wannan gagarumin fim na tarihin mujaddadin. Hanzari ya zo kusa, domin kamfanin ta kammala ɗaukan fim ɗin gami da tsarawa da kuma fitar da shi, za a fara nuna wannan fim ɗin tarihin ne a Jihar Bauchin Yakubu, inda ma suka bayyana cewar wannan fim na tarihin nan gaba ɗakan zai shiga kasuwa.

To sai dai, a shekaran jiya asabar ne jagororin shirya fim ɗin tarihin Shehu Ɗan Fodio suka kai ziyara wajen Sarkin Bauchi Alhaji (Dk) Rilwanu Sulaiman Adamu domin neman goyon bayan masarautarsa da kuma kaddamar da fara nuna wannan fim ɗin a cikin garin na Bauchi, inda masarautar nan take ta amshi shirin hanu biyu-biyu, inda ta ce a shirye take ta mara baya wajen fara nuna wannan tarihin mai tarin fa’ida da kuma alfanu ga duniya baki ɗaya.

A yayin ziyarar, Ali Babba wanda shi ne mai duba yanayin ɗaukan fim ɗin ‘Furudusa’ ya fara ne da bayyana cewa a gaban Sarkin cewar sun zaɓin jihar Bauchi a matsayin jihar da za a fara nuna wannan tarihin ne a bisa alaƙar da masarautar Bauchi ke da shi da wanda aka shirya fim ɗin domin tarihin rayuwarsa wato Shehu Ɗan Fodio. Ta bakinsa “Zaɓinmu na wannan Masarautar Bauchi domin fara nuna wannan ‘fim’ sakamako ne na matsayin masarautar Bauchi a tarihin daular Shehu Usman bin Fodiyo. Lallai ba mu ko shayi cewar tsayuwarmu nan kamar muna tsaye ne a gaban Shehu, tarihi ya nuna matsayin fadar Bauchi a wajen daular Shehu”. Ta bakinsa

Ya ci gaba da cewa “Masarautar Bauchi ita ce masarauta ɗaya tilo da Shehu Usman ya bada dama kai tsaye a bada tuta, wannan masarautar ita ce ta ƙaryata waɗanda suka so su danganta jahadin Shehu Ɗan Fodiyo da cewa jihadin Fulani ne, wannan masarauta daga cikinta ne  Shehu bai bar Yakubun Bauchi ya taho ba sai da ya haɗa sa da jininsa”. A cewar Firedusan fim ɗin.

Ya ce a bisa waɗannan matsayi da kuma kimar da masarautar Bauchi take da shi a tarihin daular Shehu Ɗan Fodiyo ne ya sanya su suka zaɓi garin domin fara nuna wannan fim ɗin, wanda za a fara nan bada jimawa ba.

Da ya ke bayanin yanda suka fara shirin fim tarihin Ɗan Fodiyon kuwa Ali Usman Babba ya ce, “Bayan da muka samu wasu tsare-tsare na shirin mun je fadar Sultan a lokacin Mociɗo wanda muka gabatar da kanmu da kuma aiyukan da muke da shirin yi. Ya amshemu hanu biyu-biyu, ya kuma haɗamu da waɗanda za mu samu tarihi a hanunsu. Sannann mun je jami’ar Sokoto nan ma maka yi bincike, sannan mun je ABU, BUK sannan kuma mun bi wasu masana tarihi a ɗaiɗaikunsu domin fitar da tarihin yanda ya ke”.

Ya ce daga ƙarshe dai sun nemi wani littafin da ya jibinci tarihin Shehu ɗin ne idan suka gina labarin fim ɗin nasu a kansa domin ci gaba da tsara shirin “Mun gina labarin wannan fim ɗin ne da wani littafi mai suna ‘IFAƘUL MANSUR’ na Sarkin Musulmi Muhammdu Bello ɗan Shehu Usman bin Fodio”. A cewarsa

“Tarihin cewa Usmanu dai shi ne mu, domin kowace al’umma tana alfahari da tarihinta ne, kuma da tarihin tane take ɗabbakuwa har ta ci gaba”. A cewarsa

Ya ce duk da girman aikin sun jure inda suka kwashe shekaru sama da sha huɗu suna faɗi tashin fitar da shi “mun yi abubuwa da yawa, an ɗauki wannan fim ɗin a ƙasashe irin su Nijer, a Nijeriya mun zagaya wurare daban-daban domin gudanar da shi”.

Da ya ke bayyana wa Sarkin na Bauchi irin ƙalubalen da suka fuskanta a wajen shirya wannan fim na tarihin Shehu Ɗan Fodiyo kuwa, Ali Baba ya ce sun fuskanci ƙalubale marar musaltuwa “Mun fuskanci ƙalubale sosai masu tarin yawa, domin duk abun da ya ɗauki tsawon wannan lokacin dole akwai ƙalubale, misali irin fadojin da za mu yi amfani da su, wasu irin gine-gine ne waɗanda babu irinsu a yanzu a wannan zamanin dole ne sai da muka koma sai mun gina fadojin nan sannan a yi kwaikwayin ‘Acting’  yanda ake so a ciki, sannan kuma ga yawan mutane da aka yi amfani da su, domin ko wajen shirya yaƙi dole ne ka nemi mutane da yawa, sannan ga ɗibansu daga inda suke zuwa inda za tsara yaƙin da kuma ɗaukan fim ɗin, ga ciyar da su, ga kayyakin da za a sanya wajen sajewa da kuma alamta zamanin Shehu ɗin, daidai da tarihin yanda yake, an dai sha aiki sosai, amma zuwa yanzu Allah ya daba yanzu haka an riga an kammala wannan fim ɗin, wanda an kaisa ne har zuwa cin Alƙalawa a daidai wajen ne muka tsaida shi wannan shirin na tarihin Shehu Ɗan Fodiyo”. A cewarsa

Da shugaban mai sanya ido wajen ɗaukan shirin ya bayyana irin kuɗaɗen da wannan fim ya lashe kuwa, ya bayyana cewa sun kashe miliyoyin kuɗi wajen gudanarwa da kuma tabbatar da tarihin ya samu kammaluwa da tsaruwa yanda ya dace “Wannan shirin ya lakuɓe mana kuɗi banda gine-ginen da muka yi, wasu gine-gine da ya ke na ƙasa ne ruwa ya zo ya zubar, mu sake tada su wasu kuma mu sake ginawa, gaskiya ba mu iya kiyasce nawa gine-gine suka ci mana ba. mun iya kashe kuɗin da bai yi ƙasa da miliyan tamanin 80 wajen shirya wannan fim ɗin, banda aiyukan gine-ginen da muka yi”. A cewarsa

Ya bayyana cewar a bisa haka ne suke neman haɗin guiwar masarautar Bauchi gami da zaɓan jihar Bauchi a matsayin jihar da za a fara nuna wannan shirin na tarihin Shehu Usman bin Fodiyo Rahimahullahu “A don haka muke rokon dukkanin goyon baya daga wannan masarautar wajen ganin mun yi nasara wajen isar da wannan  fim na tarihi ga al’umma”. In ji Firedusan fim ɗin.

A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji (Dr) Rilwanu Sulaiman Adamu ya bayyana wannan aikin da kamfanin I.M Production ta gudanar a matsayin wani jahadi da ladarsa kawai sai a wajen Allah ya kuma bayyana cewa duniya baki ɗaya ne za ta amfana da wannan tarihin ganin yanda tarihi ke da matuƙar muhimmancin “Wannan ƙoƙarin na ku ba kawai wa al’umman Nijeriya akɗan kuka yi ba, Afrika baki ɗaya ma za su amfana da wannan. wannan ƙoƙari da jajircewa da kuka yi zai taimaka, ƙalubale da ka fuskanta”.

Hakazalika Sarkin na Bauchi ya ci gaba da bayyana muhimmancin da tarihi ke da shi wa jama’a “A lokacin da muke rayuwar Sakandari muna kallo masu ilimin tarihi a matsayin masu karatun ƙarya, suna karanta abun da ba su gani ba. amma idan mutum ya ga abu a cikin sigar tarihi koda bai kasance a lokacin ba ya san an yi wannan abun, don haka wannan tasirin wannan fim ɗin ina mai tabbatar muke Allah ne kaɗai ya san irin amfanun da wannan fim ɗin zai yi, haɗainiyar da aka sha kuma sai mu ce kamar jahadi ne Allah ya zaɓeku kuka yi, dukkanin ɗawainiyar da kuka yi baku faɗi ba”.

Dakta Rilwanu, kuma Sarkin garin na Bauchi ya ci gaba da cewa, wajibi ne a yi godiya wa Allah maɗaukakin Sarki a bisa kammala wannan shirin, haka kuma ya nuna godiya ga Sarkin Musulmai Allah Sa’ad Abubakar a bisa shawarar da ya bayar na zo Bauchi domin fara nuna wannan shirin na tarihin Shehu Usmanu “A bisa shawara da ya bayar kasancewar yanda fadar Bauchi take a masarautar daular Usmaniyya, ya bada shawara a zo Bauchi a fara nuna wannan shirin, muna godiya, muna godoya muna kuma alfahari da kasancewar hakan, kuma fatan Allah ya ya kawo dukkanin taimakonsa cikin wannan al’amarin”. Ta bakin Sarkin

Masautar Bauchi sai ta bayyana aniyarta na mara baya domin kaddamar da wannan shirin mai tarin fa’ida “Muna shirye mu bada dukkanin goyon baya da kuma tallafi gwargwadon hali”. Ta bakin Sarkin

Haka kuma Sarki, Rilwanu ya yi fatan Allah ya sa a fara nuna wannan tarihin cikin nasara haɗe da yin addu’an wasu su yi koyi da wannan na mijin ƙoƙarin da I.M ta yi wajen fitar da wannan tarihin mai tarin fa’ida da kuma isar da sako wa al’umman duniya.

Sayyid Muhamamd Ibrahim ɗaya daga cikin manyan Daraktocin wannan fim ɗin ya gabatar wa Sarkin Bauchi fuskokin wasu daga cikin haziƙan jaruman da suka taka lawa wajen ɗaukan wannan shirin, inda ya nuna masa kaɗan daga cikinsu waɗada suka fito a matsayin Abdullahi Gwandu, Shehu Ɗan Fodiyo, da kuma jaruman da suka fito a Sarkin Gobir NaFata, Umaru Ma’alkamu, da sauran waɗanda suka fito. A cikin shirin na tarihin Shehu  Ɗan Fodiyon, wanda nan bada jimawa bane za a fara nuna wannan shirin gami da kaddamar da shi a jihar Bauchi. haka kuma ya nuna masa samfurin kaladar fim ɗin.

Ya zuwa yanzu dai shirye-shiryen fara nuna wannan shirin na tarihin Shehu a jihar Bauchi ya yi nisa domin kuwa zaƙaman haziƙan da suka yi hidima wa shirin suna nan suna ci gaba da duba yanda za a yi wajen inganta fara nuna wannan shirin, a bisa haka ne suke bayyana aniyarsu ne neman goyon bayan masu ruwa da tsari ganin yanda shirin tarihin ked a matuƙar muhimmanci a daidai wannan lokacin.

Sources :-hausa.leadership.ng

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment