Ita de wannan tambaya kamar yadda suke fada tambaya ce ta tarihi kuma tarihi miscellaneous ne wato abunda bai da muhimmanci sosai, babu laifi idan mutum bai sani ba idan ba ikirarin malumta yake ba. Amma mutum Aami wato mutum na gama gari ba dole ba ne ya sani. Tarihi dai zaizo ne a mataki da uku bayan Aqeedah da Ibadaat wato abubuwa da suka shafi imani da aikace aikace (kamar tsarki, sallah) da sauran su. Kuma idan mutum ya nakalci abu biyun nan ba abunda zai taba musuluncin su.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment