Kannywood:- Mai Rahama Sadau ke shiryawa a kasar Cyprus? - NewsHausa NewsHausa: Kannywood:- Mai Rahama Sadau ke shiryawa a kasar Cyprus?

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 11 October 2017

Kannywood:- Mai Rahama Sadau ke shiryawa a kasar Cyprus?

Jarumar fina-finai hausa na masana'antar Kannywood ta sanya alamun tambaya ga kowa kasancewar ta a ƙasar Cyprus.

A cikin hotunan da  hausaloaded ta samu zaku gan inda tauraruwar fina-finan hausa na dandalin kannywood take taya yan Nijeriya mazaunin ƙasar har da dalibai murna a bikin murnar ranar Nijeriya a ƙasar.

ganin hoton muke tambaya; wata kila taje ƙasar domin shirya wani sabon fim bayan shirin RARIYA wanda ta shirya da kanta wanda yayi tasiri a kasuwa.
Ko kuma ta tafi hutu ne ganin ƙasar tana da wuraren hutawa da shakatawa?

Rahama wanda ta samu fitowa cikin sabbin shirin Nollywood TATU da Hakkunde kuma ta samu matsayi a shirin MTV Shuga tana morewa da nasarorin data samu sanadiyar basirar ta a harkan fim.

Ku kasance tare damu domin samun asalin dalilin da ya kai ta ƙasar turai.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment