NewsHausa: ISLAM NewsHausa: ISLAM

Pages

LATEST POSTS
Showing posts with label ISLAM. Show all posts
Showing posts with label ISLAM. Show all posts

Friday, 24 November 2017

Wa'azin IZALA a kasashen Turai Da Lokutan Da Zasuyi Wa'azi a ko wace Kasa Kamar Yadda Wannnan Hotunan Ya Nuna


Daga Ibrahim Baba Suleiman

Kamar yadda kuma sani Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau, tare da Sakataren Izala Na kasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, suna kasashen Turai domin gudanar Da'awa a wannan yanki.

A halin yanzu suna Kasar London, daga bisani kuma zasu shiga zuwa kasashen Germany, France, Belgium, Holand, Italy, Spain, da Greece,  domin aiwatar da aikin Da'awa a wadannan kasashe.

Kungiyar Wa'azi ta Izala a Naijeriya tare da kungiyar Wa'azi ta ''Sautus Sunnah dake kasashen Turai ne sukayi Hadin Gwuiwa domin gabatar da wa'azozin. 

Manufar Ziyarar dai itace, Wa'azi zuwa ga 'yan uwa Na wadannan kasashe, musamman ma 'yan Afurka da suke da Zama a can, da kuma saduwa da cibiyoyin ahlu sunnah na kasashen turai (Europe) Kamar kungiyar 'Sautus Sunnah' mai wa'azin musulunci, da Kira a tsaida Sunnah tsantsa, a fatattaki Bidi'ah, wadanda suke da Zama a can, saboda hada karfi da karfe wajen Da'awa.

Kungiyar ta Sautus-Sunnah Sukanyi taro lokaci bayan lokaci a yankin, kuma a wannan karon sun gayyaci kungiyar Izala ta Kasar Naijeriya domin su shiga wadanan kasashe a ci gaba da Wa'azi ba kakkautawa. 

 Allah ya bada sa'ar Da'awa, yasa a samu gagarumar Nasara.

Tuesday, 20 June 2017

Darikar Tajjaniyya Da Shi'a Duk Daya Ne, Cewar Sheik Dahiru Bauchi


Shahararren malamin nan Sheik Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa Darikar Taijjaniyya da Shi'a duk daya ne.

Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a yayin da ya karbi bakoncin tawagar wasu mabiya Shi'a a gidansa dake Kano.

Ya ce da Shi'a da Darikar Tijjaniyya duk tafarkin Annabi (S.A.W) suke bi kuma masoyan iyalansa ne. Ya kara da cewa babu wani bambanci tsakanin akidun biyu.

"Da Shi'a da Darikar Tijjaniyya duk daya ne saboda dukkansu suna bin tafarkin Annabi (S.A.W) ne kuma masoyan iyalansa.

"Duk mulumin kwarai ya zama dole ya yi imani da Annabi (S.A.W) da kuma nunawa iyalansa kauna. Don haka dukkanmu mun iya imani da shi. Don haka daya muke" cewar Shehin Malamin.

Ya kuma yabawa tawagar Shi'an kan ziyarar da suka kawo masa, inda ya bayyana hakan a matsayin wata hanya ta hadin kan musulmai.

Tun a farko, jagoran tawagar mabiya Shi'an, Malam Yakubu Yahaya, ya bayyana cewa makasudin kawowa Shehin Malamin ziyara shine don taya shi murnar kammala tafsirin azumin Ramadan na wannan karo da ya yi.

Sources:Rariya

Wednesday, 14 June 2017

Bajintarsa A Gasar Kur'ani Ta Sa Limamin Harami Ya Sumbace Shi Daga Abu Abdur

Bajintarsa A Gasar Kur'ani Ta Sa Limamin Harami Ya Sumbace Shi

Daga Abu Abdurrahman

Limamin Harami Shaykh Sudais ya sumbaci goshin yaron nan (Amer Falatah) ya kuma fada masa cewa insha Allah shine zai zama limamin Harami nan gaba.

Wannan yaro dan Albarka wanda ya zama abin Alfahari ga mahaifansa, Musulinci da musulmin duniya ya taka rawar gani a musabukar Alqur'ani ta Duniya.

Ameer Falatah dan kasar Malawi shine ya zo na daya a gasar karatun Kur'ani na duniya da aka gudanar.

Da wannane muke kara kira ga iyaye lallai a rage fifita karatun boko na yara sama da karatun Addini 

Domin halin da muke ciki yanzu akwai bukatar kowa ya yi tunani gina al'umma ta gari, mu fara daga gidajen mu, 

✔Kayi tunani da kanka wai shin a family dinku kuna da background na ilimin addini ? 

✔Idan babu ka fara tsarawa daga 'yay'anka, don kuma ku shiga cikin mafificiyar al'umma. Shima ilimin zamanin yana da amfanu, amma kar a nunawa yara tun suna kanana cewa ilimin bokon yafi daraja. 

Domin Allah (SWT) yayi yabo na musamman ga bayinsa masu haddace Alqur'ani a cikin littafinsa yake cewa:

*"بل هو ايات بينا ت في صدرالذين اوتواالعلم"* 

Ku saurari karatun yaronnan....subunallah

©Rariya

Friday, 9 June 2017

Matasan Musulmi Da Ke Wurin Horaswar Soja,Suna Iya Ajiye Azumi Daga Baya Su Rama-inji MallamBashir Ahmad Sani Sokoto

MATASAN MUSULMI DA KE WURIN HORASWAR SOJI, SUNA IYA AJIYE AZUMI DAGA BAYA SU RAMA, IDAN HAR DON ALLAH SUKE YI, CEWAR MALAM BASHIR AHMAD SANI SOKOTO

DAGA Mukhtar A. Haliru

MALAM BASHIR AHMAD SANI DAKE GABATAR DA TAFSIRIN SA A MASALLACIN ALIYU BN ABI DALIB DA KE UNGUWAR KOKO CIKIN GARIN SOKOTO, A WAJEN TAFSIRIN DA YAKE GABATARWA, YA AMSA WATA TAMBAYA DA NEMAN SANIN HUKUNCIN MATASA DA KE WURIN DAUKAR HORASWAR SOJI, INDA MALAMIN YA YI CIKIAKKEN BAYANI KAMAR HAKA;

"AKAN (TRAINING) HORASWAR  NA SOJOJI, WASU MALAMMAI NA KIRA GA GWAMNATOCI CEWA DAN ALLAH A DAGE SAI BAYAN AZUMI",

 YA CE A NASA GANIN "BAMA SAI AN YI HAKAN BA INDAI DAN ALLAH MUTUM ZAI YI, TO YA SHA AZUMIN YA JE YA YI TRAINING DIN BAYAN SALLAH SAI YA JE YA RAMKA, KUN GA INDAI AN YI HAKAN DA NIYAR SHARRI ANA GANIN AN YI HAKA NE DA NIYAR MUSULMI SU KASA, TO IN SUN GA MUSULMI SUN AJIYE AZUMI BAYAN SALLAH SUN RAMKA, WATA SHEKARA BA SAI AN ROKE SU AN CE DAN ALLAH BA, SU DA KAN SU BA ZA SU YI BA,".

 MALAMIN YA KARA DA CEWA "ADDININ MUSULUNCI ADDINI NE MAI SAUKI MATAFIYI AI AN SAUWAKE MAI AN CE YA AJIYE AZUMI, TO INA GA MAI IRIN WANNAN AIKIN, JIHADI NE AMMA GA WANDA YA YI SABODA ALLAH"

©Rariya

Tuesday, 30 May 2017

Wata Magana Mai Ratsa Zuciya Da Marigayi Sheik Jafar Mahmud Adam Ya Fada Daf Da Za A Kashe Shi

Wata Magana Mai Ratsa Zuciya Da Marigayi Sheik Jafar Mahmud Adam Ya Fada Daf Da Za A Kashe Shi

"Idan kai kana ganin baka shirya ka mutuba, to idan ina karatu, ko huduba, ka daina zuwa sahun gaba, saboda idan an harbe ni, kada jini ya fallatsar maka a shaddarka da kake sawa kake ado da ita"

Hakan kuwa aka yi, domin a ranar wata Juma'a yana Limancin Sallar Asuba, wasu suka shiga sahun Sallar, kuma suka harbe shi.

Allah jikan Malam ya masa rahama. Amin.

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

Sunday, 12 March 2017

Kungiyar Izala Zata Zagaya Jihohin 37 Harda Abuja A Tarayyar Nigeria

Kungiyar Izala zata zagaya jihohi 37 harda Abuja a tarayyar Naijeriya 

Daga: Ibrahim Baba Suleiman 

A ranar alhamis dinnan mai zuwa (16/3/2017 (wato 17/6/1438AH) in sha Allah. Kungiyar Izala zata fara zagaye zuwa wajen 'ya'yanta a jihohi 37 harda Abuja da ke fadin kasar Naijeriya

Shugaban kungiyar ta tarayyar Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ya shaidawa manema labarai cewa, kungiyar zata zagaya zuwa jihohin ne domin ganin yadda ayyukan kungiyar suke tafiya a lungu da sako tare da wasu birane na sassan kasar.

Zagayen wanda za'a fara da jihohin Bauchi, Gombe, Adamawa da taraba, Manufar zagayen shine 'Karantar da masu wa'azi' domin inganta harkokin Da'awa zuwa ga wadanda basu fahimci addinin islama ba, tare da farfado da harkokin ilimi a makarantun Islamiyya da dai sauran su.

Jadawalin zagayen na farko zai kasance kamar haka;
Kwana daya aka kebewa kowace jiha. 

Jihohin farko sune-
Bauchi 16/3/2017, 
Gombe 17/3/2017,
Adamawa 18/3/2017 
Taraba 19/3/2017. 

Tawagar da zasu raka Shugaba Sheikh Bala Lau ta hada da wasu shugabanni, Malamai da daraktocin kungiyar a matakin kasa,  zata sauka a birnin Bauchi da misalin karfe 12 na ranar Alhamis 16/3/2017 in sha Allah.

Sanarwa daga ofishin babban sakataren kungiyar ta kasa, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe.

#Jibwis_Nigeria
13/Jumada Awwal/1438
12/March/2017

Tuesday, 7 February 2017

Dr Muhammad sani Umar R/lemo -Yayin da yake Karba Kyauta Daga Madina(cikin hoto)

Sheikh Dr. Muhd Sani Umar Rijiyar Lemo kenan yayin da yake karbar kyautarsa daga Sheikh Abdurrahman Arragdadiy Shugaban sashen Shari'a na Jami'ar Musulunci ta Madina, daren jiya Litinin 06 Feb 2017.

Sunday, 5 February 2017

Tarihin Muhammad Auwal Abu Abdirahaman Albaniy Zaria[Rahamahullah]

Tarihin Muhammad Auwal Adam Abu Abdirrahaman Albaniy [Rahamahullah]



Sunana: Muhammad Auwal
Sunan mahaifina :Adam
Sunan mahaifiyata: Saudah
Abu Abdirrahman shine Alkunyata
Albaniy shine laqabina

An haifeni a unguwar Muciya sabon garin Zaria a shekarar 1960.

Nayi makarantar Allo har nayi sauka
Na koyi litattafan da akeyi a zaure na fiqhu dana Lugah da Adab
Nayi karatu a wurin manyan malamai mabanbanta a kasata Nigeria da kasashen waje inda na koyi Qur'ani da dukkan kira'o'insa, hadisi da musdalah dinsa, tafsiri da usul dinsa, harshen larabci da fannoninsa, fiqhu da usul da Qawa'id dinsa d.s.

Nayi makarantar firamare a sabon garin Zaria
Nayi sakandare a kwalejin barewa Zaria
Nayi Diploma akan:

Law

Computer science

Mass Communication

Hausa Language

Nayi Degree akan ICT

Nayi Masters akan Islamic studies

Ni Professional journalist ne

Ni Certified microsoft engineer ne

Ni Linguistic ne

Na karanci library science

Nayi programme na N+ akan Computer

Nayi Programme na A+ d.s

Ina da company wanda yake gabatar da ayyuka a fannoni dabam-dabam
Na karantar da litattafai kusan dari a rayuwata a fagage da fannoni mabanbanta
Na gabatar da laccoci dabam-dabam a gida Nigeria da kasashen ketare
Na fassara litattafai na musulunci masu yawa.

Nayi tahqiqin litattafai da dama
Na gina cibiya mai suna Darul-Hadeethissalafiyyah Zaria Nigeria (DHSN) wadda a karkashinta akwai makarantu kamar:

Albaniy science international Academy (pre-nursery, nursery, primary da secondary) na bangaren maza dana bangaren mata

Daaru Ibn Katheer Litahfeezil Qur'an
Sheikh Nasiruddeenil Albaniy College of Higher Islamic studies.

Na fara gina jami'a mai suna Albaniy University of Information and Communications Technology

Na fara gina gidan marayu

Na samar da inda zan gina asibiti

Na samar da inda zan gina gidan rediyo da talabijin.

Na samar da dakin karatu (library) domin anfanar malamai da daliban ilmi

Ni mutum ne mai son cigaban al'ummata ta hanyar ilmi da wayewa
Manzon Allah (saw) shine mai gidana
Banayin sassauci ko daga kafa akan duk abinda ya sabawa Qur'ani da sunnah a bisa manhajin magabata na kwarai, amma ina yin hakan tare da duba yanayi, wuri da kuma halayen mutane
Daga cikin sana'o'ina akwai:

Dinki

Kanikancin computer (computer engineer)

Mashawarci a harkar computer (computer consultant)

Computer networking

Aikin jarida

Kasuwanci maban-banta
Aikin rubuce-rubuce d.s

Duk abinda na assasa a rayuwata da kudina na samar dasu domin ban dogara da kowa ba bayan Allah Mahaliccina, sannan sai sana'o'in da nakeyi
Nayi waqafin abubuwa dana assasa baki dayansu gareni domin anfanar al'ummar musulmi

Babban manufata shine sharewa musulmai hawaye game da matsalolin da suke fama dasu na addini da rayuwa a fannoni daban-daban a karkashin mahanga na addinin musulunci

Nasan wadanda suka kasheni da wadanda sukasa a kasheni, amma KASH! bazai yiwu indawo duniya in bayyanasu ba! Amma Ubangijinmu yana nan a madakata yana jiranmu a inda ranar Alkiyamah zan shako wuyansu na gurfanar dasu a gaban Allah Sarkin sarakuna ince Ya tambayesu don me yasa suka kashe ni....?

Ina rokon Allah Yajikaina
Yayi mini rahma
Ya yafe mini kura-kuraina
Ya karbi shahadata
Ya hadani da Maigidana Manzon Allah (saw) a Aljannar Firdausi da sauran musulmi baki daya.
Ameeen.

Friday, 27 January 2017

Innah lillahi wa'innah Alaihi raju'un:Allah yayiwa Sheikh muhammad Rabiu Daura Rasuwa

Innah lillahi wa'innah Alaihi raju'un

ALLAH yayiwa babban mallamin nan kuma jigo na kungiyar izalatuh bidi'ah wa'ikamatus sunnah Allah yayi wa sheikh muhammad Rabi'u Daura Ratsuwa a yau.

 SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau yana gayyatar 'yan uwa musulmi zuwa wajen jana'izar Daya daga Cikin dattawan wannan kungiya da ya rasu a yammacin juma'ar nan Marigayi Sheikh Muhammad Rabi'u Daura

Za'a gabatar da Jana'izar ne a  Masallacin Danfodio Dake unguwar sunusi a garin kaduna da misalin karfe tara na safe in Allah ya kaimu. 

Sheikh Abdullahi Bala Lau, Sheikh Kabiru Gombe, Sheikh Abdulbasir Isah U/maikawo tare da sauran manyan Malamai tuni sun isa birnin na Kaduna a shirye shiryen fara jana'izar Malam. 

Allah ya gafarta masa ya saka Ladan aikin da ya yiwa addini a mizani.  Amin.

Wednesday, 25 January 2017

WA'AZIN KASA A ANKPA, KOGI STATE 2017

WA'AZIN KASA A ANKPA, KOGI STATE 2017

Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau

Shugaban Majalisar Malamai Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

Daraktan agaji Injiniya Mustapha Imam Sitti

A madadin kungiyar Jama’atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunna ta tarayyar Najeriya, suna farin cikin gayyatar 'yan uwa musulmi zuwa wajen wa'azin kasa a garin Ankpa, dake jihar Kogi a ranakun asabar da Lahadi 28/29/January/2017. Insha Allah.

Ana san ran halartan:

-Sheikh Dr. Alhassan Sa'id Adam Jos
-Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina
-Sheikh Abbas Muhammad Jega
-Sheikh Habibu Yahaya Kaura
-Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe
-Sheikh Abubakar Giro Argungu
-Sheikh Barista Ibrahim Sabi'u Jibia
-Sheikh Abdulbasir Isah U/Maikawo
-Khalid Usman Khalid Jos
-Sheikh Abdullahi Telex Zariya
-Ustaz Abdussalam Abubakar Baban Gwale
-Ustaz Ibrahim Idris Zakariyya Jos
Da
-Alaramma Abubakar Adam Katsina
-Alaramma Ahmad Suleiman Kano
-Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
-Alaramma Abdulkarim Akwanga
-Alaramma Bashir Gombe
-Alaramma Isma'il Maiduguri
-Alaramma Ilyas Birnin Gwari
-Alaramma Usman birnin kebbi
-Alaramma Ibrahim Yahuza Bauchi

Masu masaukin baki:

Shugaban JIBWIS na jihar kogi, Alh. Yahaya Dalladi Musa, da

Sheikh Suleiman Adam (Chief Imam Ankpa)

NB/ Ana bukatar kwararrun direbobi su ja ragamar tafiyan, musamman ga masu bi ta hanyar Akwanga. Allah ya kiyaye hanya, ya bada ikon zuwa da nasarar abun da akaje yi. Amin.

Sanarwa daga ofishin sakataren kungiyar ta kasa, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe.

JIBWIS NIGERIA

Friday, 20 January 2017

An Bude Katafaren Masallacin Da Sanata Kabiru Gaya Ya Gina A Abuja a cikin (Hotuna)

An Bude Katafaren Masallacin Da Sanata Kabiru Gaya Ya Gina A Abuja

Shugaban kungiyar JIBWIS na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau  ya gabatar da wa'azi kafin zuwan liman, inda Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II ya gabatar da khuduba da Sallar Juma'a.

Gwamna jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya halarci bude katafaren masallacin juma'a wanda Mai Girma Sanata Kabiru Gaya ya gina a unguwar Wuse Zone 6 dake babban birnin tarayya Abuja.

Sauran manyan baki sun hada da shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki wanda Sanata Yarima Bakura ya wakilta da Ministan Sadarwa Adebayo Shittu da Mai Girma Sanata Barau Jibrin da yan majalisar dattijai da ta wakilai da Alhaji Dahiru Mangal da kuma sauran alumma Musulmi.

A jawabin sa Sanata Kabiru Gaya ya yi godiya ga wadanda suka taimaka wajen gina wannan masallacin juma'a wanda shine na farko a unguwar ta Wuse Zone 6. Inda ya yi kira ga alummar Musulmai da su cigaba da taimakawa dan gudanar da masallacin da sauran masallatai.

Allah ya sanya albarka. Amin.








posted by Abubakar Rabi'u

Monday, 14 November 2016

LABARI MAI DADI:WA'AZIN KASA A JIHAR SOKOTO!!!!

WA'AZIN KASA A JIHAR SOKOTO!!!
Shugaban Kungiyar Izalar Naijeriya,
Ash'Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau
Shugaban Majalisar Malamai, Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Daraktan 'Yan Agaji, Injiniya Mustapha Imam Sitti
A madadin kungiyar Jama’atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunna ta tarayyar Najeriya, Na gayyatar jama'a zuwa gagarumin wa'azi na kasa da za a yi Insha Allah a Sokoto cibiyar daular Usmaniyya ranar asabar 19 zuwa lahadi 20 ga watan nan na Nuwamba 2016 mai taken "GUDUNMAWAR MALAMAN ISLAMA WAJEN YAKI DA CIN HANCI DA RASHAWA "
A lokacin wannan wa'azi da malamai da alarammomi za su gabatar.
Dr.Mansur Ibrahim Sokoto zai gabatar da makala mai taken “ Gudunmawar daular Usmaniyya wajen yada Sunnah a nahiyar Afurka"
Sai kuma Prof. Isa Maishanu Yabo zai gabatar da takardar sa mai taken "Gudunmawar malaman Islama wajen yaki da cin hanci da rashawa"
Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe zai gabatar da na sa wa’azin da taken "Cin hanci da rashawa katafilar rushe al'umma"
Sauran Malaman da Ake sa ran zasu gabatar da wa'azi sune:
-Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe
-Sheikh Dr. Alhassan Sa'id Adam Jos
-Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina
-Sheikh Abbas Muhammad Jega
-Sheikh Habibu Yahaya Kaura
-Sheikh Rabi'u Aliyu Daura
-Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan
-Sheikh Barr Ibrahim Sabi'u Jibia
-Sheikh Abubakar Giro Argungu
-Sheikh Khalid Usman Khalid Jos
-Sheikh Abdulbasir Isah U/Kawo
-Sheikh Bello Yabo Sokoto
-Ustaz Albaniy Samaru Zariya
-Ustaz Ibrahim Idris Darus-Sa'ada
-Ustaz Imam Ibrahim Lawal Osama Abuja
-Ustaz Tajuddeen Ibadan
-Ustaz Abubakar Baban Gwale
-Ustaz Dr. Ibrahim R/Lemo
-Ustaz Dr. Rabi'u R/Lemo
-Ustaz Dr. Abdulmudallib Ahmad
-Alaramma Abubakar Adam Katsina
-Alaramma Ahmad Suleiman Kano
-Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
-Alaramma Isma'il Maiduguri
-Alaramma Bashir Abubakar Gombe
-Alaramma Suleiman Azare
-Alaramma Ilyasu Birnin Gwari
Sanarwan ta fito ne daga Ofishin sakataren kungiya ta kasa Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe
Allah ya bada ikon Zuwa Amin.
Jibwis Nigeria.
14/Safar/1438
14/November/2016

Friday, 7 October 2016

Shari'ar Da Sheik Abubakar Muhamud Gumi Yayi Wacce Ta Fi Ba Shi Mamaki

Shari'ar Da Sheik Abubakar Muhamud Gumi Yayi Wacce Ta Fi Ba Shi Mamaki
A rayuwar Malam an taba tambayar shi wacce shari'a ce wacce ya yi ta fi ba shi mamaki ko ba zai taba mantawa da ita ba.
Sai Malam ya ce, "akwai wata shari'a da na taba yi da tafi bani mamaki wanda ba zan manta da ita ba, a wani gari an yi wani attajiri da ya ke kasuwanci tare da wani mutum amma ba wanda ya san kudin ko na waye a cikinsu.
"Mutane na tsammani ko kudin nasu ne su biyu suka hada hannun jari suke kasuwanci. Ana nan haka, sai wata rana ciwon ajali ya kama wannan attaji, da ya ga ba halin tashi sai ya tara iyalansa da 'yan uwansa da wasu mutane na daban ya ce, idan ya mutu dukiyar da ke hannun Alhaji wane tawa shi ce kadai bai da ko sisi ciki.
"Bayan nan wannan Attajiri sai ya rasu. Sai aka je wa da wannan dan'uwan kasuwancin nasa da wasiyar wannan Attajiri, aka ce Alhaji ya ce idan ya mutu asa dukiyar da ke hannunka a gado domin tashi ce shi kadai. Ko da ya ji haka sai ya tunbatse ya ce, Alhaji karya ya ke, wannan dukiya tashi ce shi kadai bai da ko kobo ciki. Ya ce kawai dai ya ja shi a jiki ne suna kasuwanci tare don ya samu wani abu.
Abu kamar wasa rigima har kotu. Akai ta rafka shari'a har Alhaji mai rai ya ce aje makabarta a tambayi Alhaji mai mutuwa dukiyar waye zai fadi ko ta waye. 'Yan'uwan Alhaji mai mutuwa suka yarda duk da sun san ba'a mutuwa a dawo ballantana na kabari ya yi magana. Nan take aka rankaya da Alkali da lauyoyi da Alhaji mai rai da 'yan'uwan Alhaji mai mutuwa aka nufi makabarta. Da aka je Alkali ya kira sunan Alhaji mai mutuwa. Bisa mamaki sai aka ji muryarsa ya amsa Alkali ya ce, "dukiyar daka mutu ka bari ta waye? Alhaji mai mutuwa ya ce, ta Alhaji wane ne ba tawa ba ce."
Wannan abu ya tsorata Alkali har ya rasa yadda zai yi. Ga dai mamaci ya yi magana, abinda bai ko taba ji a wannan zamani ba.
Daga nan ne suka zo Kaduna wajen Alkali Sheikh Abubakar Muhamud Gumi a garin Kaduna. A lokacinsa ba Alkali irinsa. Nan take aka zo aka fada masa duk yadda abin ya faru tun daga mutuwar Alhaji har maganar da ya yi a kabari. Malam na ji ance mamaci yayi magana sai ya ce, "karya ne wanda ya mutu ba ya magana", ya ce amma mu je inji da kunnena. Ya bisu har can garin aka je makabartan da Alhaji ke kwance aka nunawa Malam kabarin Alhaji, Malam ya kira sunan Alhaji, ya tambayi mamacin "dukiyar da ka mutu ka bari ta waye?" Alhaji ya ce "ba tawa bace, ta Alhaji wane ne (ya fadi sunan Alhaji mai rai). Wannan abu ya daurewa Malam kai, a ce mutum ya mutu yana kabari kwance kuma ya yi magana? Abin da mamaki". Malam ya ce, "kowa ya tafi gida a dawo gobe."
Daren ranar Malam bai rumtsa ba ya kawana nafila da addu'o'i akan wannan lamari.
Washegari aka dawo Makabarta tare da Alhaji mai rai da 'yan uwan Alhaji mai mutuwa da lauyoyi da 'yan sandan kotu, Malam ya ce wa 'yan'uwan Alhaji, "zan sa a tone kabarin Alhaji kun yarda?" Suka ce, "sun yarda". Malam ya sa aka kira masu gadin Makabarta ya umurcesu da su tone kabarin. Nan da nan suka kama aiki. Abin mamaki ana bude kabarin Alhaji sai aka ga layu da guraye da da su karhu da su baru kafi uwa-uba. Malam ya sa aka kwashe. Bayan an kwashe ya sa aka maida gawar Alhaji.
Bayan an rufeta Malam ya matsa kusa da kabarin Alhaji ya kira saunansa har sau uku Alhaji bai amsa ba. Malam ya ce, kudin da ka mutu ka bari na waye? Alhaji shiru ba amsa. Malam ya maimaita tambayar har sau uku shiru ba amsa. Sai ya waiwayo ya nuna Alhaji mai rai ya ce, "ku kama shi matsafi ne dukiyar marayu ya ke so ya cinye."
To wannan shari'a ce tafi ba Malam mamaki da al'ajabi a rayuwar alkalancinsa. Fatanmu Allah Ya kiyaye mu da cin hakkin marayu kuma Ya jikan Malam da rahama ya sa ya huta, kuma Allah Ya jikan sauran al'ummar Musulmi bakidaya.
Madogara:Gumi Initiative Foundation

Wednesday, 7 September 2016

SULTAN ONLY ANNOUNCED EID-EL–KABIR, NOT PUBLIC HOLIDAY, MURIC REPLIES CHRISTIAN ELDERS

The Muslim Rights Concern (MURIC), on Wednesday said that the Sultan of Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar, only announced the day for this year’s Eid-el-Kabir and not public holiday as alleged by Nigeria Christian Elders Forum (NCEF).
The News Agency of Nigeria (NAN) recalls that the Sultan had on September 2, announced that Muslims will observe the Eid-el-Kabir on September 12.
However, a coalition of 22 Christian groups in Nigeria led by NCEF on Tuesday claimed that the Sultan had declared the day as public holiday.
MURIC’s Director, Prof. Ishaq Akintola, in a statement made available to NAN in Ibadan, advised the Christian group to help in promoting unity and religious tolerance in the country.
“For the avoidance of doubts, there is a difference between declaration of Sallah day and declaration of a public holiday.
“Only the Federal Government can declare a public holiday in the country while governors alone can declare it in their states.
“But the Sultan reserves the right to declare the day for a Muslim festival.
“The Sultan based the announcement on Saudi’s declaration of Sunday 11th September as Arafat Day. Normally, the following day should be Sallah day.
“So the Sultan was right, he was even being proactive,’’ MURIC said.
MURIC further explained that the announcement by the Sultan was to guide the government on which days to declare as public holiday for the Sallah, which is part of the national holiday, just like Christmas.
The group said all faith groups must strive to promote peace in the country based on mutual respect and tolerance.
“Let us join hands to rebuild our dear country. Let us come together to fight the ills of society.
“Our criticisms and commendations should be on the basis of an individual’s pedigree and not on his religious leaning.
“Let us celebrate our achievements together and seek corrections for our failings with one voice.

Tuesday, 30 August 2016

YIN QUNUTI CIKIN SALLAR ASUBA HAR KULLUM|Sheikh ibrahim jalo jalingo

Ibrahim Jalo Jalingo
YIN QUNUTI CIKIN SALLAR ASUBA HAR KULLUM:
Babu wani abu daga cikin ingantacciyar sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah da yake nuni a kan kebance sallar Asuba koma bayan sauran salloli biyar da ake da su ta hanyar yin Qunuti a cikinta koma bayan sauran sallolin; babu wani hadithi da ya inganta da irin wannan umurni.
**********
Babban hujjar da wadanda suka kebance sallar asuba da Qunuti ke ambata ita ce hadithi na 678 da Imam muslim ya ruwaito daga Sahabi Baraa Bin A'azib cewa:-
((قنت رسول الله صلى الله عليه وسلم في الفجر والمغرب)).
Ma'ana ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi Qunuti cikin (sallar) Asuba da Magariba)).
Babban abin da zai rusa wannan hanya da su suka dauka ta kafa hujja da wannan hadithi shi ne: kasancewarsu ba su riki yin Qunuti cikin sallar Magariba har kullum ba; ga shi kuwa nassin hadithin ya zo ne a kan sallar Asuba da kuma sallar Magariba gaba daya, a hankalce babu tayadda za a iya rarrabe tsakaninsu cikin hukuncin sai da wani nassi sahihi da zai zo bayan shi wannan hadithin, shi kuwa hakan ba zai samu ba daga gare su.
**************
Gaskiyan al'amari shi ne: Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi Qunuti a sallar Asuba da sauran salloli na wani dan lokaci saboda yin mugunyar addu'a a kan wasu azzaluman kafurai, kamar yadda ya zo cikin hadithi na 1445 da Abu Dawuda ya ruwaito da isnadi mai kyau, daga Abdullahi Bin Abbas ya ce:-
((قنت رسول الله صلى الله عليه وسلم شهرا متتابعا في الظهر والعصر والمغرب والعشاء وصلاة الصبح في دبر كل صلاة اذا قال: “سمع الله لمن حمده“ من الركعة الاخرة يدعو على احياء من بني سليم على رعل وذكوان وعصية ويومن من خلفه)).
Ma'ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi Qunuti wata daya a jere cikin "sallar" Azahar, da La'asar, da Magariba, da Isha'i, da sallar Asuba, a karshen ko wace salla in ya ce: "Sami'allahu Liman hamidahu" daga raka'ar karshe yana mugunyar addu'a a kan wasu unguwanni na kabilar Sulaim, da Ri'il, da Zakwan, da Usayyah, mamun da ke bayansa suna cewa amin)).
Kamar yadda Imam Muslim ya ruwaito cikin hadithi na 677 daga Sahabi Anas Bin Malik ya ce:-
((قنت رسول الله صلى الله عليه وسلم شهرا بعد الركوع في صلاة الصبح يدعو على رعل وذكوان ويقول عصية عصت الله ورسوله)).
Ma'ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi Qunuti na wata guda bayan ruku'i cikin sallar Asuba yana mugunyar addu'a a kan kabilar Ri'il, da Zakwan, yana cewa "kabilar" Usayyah ta saba wa Allah da manzonSa)).
Haka nan Ibnu Majah ya ruwaito hadithi na 1243 da isnadi sahihi daga Anas Bin Malik ya ce:-
((ان رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يقنت في صلاة الصبح يدعو على حي من احياء العرب شهرا ثم ترك)).
Ma'ana: ((Lalle manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya kasance ya yi ta yin Qunuti cikin sallar Asuba yana mugunyar addu'a a kan wata unguwa daga cikin unguwannin Larabawa har na tsawon wata guda sannan ya daina yi)).
***************
Idan wani ya ce: ai karanta Qunuti na dindin cikin sallar Asuba shi ne mazhabar Malikiyyah da Shafi'iyyah, don me za a ce: hakan ba shi ne ya dace da sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah ba?!
Sai a ce da shi:
1. Babu wata Mazhaba cikin Mazhabobin da ake da su da take ma'asumiya wacce za a ce babu kure a cikinta ba, babu irin wannan mazhaba har abada.
2. Babu wata Mazhaba cikin Mazhabobin da ake da su da take da matsayin zamantowa Mizani na Shari'ah, a'a Mizanin Shari'ah har kullum shi ne: ingantattun sunnonin Annabi mai tsira da amincin Allah, ko kuma a ce: Alkur'ani da Hadithi...
3. A mazhabar Malikiyyah daura layar da aka rubuta ta da Ayoyin Alkur'ani, ko aka rubuta ta da wasu maganganu masu kyakkyawar ma'ana abu ne da ke halal. To amma duk da yake wannan shi ne Mazhabar Malikiyyah an samu da yawa daga cikin mutanen da suke danganta kawunansu zuwa ga mazhabar Malikiyyar sun zabi barin mazhabar cikin wannan mas'alar sunkoma sun yi riko da abin da umumin sahihin hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah yake nunawa; watau na haramta daura laya ba tare da tafsili ba.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya taimake mu Ya cusa wa al'ummarmu soyayyar manzon Allah da kuma son yin aiki da ingantattun sunnoninsa cikin zukatansu. Ameen.

Sunday, 28 August 2016

Masu waziri:Hattara kada kilu ta jawo Bau!|Dr.sani umar r/lemo

Masu Wa’azi: Hattara Kada Kilu Ta Jawo Bau!:
“Wani labari mai ban takaici da ya faru na wani mai wa’azi, yayin da wata rana wani ya zo ya fada masa cewa, ‘Mawakiya Muniarah Al-Mahdiyya ta bude wasannin rawa da waka a dandalin Abbasiyyah”. Sai mai wa’azin nan da ya zo wa’azinsa a masallacin juma’a na “Al-Jami’ul Umawi” ya fusata ya rika yana cewa, ‘Yaya za a yi mace ta fito da jikinta waje a gaban maza tana tikar rawa, tana nuna tsiraicinta. Ina masu kishin addini suke da ba su yi komai akai ba?’.
Sai jama’a suka rika cewa, ‘A’uzu billahi! A ina wannan abu ya faru? Kuma da yaushe hakan ta auku?. Sai mai wa’azi ya kada baki a fusace, yana fada musu, ‘Ai a dandalin Abbasiyya ne abun ya faru, kuma dadaddare bayan sallar isha’i’.
Lokacin da abun ya faru, dududu jama’ar da suka halarcin wasan ba su fi rabin dakin taron ba. Amma bayan da wannan mai wa’azi ya gama wa’azinsa, sai ga shi ‘daikin taro’ ya cika makil da ‘yan kallo.
Wannan lamari da ya faru, ya kamata ya zama darasi da izina ga masu kuzuzuta ayyukan ta’asa cikin wa’azinsu, wanda hakan daga karshe yake komawa ya zama talla da kiran-kasuwa ga wannan laifin, cikin rashin sani”. – As-Sheikh Ali At-Tantawi, a cikin littafinsa “Zikrayaat”, juzi’i na 1, shafi na 53.

Saturday, 27 August 2016

Rancen Airtime na Mtn ba Riba ce ba|Dr. Muhd sani umar R|lemo

Dr. Muhd Sani Umar R/lemo

Rancen Airtime Na Mtn Ba Riba Ce Ba:

A Azumin bara (1436H) an mini tambaya game da bashin da kamfanin Mtn yake ba wa masu mu’amala da shi. Ka ranci airtime na misalin N50, a ba ka na N45. A karon farko na bayar da amasar cewa, Haramun ne! Kuma zai shi ga babin ribal Qardh!. Daga baya na janye wannan fatawar saboda yadda na kara fahimtar mas’alar, na ba da fatawar halaccin ta, saboda dalilai kamar haka:
1. Wannan mas’ala ba bashi ne na kudi da kudi ba, ballantana batun ribal Kardh ta zo.
2. Abin da yake hakikanin mas’alar shi ne, wani ne mai amfani ne da wannan kamfani na Mtn ya sayi hidima ta aritime (airtime service) wadda suke sayar da ita N45, sai suka sayar masa ita a N50.
3. Kasancewar an ambaci kudi a cikin ciki ba shi yake tabbatar da cewa kudi da kudi ne aka yi musanyan su ba. An yi musanyan kudi ne da wata hidima (airtime service) wanda masu ita suka ki ba shi ita a farashin da suke sayar da ita kudi hannu, suka kara masa wani abu akai. Wannan ba komai ne ba a shari’ance ba, saboda kayansu ne, suna da damar su yi maka kari kamar yadda suke da damar su yi maka ragi, kuma ka karba.
4. Abin da zai tabbatar maka da cewa, wannan abin da ka nema su ba ka ba tsurar kudi ne ba, hidima ce kawai, wanda aka bas hi ita a wayarsa ba za iya sayen komai da wannan ba a gurin wani ya ce yana da kudin biya a gurinsa, a she ka ga ba kudi ne ba, koda an rubuta alamar kudi a tare da shi.
5. Kamar yadda ya halatta katin waya na N100 a sayar wa da mai bukata akan N110, duk da cewa ga shi a rubuce an rubuta N100. Ko a sayar masa da shi N95, wanda babu wani masani da ya taba cewa, wannan riba ce ko haramun ne, saboda musanyar kudi da kudi ne. Domin alala hakika wannan katin wayar mai dauke da N100 a kansa ba kudi ne ba, wata hidima ce, aka yi mata ramzi da wannan 100, shi ya sanaya da zarar ka kankare ka shigar ita cikin wayarka zaka jefar da wannan katin tare da cewa an rubuta kudi a jiki, To wannn masa’al ta rance kamar haka take, don haka, duk wanda ya harmta wannan to wajibi ya haramta sana’ar sai da kati. Wanda ban a jin akowa mai fadar hakan.
6. Don haka ba magana ce ta an ba ni fatawa a baibai ba, magana ce ta sake nazari akan fatawar farko, wanda wannan abu ne sananne a gurin manyan malamanmu magabata da suke canza fatawoyinsu yayin da wasu dalilai suka bayyana gare su.
7. Wannan matsaya kuma shi ne matsayar wasu daga cikin abokai na daliban ilimi bayan sun kalli mas’alar ta mahanga lilimi da sanin abin da ake kira riba, daga cikinsu akwai abokina Dr. Bashir Aliyu Umar kamar yadda daga baya na samu labari.
8. Daga karshe ina kira ga sauran ‘yan uwana diliban ilimi mu yi kaffa-kaffa wajen sakin baki game da sha’anin halal da haram, al’amarin yana da hadari. sanin madafar shari’a ta wanda ya karanta ta ne. Allah ya sa mu dace. Amin.

Sheaik Dr Muhd Sani Umar Rijiyar Lemo

Thursday, 23 June 2016

IZALA TA YABA DA BADA BELIN SHEIKH DR NAZIFI YUNUS JOS

Izala Ta yaba da bada belin Sheikh Dr. Nazeefi Yunus Jos
Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya nuna farin cikin sa ga bada belin da kotu tayi na Sakin Sheikh Dr. Nazeef Yunus, Shugaban yace wannan kadan ne daga cikin irin addu'oin da 'yan uwa sukayi a lokacin da aka kama shehin Malamin wanda ya shafe kusan shekaru uku a tsare, gashi Allah ya kawo lokacin da zai koma ga iyalansa.
Sheikh Lau ya kara da cewa wannan ya nuna irin adalci da wannan gwamnati ta maigirma shugaban kasar Naijeriya Muhammadu buhari ke da shi wajen maida wa wadanda aka zalunta hakkin su.
Shugaba Bala Lau ya sake kira ga Gwamnatin tarayya da ta sa ke sa ido a gidajen yarin kasar nan, Don rage chunkoso dake chikin gidan, Gwamnati tayi afuwa ga masu zaman jiran Shari'a da ake Ajiye da su fiye da kima.
Shehin Malamin yace Allah (SWT) yanason masu rangwame, saboda haka ma wannan kungiya ta Izala ta kasa, take kai ziyara gidajen yari a fadin kasarnan domin wa'azi, ko a wannan wata ta Ramadan kungiyar ta kai ziyara gidan yari na yola, tayi Wa'azi da gargadi ga 'yan gidan yari, kuma ta bada tallafin kayan Azumi da sabulai maiyawa ga 'yan fursuna. Sannan ta biya taara wa mutane 20 daga cikin yan fursuna, wanda aka fiddasu daga chikin gidan yari a matsayin masu 'yancin komawa ga iyalansu. Wannan duk yana nuna mana muhimmancin lura da yanayin da wadanda suke zaune a gidajen yari suke bukatar a bibiyi lamarin su domin wadanda basu da hakki su koma ga iyalansu suyi rayuwa kamar kowa.
Daga karshe Sheikh Bala Lau ya kara da addu'ar Allah ya kare duk wani musulmi daga shiga irin wannan jarrabawar, yasa mu gama da duniya lafiya.

Saturday, 18 June 2016

DR. NAZIFI JOS YANA CIKIN MAWUYACIN HALI, INJI IYALINSA

Dakta Nazif Jos Yana Cikin Mawuyacin Hali, Inji Iyalinsa
Daga Saleh Aliyu
Iyalan fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan da ke Jos, Dakta Nazeef Muhammad Yunusa da ke tsare a hannun hukumar DSS, sun koka matuka game da mummunan halin rashin lafiya da yake fama da ita.
Mai dakin Shehin Malamin, Hajiya Saudatu Yunusa ce ta yi wannan kukan a lokacin da take zantawa da manema labarai. Ta ce halin da yake cikin abin damuwa ne matuka.
Dakta Nazeef Yunusa, wanda fitacce Malamin Salafiyya ne, an kama shi ne a ranar 29/10/2013 a gidansa da ke Unguwar Rogo a Karamar Hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, bisa zargin da ake masa na shigar da mutane cikin kungiyar Boko Haram. Kamun nasa ya biyo bayan kama wasu dalibansa hudu ne da aka yi a jihar Kogi.
Hajiya Saudat, wacce ke bayani cikin kuka, ta tabbatar da cewa wasu majiyoyi masu tushe daga inda ake tsare da shi, sun tsegunta masu cewa Shehin Malamin yana fama da matsananciyar rashin lafiya.
Ta ce; 'Ko lokacin da aka kama shi ya shaida masu ba shi da lafiya yana bukatar kulawar Likitoci saboda Ulcer da hawan jini da yake fama da su. Ya kamata ya bayyana a gaban kotu ranar Larabar da ta wuce, kuma bai bayyana ba saboda rashin lafiyar da yake fama da ita'.

Saturday, 4 June 2016

Look for Ramadan moon today, Sultan tells Muslims

Sultan of Sokoto Alhaji Muhammad Sa’ad Abubabar (0 Likes) The Sultan of Sokoto and President General of the Nigerian Supreme Council for Islamic Affairs (NSCIA) Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar has called on Muslims across the country to look for the new moon of Ramadan today, June 5. Secretary-General of NSCIA, Prof. Is-haq Oloyede, said in a statement yesterday that the National Moon Sighting Committee (NMSC) of the NSCIA, under the leadership of Mallam Hafiz Wali and Prof. Usman El-Nafaty, and Muhammad Yaseen Qamarud-Deen, advises the Sultan on the commencement of every lunar month and that the Sultan, as advised, always makes monthly declaration of the commencement of every lunar month. “The NMSC had advised the President General that the crescent of Ramadan should be searched for on Sunday, June 5, 2016 equivalent to 29th Sha’ban 1437 AH. If the crescent is actually sighted by informed persons on Sunday night and His Eminence is so advised by the experts, he would declare Monday, June 6, 2016 as the first day of Ramadan. If, however, the crescent is not sighted on the night of Sunday, Tuesday, 7th June, 2016 automatically becomes the first of Ramadan, 1437 AH,” Oloyede said. He enjoined Muslims across the country to be on the lookout, adding that in addition to established and traditional Islamic leaders in each locality, members of the NMSC can be contacted for information and clarification.