Shahararren malamin nan Sheik Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa Darikar Taijjaniyya da Shi'a duk daya ne.
Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a yayin da ya karbi bakoncin tawagar wasu mabiya Shi'a a gidansa dake Kano.
Ya ce da Shi'a da Darikar Tijjaniyya duk tafarkin Annabi (S.A.W) suke bi kuma masoyan iyalansa ne. Ya kara da cewa babu wani bambanci tsakanin akidun biyu.
"Da Shi'a da Darikar Tijjaniyya duk daya ne saboda dukkansu suna bin tafarkin Annabi (S.A.W) ne kuma masoyan iyalansa.
"Duk mulumin kwarai ya zama dole ya yi imani da Annabi (S.A.W) da kuma nunawa iyalansa kauna. Don haka dukkanmu mun iya imani da shi. Don haka daya muke" cewar Shehin Malamin.
Ya kuma yabawa tawagar Shi'an kan ziyarar da suka kawo masa, inda ya bayyana hakan a matsayin wata hanya ta hadin kan musulmai.
Tun a farko, jagoran tawagar mabiya Shi'an, Malam Yakubu Yahaya, ya bayyana cewa makasudin kawowa Shehin Malamin ziyara shine don taya shi murnar kammala tafsirin azumin Ramadan na wannan karo da ya yi.
Sources:Rariya
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment