Kira Ga Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El'rufa'i Da Sauran Gwamnonin Arewa - NewsHausa NewsHausa: Kira Ga Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El'rufa'i Da Sauran Gwamnonin Arewa

Pages

LATEST POSTS

Friday, 9 June 2017

Kira Ga Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El'rufa'i Da Sauran Gwamnonin Arewa

Kira Ga  Gwamna Kaduna Malam Nasiru El'rufa'i Da Sauran Gwamninin Arewa

...su masu fafutukar kafa yankin Biafara ba su da shugabanni masu tsawatar musu ne?
Ali Muhammad Idris (Artwork)

DAGA ALI MUHAMMAD IDRIS (ARTWORK)

Akwai ingantaccen hadisin Manzon Allah (S.A.W) da ya sanar da mu cewa “idan muka ga abin ki mu dakatar da shi da karfin mu, idan ba mu da karfin mu dakatar dashi da bakin mu, idan hakan bai samu ba sai mu kyamaci lamarin a zukatan mu” sai ya kara da cewa “amma wannan shine mafi raunin imani”.

Wasu dabi'u dake yawo a zukatan shugabannin mu na Arewa su suka tunzura ni nake so na isar da sakon dake raina wanda ban yi wa kaina alkawarin zan iya dauke kai suna faruwa ba.  Duk da da dama daga cikin mutanen mu irina idan suka yunkuro za su yi nuni kai tsaye sai a kira su da masu neman tada zaune tsaye, ko neman tada husuma. Kwatankwacin wani al’amari da ya faru a Kaduna. Na wasu matasa da suke kungiyar matasan Arewa suka tunatar da wasu yanki na kabilun kudu (Igbo) cewa lallai sun ba su watanni uku su tattara ya nasu ya nasu su koma garinsu. 

Al’amarin ya mallakawa gwamnan Kaduna Mal. Nasiru elrufa’i karfi da ikon sawa a kama su (a tunaninsa sun yi wani gagarumin laifin da suka cancanci haka.

Abunda nake so gwamnatin mu ta arewa da ta Kaduna su duba shine wace fuska maganar matasan ta nufa? Menene manufa da ma’anar maganar? Wane tasiri ne na maganar da ya zama cewa tada hankali ne?


Gwamnan Kaduna Nasiru El'rufa'i
Anya gwamnan Kaduna ya san irin cin gashin dankalin da kabilar Igbo ke yi wa dan arewa a kudanci kuwa? Anya ya san wulakantawa da kashewar da ake wa mutanen mu na arewa mazauna can kuwa?

Kodai Nijeriya ba kasar dan arewa bace? Bashi da ‘yanci da ikon zama a ko’ina? 
Me ya sa shugabannin su na kudu ba su taba kama wasu nasu da suke cutar da ‘yan arewa ba? Me ya sa shugabannin mu basu mike sun kare martabar yan arewa dan hana su daukar mataki a hannu kamar yadda suke gani a yanzu sunyi ba?

A tsammanina idan da gwamantin arewa sun san cewa ana irin fiye da haka a kudu za su fahimci inda kira da manufar wadannan matasa yake. Basa ganin kamar tunatarwa ce dan nemawa dan arewa ‘yanci a can kudu yasa su wannan maganar? Basa ganin wani abu ne da su ya kamata su yi dan mutunta wadanda suke tare dasu da kuma daraja ‘yan arewa dan a samu balance na zama lafiya a ko’ina ba? 

Anya basu san hakan da suka yi na hukunta bangare daya illolin da za su haifar ba?
Sun tabbatarwa da ‘yan kudu su ci gaba da wulakanta ‘yan arewa kenan?
Sun tabbatarwa da ‘yan kudu ‘yan arewa ba ko’ina bace wurin zamansu kenan?
Tunda su sun kasa tsawatarwa da nuna abunda ya  kamata suyi. 

Akwai wani abu da nake so gwamnati da duk wani dan arewa su fahimta shine mufa ‘yan arewa ne kuma shuwagabannin mu na arewa mun zabe su ne dan kare martabar arewa, dan samarwa da dan arewa mutumci, dan kuma tsayawa a yiwa dan arewa adalci a duk abinda ya faru. Idan dakikin dan arewa yana maganar cewa ai gwamnatin ba ta dan arewa kadai bace to mu zauna mu zabi ‘yan kudun mana?
senator Dr Rabi'u musa Kwankwaso

Mun zabe kune dan muna so ku yi koyi da tsohon gwamnan kano Sanats Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi kadai ne ya iya tashi takanas ta kano ya isa garin ILE IFE ya tsawatar irin tsawatarwar da bata saba doka ba, kuma ta dago daraja da mutuncin yan arewa.  

Lallai irin albishirin da ya yi cewa idan aka ci gaba da yiwa yan arewa wulakanci suma aka kaisu bango suka yunkuro suna tsammanin kasar zata zauna lafiya ne? to babbar masalaha idan irin wannan al’amarin ya faru shine a yi hukunci na gaskiya, a duba kowanne bangare a basu rashin gaskiyar su da gaskiyarsu. Amma daga  cikin wasu lalatattu marasa kishin arewa sai suka ce ya shigo da siyasa, ni a nawa ganin wannan shine hakkin daya rataya a gun shugaba dan arewa.  Kamar yadda suma idan wani abu da ya faru suke tsayawa su ga sun kwato musu yanci. Kamar wani abu daya faru a kano akan wata mata yar kudu datayi batanci… matasa suka kashe ta. sai da wasu shuwagabannin su na kudu suka tsaya saida aka biya diyyar wannan matar. Me dan arewa zaka kira wannan abun idan ba kishi ba?

Yanzu an kama matasan arewa su kuma can ba a tsawatar musu ba me hakan yake nufi? Yana nufin an basu kofar ci gaba da wulakanta yan arewa, mu kuma an rufe mana baki mun kasa Magana?

Idan an hana mu magana, to wane shugaba zai iya tsayawa a kudun ya tsawatar musu, ya dago darajar matasan mu?

Wannan mulkin yana so yayi kama da mulkin mallaka… dan adam bashi da ‘yancin yin Magana ne idan an cutar dashi, musamman dan arewa?

Shirun da muke yi ta dalilin tsoron kada a kama mu ko a hukunta mu shine yasa ‘yan kudu suka raina yan arewa, saboda shugabannin sun riga sun jefa tsoro a zukatan yan arewa. Muna son zaman lafiya amma bamu yarda shugabannin mu su kasa tsayawa su zama bango da kafafun mu ba. 
Yanzu rainin har ya kai fariyar a raba kasa a wurin yan kudu.

Abunda yake sa ‘yan kudu surutu da karfin halin cewa a raba kasa saboda sune suke da man fetur, shin sun manta ne.. arewa fa ba kasar talauci bace, mune muke da duk wani arziki idan ka dauke man fetur da najeriya ta jingina dashi. Ko sun manta mulkin duk da aka yi a najeriya basu kai yan arewa yi ba? Ko sun manta gyada da auduga sun daga darajar najeriya suka kaita inda har ake iya gane najeriya a sahun kasashe?
Daga karshe ina kira ga gwamnati da talakawan arewa, wallahi mu farka mu tuna cewa najeriya kasar muce. Kuma idan tura ta kai bango al’amarin bazai yi kyau ba.

Sannan ina tunatarwa cewa mu ba masu nufin tada zaune tsaye bane. Ba na yi rubutun nan dan tunzurawa ko haifar da wani abu ba face tunatarwa kamar yadda Allah (SWA) Yace “ku tunatar, domin lallai tunatarwa tana amfanar da mumini” 

Za mu ci gaba da yin biyayya ga shugabanni in har sun tsaya mana suka daraja darajar mu. 
Daga: ALI MUHAMMAD IDRIS  (ARTWORK)

©Facebook/Rariya

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment