Daga Jamilu Sani Rarah Sokoto
Wadannan sune Shugabannin da suka Jagoranci Yakin Kafa Yankin Biafara yakin da Ujukku ya jagoranta a shekarar 1967.
Wadanda Sune wadanda ke gefen Nijeriya;
1. Yakubu Gowon (Shugaba).
2. Murtala Ramata Muhammed
3. Benjamin Adekunle
4. Olusegun Obasanjo
5. Mohammed Shuwa
6. E.A. Etuk
7. Shehu Musa Yar'Adua
8. Theophilus Danjuma
9. Ibrahim Haruna
10. Ipoola Alani Akinrinade
11. Ted Hamman †
12. Muhammadu Buhari
13. Ibrahim Babangida ( WIA )
14. Isaac Adaka Boro †
15. Idris Garba
Wadannan Sune a gefen Biafara;
1. Odumegwu Ojukwu (Shugaba)
2. Philip Effiong
3. Alexander Madiebo
4. Albert Okonkwo
5. Victor Banjo
6. Ogbugo Kalu
7. Joseph Achuzie
8. Azum Asoya
9. Mike Inveso
10. Timothy Onwuatuegwu †
11. Rolf Steiner
12. Festus Akagha
13. Lynn Garrison
14. Taffy Williams
15. Jonathan Uchendu
16. Ogbo Oji ( WIA)
17. Humphrey Chukwuka
18. H.M. Njoku
Duk da a lokacin Shugabannin 'yan tawaye sun fi shugabannin da suka tsaya tsayin daka ga Nijeriya yawa amma hakan bai hana wa masu rajin kafa Biafara sha da kyar ba.
Abinda ya kai ga sai da Ojukwu ya tsere da kafafunsa duk da ya samu taimako daga wasu kasashe. Inda a kalla mutane dubu 500,000 zuwa miliyan 2 'yan Yankin Biafran suka mutu sanadiyar tsananin yunwa da rashin abinci. (Tunda dama cen daga Arewa ake kai musu abinci).
A ranar 15 ga watan Janairun 1970 a barikin sojoji da ke Lagos da ake kira (Dodan Barrack) Philip Effiong ya bayyana janyewar su daga yakin tare da bada hakuri akan abinda ya faru yake cewa"
"I, Major-General Phillip Efiong, Officer Administering the Government of the Republic of Biafra, now wish to make the following declaration: That we affirm that we are loyal Nigerian citizens and accept the authority of the Federal Military Government of Nigeria. That we accept the existing administrative and political
structure of the Federation of Nigeria. That any future constitutional arrangement will be worked out by representatives of the people of Nigeria. That the Republic of Biafra hereby ceases to exist."
Ma'ana, "Ni Manjo Janaral Phillip Efiong Shugaban tafiyar da Gwamnatin Biafara ina shelanta cewa, cikin aminci mun yarda mun bi mun amince mu 'yan Nijeriya ne. Mun amince da duk dokokin Siyasar Nijeriya, dadadden kundin dokikin da dama cen mun yarda da shi yanzu ma mun sake yarda da shi a matsayin dokar Nijeriya daga yanzu an daina maganar wani yanki na Biafara."
Al'amarin Ojukwu dan tawaye kuwa, bayan da aka yi galaba kansa a Shekarar 1970, sai Ojukwu ya tsere daga kasar Nijeriya ya yi shekaru 13 ya na gudun hijira.
Ya dawo Nijeriya bayan da aka masa afuwa a Shekarat 1982, daga bisani kuma ya shiga takarar shugaban kasa har sau biyu amma bai samu nasara ba.
Wani abin ban dariya duk fitinar Ojukwu akan kafa yankin Biafara amma da ya mutu tun daga Ingila aka rufo gawarsa da tutar Nijeriya. Sannan bincike ya nuna hawan jini ne ya kashe shi.
Don haka duk mai tunanin kafa yankin Biafara ina kyautata zaton shi ma hawan jini ne zai kashe shi.
®www.hausaloaded.com
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment