Wasanni: Ronaldo ya fi kowa karbar kudi a wasanni a duniya - NewsHausa NewsHausa: Wasanni: Ronaldo ya fi kowa karbar kudi a wasanni a duniya

Pages

LATEST POSTS

Thursday 8 June 2017

Wasanni: Ronaldo ya fi kowa karbar kudi a wasanni a duniya

- Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya ci gaba da zama a matsayi na daya a wanda ya fi karbar albashi a tsakankanin masu wasanni a duniya in ji mujallar Forbes.

- A bara Ronaldo ya karbi fam miliyan 72.05 kudin albashi da ladan wasanni da tallace-tallace da ya yi, amma a bana ya samu karin fam miliyan 3.87.

Cikin jadawalin da Forbes ta fitar 'yan wasa 11 ne daga wasanni daban-daban suke kan gaba a wajen samun kudi.

Masu wasan kwallon kwando su 32 ne suke cikin 100 farko, sai masu buga kwallon baseball 22 da 'yan wasan zari-ruga na Amurka 15 da masu taka-leda tara.

NAIJ.com ta samo jerin 'yan wasa 10 da suka fi samun kudin a duniya:

1.Cristiano Ronaldo - kwallon kafa ($93m/£72.05m)


Wasanni: 
2.LeBron James - kwallon basketball ($86.2m/£66.79m)

3.Lionel Messi - kwallon kafa ($80m/£61.98m)

4.Roger Federer - kwallon tennis ($64m/£49.58m)


5.Kevin Durant - kwallon kwando ($60.6m/£46.95m)

6.Andrew Luck - zari-ruga ($50m/£38.74m)

7.Rory McIlroy - kwallon golf ($50m/£38.74m)

8.Stephen Curry - kwallon kwando ($47.3m/£36.64m)

9.James Harden - kwallon kwando ($46.6m/£36.10m)

10.Lewis Hamilton - tseren motoci a($46m/£35.64m)

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment