Da gaske ne Sergio Ramos ya ɗaga tutar Nigeria? - NewsHausa NewsHausa: Da gaske ne Sergio Ramos ya ɗaga tutar Nigeria?

Pages

LATEST POSTS

Wednesday, 7 June 2017

Da gaske ne Sergio Ramos ya ɗaga tutar Nigeria?


A ranar Asabar ne kulob ɗin ƙwallon ƙafa na Real Madrid ya lashe kofin Gasar Zakarun Turai bayan doke Juventus da ci 4-1 - karo na biyu a jere da kulob ɗin ya lashe kofin.
Sai dai yayin da 'yan wasa da magoya bayan Real Madrid suke murna da farin ciki da samun wannan nasarar, an ga kaftin ɗin Madrid, Sergio Ramos, ɗaure da wata tuta mai launi iri ɗaya da ta Najeriya a jikinsa.

Hakan ya jefa jama'a da dama cikin mamaki musamman ma'abota shafukan sada zumunta a Najeriya, kan ko ɗan wasan yana da wata dangantaka da Najeriya ne.
Akwai kuma wasu da suke tunanin ko shi ɗan asalin Najeriya ne da dai sauransu. Hakazalika, wasu suna cewa ya yi hakan ne don ya martaba magoya bayan Madrid da ke Najeriya.

Binciken da BBC ta yi ya gano cewa Sergio Ramos ɗan asalin kasar Spain ne, kuma ba shi da wata dangantaka da Najeriya.
Har ila yau, tutar da aka ga ɗan wasan da ita bayan sun lashe kofin Zakarun Turai tutar wani yanki ne mai ƙwarya-ƙwaryar 'yanci a ƙasar Spain wato Andalusia, amma ba tutar Najeriya ba ce.

Wato tutar yankin da aka haifi ɗan wasan ne.
Tutar Andalusia tana yin kama sosai da ta Najeriya, inda duka tutocin suke da launin kore da fari da kuma kore.
Bambancin kawai ta fuskoki biyu ne:

An jera launin kore da fari da kuma kore daga kwance ne. Ta Najeriya kuma launukan a tsaye aka jera su.

Tutar Najeriya ta bambanta da wadda Ramos ya ɗaura ta fuskar ita ta Andalusia tana da hoton kan sarki a tsakiyarta, yayin da ta Najeriya ba ta da hoton komai a tsakiya.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment