Matasan Musulmi Da Ke Wurin Horaswar Soja,Suna Iya Ajiye Azumi Daga Baya Su Rama-inji MallamBashir Ahmad Sani Sokoto - NewsHausa NewsHausa: Matasan Musulmi Da Ke Wurin Horaswar Soja,Suna Iya Ajiye Azumi Daga Baya Su Rama-inji MallamBashir Ahmad Sani Sokoto

Pages

LATEST POSTS

Friday, 9 June 2017

Matasan Musulmi Da Ke Wurin Horaswar Soja,Suna Iya Ajiye Azumi Daga Baya Su Rama-inji MallamBashir Ahmad Sani Sokoto

MATASAN MUSULMI DA KE WURIN HORASWAR SOJI, SUNA IYA AJIYE AZUMI DAGA BAYA SU RAMA, IDAN HAR DON ALLAH SUKE YI, CEWAR MALAM BASHIR AHMAD SANI SOKOTO

DAGA Mukhtar A. Haliru

MALAM BASHIR AHMAD SANI DAKE GABATAR DA TAFSIRIN SA A MASALLACIN ALIYU BN ABI DALIB DA KE UNGUWAR KOKO CIKIN GARIN SOKOTO, A WAJEN TAFSIRIN DA YAKE GABATARWA, YA AMSA WATA TAMBAYA DA NEMAN SANIN HUKUNCIN MATASA DA KE WURIN DAUKAR HORASWAR SOJI, INDA MALAMIN YA YI CIKIAKKEN BAYANI KAMAR HAKA;

"AKAN (TRAINING) HORASWAR  NA SOJOJI, WASU MALAMMAI NA KIRA GA GWAMNATOCI CEWA DAN ALLAH A DAGE SAI BAYAN AZUMI",

 YA CE A NASA GANIN "BAMA SAI AN YI HAKAN BA INDAI DAN ALLAH MUTUM ZAI YI, TO YA SHA AZUMIN YA JE YA YI TRAINING DIN BAYAN SALLAH SAI YA JE YA RAMKA, KUN GA INDAI AN YI HAKAN DA NIYAR SHARRI ANA GANIN AN YI HAKA NE DA NIYAR MUSULMI SU KASA, TO IN SUN GA MUSULMI SUN AJIYE AZUMI BAYAN SALLAH SUN RAMKA, WATA SHEKARA BA SAI AN ROKE SU AN CE DAN ALLAH BA, SU DA KAN SU BA ZA SU YI BA,".

 MALAMIN YA KARA DA CEWA "ADDININ MUSULUNCI ADDINI NE MAI SAUKI MATAFIYI AI AN SAUWAKE MAI AN CE YA AJIYE AZUMI, TO INA GA MAI IRIN WANNAN AIKIN, JIHADI NE AMMA GA WANDA YA YI SABODA ALLAH"

©Rariya

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment