Hukumar Zakka Da Wakafi Ta Jihar SOKOTO, Ta Biyawa Wasu Fursunoni 31, Bashi Na Naira Miliyan Biyu - NewsHausa NewsHausa: Hukumar Zakka Da Wakafi Ta Jihar SOKOTO, Ta Biyawa Wasu Fursunoni 31, Bashi Na Naira Miliyan Biyu

Pages

LATEST POSTS

Sunday, 11 June 2017

Hukumar Zakka Da Wakafi Ta Jihar SOKOTO, Ta Biyawa Wasu Fursunoni 31, Bashi Na Naira Miliyan Biyu

Hukumar  Zakka  Da Wakafi Ta Jihar SOKOTO, Ta Biyawa  Wasu Fursunoni 31, Bashi Na Naira Miliyan Biyu

Daga Mukhtar A. Haliru

A jiya Assabar 15, Ramadan 1438 wanda ya yi daidai da 10-6-2017 Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi ta jihar Sokoto Malam Muhammad Lawal maidoki ya jagoranci wasu mambobin Hukumar zuwa gidan yarin jihar Sokoto, inda Shugaban ya samu kyawawan tarbo daga ma'aikatan wannan gidan yari.

A jawabin da Shugaban ya ce sun je gidan kason ne domin biyawa wasu fursunoni kananin basussukan da ake biyan su, kuma suka kasa biya domin su fita.

Malam Maidoki yace dalilin wannan wani Bawan Allah ne ya bada Wakafi(Sadaka) kudi Naira miliyan daya ga wannan Hukumar, kuma yace kar a bayyana sunan shi a nan Sokoto. Yana son a yi mai Wakafin  a gidan kaso. A kan haka suka garzaya gidan kason, domin nemo  masu kananan  basussuka kusan mutum 31, amma kudin su sun kai Naira Miliyan biyu, sai suka tunfaye da naira miliyan daya cikin kudaden da Gwamnan  jihar Sokoto Rt.Hon Aminu Waziri Tambuwal (Matawallen Sokoto) ke tallafawa Hukumar a duk wata, suka cika kudin dan ceto rayukkan wadannan bayin Allah, wanda mafiyawan su matasa ne.

A wani bangaren jawabin sa, Malam Lawal Maidoki ya yi kira ga ga 'yan gidan kason  wadanda aka fidda da wadanda ke ciki, cewa ba duk wanda ya sami kan shi a gidan kaso ne mai aikata laifi ba, wani tsausayi ne, wani ko Allah kadai ne ya san hakikanin laifin da ya aikata har aka garkame shi. Ya yi kira a gare su da su zama jakadu na gari, domin amfanar da al'ummar su, su kuma nemi ilimi na addini da zamani, su kasance masu tsafta da hakuri a lokacin zaman na su.

Daya daga cikin fursunonin kuma limamin su, ya nuna jin dadin su kan wannan ziyarar, kana ya gabatar da nasiha mai ratsa jiki, gami  da kira ga hukumomi, NGOs, kungiyoyin da masu hannu da shuni da su yi wa Allah su garzaya gidan kaso dan ganin yanayin da suke ciki, da tallafa masu domin su fito, kasancewar wasun su abinda aka yi masu tara bai kai ya kawo ba.

A karshe Shugaban Hukumar ya bayyana cewa za su baiwa kowane mutun daya cikin fursunonin da aka fidda naira dubu goma dan yin na mota, sutura da abinci. Kuma ya ce za su duba koken da suka yi domin ganin abin da suke iyawa. 

Shugaban Hukumar Zakka ya mika wadannan kudaden na naira dubu goma goma ga hannun wadanda aka fidda din.
Wasu da aka zanta da su, sun yi alkawarin zama jakadu na gari.

©Rariya
Ga Hotuna kamar Haka:



®www.hausaloaded.com


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment