Sarauniyar kyau ta karbi musulunci - NewsHausa NewsHausa: Sarauniyar kyau ta karbi musulunci

Pages

entclassblog-bg
entclass-fire LATEST POSTS entclass-fire

Monday, 5 June 2017

clonebar

Sarauniyar kyau ta karbi musulunci


IMG_20170605_174713_901


- Wata Sarauniyar kyau yar kasar Czech Republic data samu haske ta Musulunta

- Budurwar mai suna Marketa Korinkova ta koma Maryam

Wata kamfanin jaridar kasar Birtaniya ta ruwaito labarin wata Sarauniyar kyau yar kasar Czech Republic data samu haske ta Musulunta, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Budurwar mai suna Marketa Korinkova wadda a baya Kirista ce ta gane hasken Musulunci ne yayin da take karatu a jami’ar Charles dake Prague shekaru 3 da suka gabata.

A yanzu haka Marketa ta koma zama a kasar Dubai da zama, kuma ta sauya sunanta zuwa Maryam, inda tace ta gamsu da zaman kasar Dubai, don ta kara samun daman fahimtar addini.

vllkyt7gl4fu1kude.d6a12d1a
Musulma


Maryam tace abinda tafi kauna a kasar Dubai shine kwanciyar hankali da saukin rayuwa, ba wai wani kyale kyalen gidaje ba.

Maryam tace bata ganin ana cin zarafin Musulmai mata a Musulunci, inda tace sama da shekaru 1400 da suka gabata musulunci ya tanadar da hakkin mata, tare da kuma rashin bautar dasu, sa’annan Musulunci ya baiwa mata damar shigar harkar mulki..

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment