Duk Ranar Dana Zama Shugaban Najeriya, Sai Na Tsagata Gida Biyu Uban Kowa Ya Kama Gabansa!!! - Inji Dr Rabiu Musa Kwankwaso - NewsHausa NewsHausa: Duk Ranar Dana Zama Shugaban Najeriya, Sai Na Tsagata Gida Biyu Uban Kowa Ya Kama Gabansa!!! - Inji Dr Rabiu Musa Kwankwaso

Pages

LATEST POSTS

Monday 12 June 2017

Duk Ranar Dana Zama Shugaban Najeriya, Sai Na Tsagata Gida Biyu Uban Kowa Ya Kama Gabansa!!! - Inji Dr Rabiu Musa Kwankwaso

Duk Ranar Dana Zama Shugaban Najeriya, Sai Na Tsagata Gida Biyu Uban Kowa Ya Kama Gabansa.


HAUSA PRESS24__
Mai girma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fusata dangane da irin ce-ce-ku-can, dake yawo a kasar nan da kuma irin muzgunawar da ake yiwa Arewatawa a yankin Kudu, inda yace.


Rainin hankalin da yan kabilar Igbo, ke yiwa yan'uwanmu a Kudancin kasar nan ya-yi yawa, ana kama yan Arewa, ana kullewa ba tare da sun-yi laifin komai ba, ana kashe su a kone kayansu, ana muzguna musu saboda tsabar rainin hankali Igbo, har cewa  suka yi.


Duk dan Arewan dake zaune a Kudu, sai ya-yi ID-Card, wai kuma da sunan kasa daya Al'umma daya, to wannan wulakanci ya isa hakanan.


Dama muna yin kawaici ne muna kauda ido, daga dukkanin abubuwan dake faruwa, saboda muna da gwamnoni kuma abokanmu wadanda muke jin kunyarsu, a yankin amma ba don haka ba da tuni sun gane kurensu.


Saboda haka ina gargadin yan kabilar Igbo, da-su zauna lafiya da mu yan uwansu yan Arewa, idan kuma ba haka ba to zamu ci gaba da tuntubar jagororin yankin domin su magance wadannan matsaloli.


Idan kuma abin ya-ci tura to Rabiu Kwankwaso, ba na yan Arewa, ko yan Kudu, bane, Rabiu Kwankwaso, na kowa da kowa ne, amma ba-zan zuba ido ina kallon wanan rainin hankali daga Igbo, ba saboda haka zan fitar musu da yankinsu, suje suci gaba da hawan Kwale-Kwalensu, matukar na zama shugaban Najeriya.


Saboda sanin kansu ne cewa muna da arziki kala-kala a wannan yanki namu na Arewa, ciki harda man fetur din da suke takama da shi, kawai rashin shugaba mai kishi ne ya hana mu tono namu,__inji Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kamar yadda ya shaidawa manema labarai. 

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment