Wasu Mutane Da Ba'a San Ko Su Waye Ba Sun Kone Wani Mutum A Garin Kura Dake Jihar Kano - NewsHausa NewsHausa: Wasu Mutane Da Ba'a San Ko Su Waye Ba Sun Kone Wani Mutum A Garin Kura Dake Jihar Kano

Pages

LATEST POSTS

Saturday 10 June 2017

Wasu Mutane Da Ba'a San Ko Su Waye Ba Sun Kone Wani Mutum A Garin Kura Dake Jihar Kano

Wasu Mutane Da Ba'a San Ko Su Waye Ba Sun Kone Wani Mutum A Garin Kura Dake Jihar Kano

A ranar Larabar da ta gabata ne da tsakar dare wasu da ba'asan ko su wane ba suka je karamar hukumar Kura dake jihar Kano da wannan bawan Allah a cikin mota a daure, daidai titin zuwa kauyen Bugau bayan Nitel suka tsaya suka fito dashi suka kone shi kurmus sukayi tafiyarsu.

Fulanin dake kusa da wajen sun shaida hakan, domin sune suka ankarar da abin dake faruwa, kafin ayi yunkurin daukar mataki har sun kone shi sun gudu.

Wayewar gari jami'an tsoro sunje sun tafi da gawar zuwa babban sashin bincike na hukumar 'Yan Sanda ta jiha. Sai dai ana kyauta zaton mutanen daga cikin birnin Kano suka fito da mutumin.

Allah ya tsaremu, ya tsare mana imaninmu.

Daga Shafin Hausa Daily

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment