Farawa da iyawa! Jaruma Rahma Sadau ta lashe kyauta a masana’antar fina-finan kudu - NewsHausa NewsHausa: Farawa da iyawa! Jaruma Rahma Sadau ta lashe kyauta a masana’antar fina-finan kudu

Pages

LATEST POSTS

Sunday 24 September 2017

Farawa da iyawa! Jaruma Rahma Sadau ta lashe kyauta a masana’antar fina-finan kudu


Farawa da iyawa fitacciyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa na masana’antar Kannywood da a kwanan baya aka dakatar da ita da kuma ta shilla zuwa masana’antar fina-finan kudancin kasar nan na Nollywood tuni har ta fara lashe kyauta.

Mun samu dai cewa jarumar yanzu haka an lissafa ta a matsayin jarumar da ta lashe kyautar nan ta BON a rukunin yan wasa sabbin jini tare da wani jarumin kuma Namiji mai suna Gbenro.

Arewafresh.com.ng dai ta samu cewa jarumar ta sanar wa da duniya wannan nasarar da ta samu ne a shafin ta na Instagram inda ta bayyana cewa tana yiwa dukkan magoya baya da kuma masoyanta jinjinar ban girma.


  1. A wani labarin kuma fitacciyar jarumar nan ta wasan Hausa a masana’antar Kannywood mai suna Hadiza Gabon ta fara fitowa a cikin fina-finan turanci na kudancin kasar nan watau Nollywood.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment