Dalilai guda 10 da suka sa ALI NUHU Yayi fice kuma ya zama abin koyi a masana'antar kannywood - NewsHausa NewsHausa: Dalilai guda 10 da suka sa ALI NUHU Yayi fice kuma ya zama abin koyi a masana'antar kannywood

Pages

LATEST POSTS

Saturday 30 September 2017

Dalilai guda 10 da suka sa ALI NUHU Yayi fice kuma ya zama abin koyi a masana'antar kannywood

Hakika masana’antar kannywood ta samu babban abun
al’fahari kasancewa tare da wannan jarumin a masana’antar.

Ga wasu dalilai 10 da muke ganin cewa sune abubuwan da
yasa yan arewa ke farin ciki gannin wannan tauraron wanda
aka wa lakabi na “sarkin kannywood” a talabijin;

1. Ya dade yana harkar fina-finai

Tun shekara 1999 Ali nuhu ya fara fitowa cikin fina-finai kuma
babban shirin da ya fitar dashi idon jama’a shine “sangaya”.

2. Banda Kannywood jarumin jakada ne a masana’antar Nollywood

Wannan jarumin ya nuna mana cewa banda haushen hausa ya
kware wajen yin fina-finai cikin harshen turanci.Ya fito a cikin
shirin nollywood da dama.

3. Ya amshi lambar yabo da dama

Wannan jarumin ya amshi lambobin yabo bila adadi cikin gida
har da ƙasashen waje.

4. Shi na kowa ne

Indai ta yadda abokan hamayen shi na masana’antar zasu
samu karuwa wannan jarumin yana gaba gaba wajen tabbatar
da haka kuma sauran jaruman na alfahari kasancewa tare
dashi.

5. Yana da ƙwarjini har ƙasashen waje da masana’antu daban daban

Hakika idan muka shiga wasu kasashe zamu ji cewa sunan Ali
Nuhu yana yaduwa sanadiyar rawan da yake takawa a wajen
yin fim.

6. A harkar fim ya nuna cewa na “Uba da ɗa” ne

Shima dai dan sa Ahmad Ali Nuhu ya fara fitowa a fina-finai
hausa tun yana dan yaro bayan ya bayyana ma uban shi cewa
shima a gaskiya yana sha’awar yin fim, ganin cewa faduwa ta
zo dai dai da zama uban ya mara masa baya amma da
sharadi na dole sai ya dage wajen koyan ilimi kuma zai dinga
yin haka idan ya samu hutu daga makaranta.

7. Da ka ganshi ka gan tambarin Arewa

Shi dai wannan jarumin baya boye ma jama’a a duk inda ya
sinci kanshi cewa shi ban dan arewa bane kuma kullum yana
neman yadda zai yada al’adar yan arewa ga sauran jama’a.

8. Suma masoyan shi suna farin ciki

idan suka ci karo dashi
Ganin cewa ya shahara a fannin shirya fina-finai jarumin baya
kyamar tarbar masoyan shi a duk inda ya gamu dasu.

9. Yana son ƙwallon kafa kuma yana tare da tawagar Nijeriya
dari bisa dari

Duk wani wassan kwallo da ya danganci Nijeriya tauraron
Kannywood yana gaba gaba wajen goyon bayan tawagar kuma
aboki ne ga yan wassan super eagles.

10. Ko zamu iya cewa mutu ka raba?

A yanzu dai wannan jarumin yana da shekaru 43 a duniya kuma ya kwashi shekara 19 yana nishatarda mu. Har yanzu
jarumin yana nuna cewa kamar yanzu ya fara wannan sana’ar
shirya fina-finai kuma ba alamun gazawa tare dashi.
Daga nan mu dai muna jinjina ma wannan ƙwararren jarumin
da ayyukan da yake yi wajen fadakarwa, nishatarwa tare da
ilmantar da mutanen Arewa.

1) Wow Ku Kalli Sabbin Zafafan Hotunan RAHAMA SADAU Na Wannan Satin (Hot photos)  
2) HADIZA GABON TA ZAMA MAWAKIYA Ku kalli videon wakar datayi 
3) RAHAMA SADAU TA BAYYANA DALILIN TA NA YIMA CLASSIQ KISS A WAKAR SA 
4) Subahanalillah Ku Kalli videon yadda Aka Kama wani mutumi shi da uwar matar sa 
5) Video: KU KALLI VIDEON YADDA WATA AMARYA TA KASHE KANTA RANAR DAURIN AUREN T


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment