Barnabas buba Luka wanda aka fi sani da “Classiq” jarumi ne a fannin wakar hip-hop.
Ga masu tambaya ko wannan shahararen mawaki dan arewa ne, ku sha kurumin ko domin wannan jarumin dan arewa ne mai asali.
Shidai wannan mawakin ya ficce a wakokin hausa hip-hop kuma ya shahara sosai a ƙasar domin yadda yake sako baitutukar shi cikin harshen hausa.
“Sarki” kamar yadda masoyan shi ke kiran shi yana alfahari da yaren hausa kuma a duk inda ya tsinci kanshi yana tallafa yaren tare da al’adar yan arewa.
Kasancewa yau take ranar haihuwar shi ne ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da shi ;
1. Dan jihar bauchi
Wannan mawakin da aka haifa ranar 21 ga watan Satumba na 1991 haifaffen dan jihar Bauchi ne kuma shine da na karshi cikin yara 3 da iyayen sa suka haifa.
2. Baban shi malami ne
Kwarrai ko kana iya kiran shi da “dan mallam” domin shima na alfahari da haka kasancewa babban shi malami ne a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake nan jihar Bauchi. Baban shi likita ne na boko a fannin ilimin “geography” ita kuma uwar sa malama ce a asibiti.
3. Yayi karatun sa a Arewa
Shidai wannan jarumin waka ya fara karatun sa na firimari garin Bauchi kuma ya kammala karatun digiri dinsa a jami’ar Ado Bayero dake
Kano inda yaa karanta ilimin kwamfuta.
4. Ya yayi wasa a garuruwa da dama kuma jakadan arewa ne
Classiq ko kuma “arewa Mafia” kamar yadda yake ma kansa lakabi yayi wasa a wurare da dama kuma ya yi waka tare shahararrun mawakan
Nijeriya .
5. Duk wakar shi akwai dangantaka da Arewa.
Ko cikin baitutukar shi ko sunnan wakar ko kuma yanayin shigar shi a bidiyo zai ka ji ko ka gan abun da ya ganganci arewa. Duk da cewa wannan mawakin yana iya basaja ya koma wakokin turanci amma ya amince da ya dabbaka yaren ga idon duniya.
yayi wakoki irin su Zauna, Sama, hoto, barka da sallah, Ana haka da dai sauransu.
Daga nan sashen hausa na pulse muna ma wannan jarumin mawaki mai hazaka murna da zagayowar ranar haihuwar shi.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment