Daga Ibrahim Baba Suleiman
Daraktan hukumar inganta fasahar bayanai ta kasa (NITDA) Dakta Isa Ali Pantami yace Kafin Nijeriya ta samu sauyin zamani, sai an inganta fasahar bayanan kasar.
Daraktan ya bayyana haka ne a taron 'Microsoft Nigeria Digital Government' wanda ya gudana yau a babban hotel na Hilton dake Abuja.
Dakta Pantami a bayanan shi yace babban muradin hukumarsa ta NITDA shine inganta fasahar bayanai a Nijeriya, inda yace tun da ya shiga ofis, hukumar ta fitar da tsari mai dauke da manyan tsaruka guda bakwai na sauya Nijeriya zuwa kasa ta zamani.
A saboda haka, Daraktan ya nemi dukkan ma'aikatu da hukumomin gwamnati da su bu tsarin umurnin gwamnatin tarayya mai lamba SGF/6/S.19/T/65 na 18 ga watan Afrilu 2006, wanda ya wajabtawa ma'aikatun neman izini daga hukumar NITDA kafin yin kowani irin aiki na fasahar bayanai, inda yace kin yin hakan laifi ne karkashin sashin doka na 17 kuma akwai hukunci kamar yanda aka zayyana a sashi na 18 na dokar.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment