Wasu ma'aurata sun gano cewar su 'yan uwan juna ne bayan shekaru 24 da aurensu Abdul Rahim da Aisha 'yan asalin kasar Pakistan,sun gano cewar ashe su din yaya da kanwa nevbayan da suka shafe shekaru 24 a matsayin mata da miji.
Tun asali dai Abdul Rahim da Aisha, an raba su da juna ne, bayan wani mummunan hadari da yayi sanadiyar rasuwar mahaifansu, inda, daga bisani ne, wasu iyalai mabambanta suka dau macen da namijin don kula da su, kafin daga bisani su auri juna ba tare da sun san cewar su din 'yan uwa bane.
Ya dauke su, tsawon shekaru 24 kafin su gane cewar su 'yan uwan juna ne. "Mun zata cewar aurenmu aure ne kamar kowanne aure, kawai dai muna zargin kamar muna da danganta wadda ba ta uwa daya uba daya ba" a cewar Abdul Rahim.
"Abin mamakin ashe mutane da yawa a garinmu sun san cewar ni da matata yaya da kanwa ne, amma aka kasa samun wani wanda zai yi karfin halin shaida mana" A cewar Aisha yayin da take bayani tana zubar da hawaye.
Sai dai wasu masana, sunce irin wannan aure, ba sabon abu bane a kasar Pakistan. Juliane Edwards, ta shaidawa majiyar SMACK cewar, " na sha cin karo da balahirar aure irin wannan a kasar Pakistan, inda dan uwa yake auren 'yar uwarsa da suka fito ciki daya"
Ta kara da cewar "akwai wani lokaci da wani mutum ya tursasawa dansa ya auri kanwarsa, a cewarsa, ita 'yar tasa mummuna ce ba zata iya samun miji ba, dan haka ne ya yanke shawarar wan yarinyar ya aureta, sabida shi yayan malalaci ne" inji Juliane.
Ko a shekarar da ta gabata, wata kotun Shariar ta hana wata mata neman saki daga mijinta wanda dan uwanta ne da suka fito ciki daya. Kotun na mai cewar dan sun fito ciki daya baya tabbatar da hukuncin haramcin aurensu a dokar kasar.
Allah daya gari bamban. Meye ra'ayinku kan wannan kwamacala a kasar Pakistan?
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment