Babu Bambamci Tsakanin Fina Finzan Kannywood Da Nollywood - Inji Hadiza Gabon - NewsHausa NewsHausa: Babu Bambamci Tsakanin Fina Finzan Kannywood Da Nollywood - Inji Hadiza Gabon

Pages

LATEST POSTS

Saturday 30 September 2017

Babu Bambamci Tsakanin Fina Finzan Kannywood Da Nollywood - Inji Hadiza Gabon

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta soma fitowa a fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.


Jarumar ta shaida wa kafar bbc hausa cewa ta fara gwada sa’arta a fina-finan Nollywood ne domin ta nuna basirar da take da ita ta yin fina-finai a ɓangarori daban-daban.

A cewarta, “Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a gajerun fina-finan turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood.

Fitaccen Jarumi kuma Furodusa a Fina-finan Nollywood Mike Ezuruonye da Jaruma Hadiza Gabon Ayayin Aikin fim ɗin Lagos Real Fake Life.
“Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna ‘Lagos real fake life’.

“Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin ‘yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan fim”.

Hadiza Gabon ta ƙara da cewa “Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim ɗinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saɓa da addini da al’adata ba”.

Jarumar ta ce babu wani “bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finan Kannywood da na Nollywood idan ban da bamabancin harshe. Don haka na ji daɗin soma fitowa a fina-finan Nollywood”

1) Wow Ku Kalli Sabbin Zafafan Hotunan RAHAMA SADAU Na Wannan Satin (Hot photos)  
2) HADIZA GABON TA ZAMA MAWAKIYA Ku kalli videon wakar datayi 
3) RAHAMA SADAU TA BAYYANA DALILIN TA NA YIMA CLASSIQ KISS A WAKAR SA 
4) Subahanalillah Ku Kalli videon yadda Aka Kama wani mutumi shi da uwar matar sa 
5) Video: KU KALLI VIDEON YADDA WATA AMARYA TA KASHE KANTA RANAR DAURIN AUREN T


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment