Mutumin da ya kirkiro mujallar 'batsa' ta Playboy Hugh Hefner, ya mutu - NewsHausa NewsHausa: Mutumin da ya kirkiro mujallar 'batsa' ta Playboy Hugh Hefner, ya mutu

Pages

LATEST POSTS

Thursday 28 September 2017

Mutumin da ya kirkiro mujallar 'batsa' ta Playboy Hugh Hefner, ya mutu





Hugh Hefner,

dan Amurkar nan da ya kirkiro mujallar da ke nuna mata tsirara ta kasa da kasa Playboy, ya mutu yana da shekara 91.
Kamfanin Playboy Enterprises Inc
ya ce Mista Hefner ya mutu ne a gidansa da ke Los Angeles.
Hefner ya fara buga mujallar Playboy ne a wajen da yake dafa abinci a shekarar 1953.

Mujallar ta zamo mujallar da ta fi ko wacce kasuwa a duniya inda take sayar da kwafi miliyan bakwai a ko wanne wata a lokacin da mujallar ta fi yin kasuwa.

Cooper Hefner, dansa, ya ce: "mutane da yawa za su" yi kewarsa.

Cooper ya yaba da rayuwarsa babansa "ta musamman mai gagarumin tagomashi," inda yake ganin mahaifin nasa a matsayin wani mai fasaha a fannin ala'ada da kafafen watsa labarai.

Ya kuma bayyana babansa a matsayin mai fafatukar 'yancin tofa albarkacin baki da 'yancin jama'a da kuma 'yancin jima'i.

Mujallar Hefner da ta kafa tarihi ta sa ana kallon nuna tsiraici ba komai ba ne a kafofin yada labarai, duk da cewar mujallar ta fara fitowa ne a lokacin da jihohin Amurka ka iya hana anfani da magungunan hana daukar ciki.

Mujalallar ta kuma mayar da shi miloniya, lamarin da ya haifar da wata daular kasuwanci da ta kunshi gidajen caca da gidajen rawa.

Mujallar ta farko tana dauke ne da hotunan Marilyn Monroe tsirara,
wadanda asali an daukesu ne domin bugawa a wata kalandar shekarar 1949, amman shi Hefner ya sayi hotunan kan kudi $200.

Attajirin wanda aka san shi da yawan son saka kayan barci, ya shahara da dabi'arsa ta fifita sha'awa da nema tare da auren 'yan matan da ke fitowa a mujallarsa tare da gudanar da bukin fitsara a kawataccen gidan Playboy da ke Los Angeles.

A shekarun 1980, gogayya daga wasu mujallun da suka fi Playboy nuna tsiraici ta sa kasuwar mujallar ta ragu, kuma Hefner da kansa ya yi fama da mutuwar wani sashe na jikinsa a shekarar 1985.

'Yara, Christie ta karbi jagorancin kamfanin bayan shekara hudu, kuma Hefner ya koma katafaren gininsa tare da wasu mata.

A shekarar 2014 ne Cooper Hefner ya taka gagarumar rawa a kamfanin bayan Christie ta yi murabus a shekarar 2009.

Mujalar ta yanke shawarar nuna tsiraici a watan Maris din shekarar 2016, amman ya sake shawara a farkon wannas shekara ta 2017.

Wani makwabcin Hefner ya sayi katafaren gidan Playboy kan kudi dala miliyan 100 a watan Augustan shekarar da ta gabata, amman ya amince da cewar Hefner ka iya ci gaba da zama a ciki har sai ya mutu.

Takaitaccen tarihinsa

An haifi Hefner ne a shekarar 1926 a birnin Chicago, kuma ya yi aikin sojin Amurka a tsakiyar shekarun 1940.
Ya kammala karatun digiri a fannin nazarin halayyar dan adam, kuma ya yi aiki a matsayin marubuci a mujallar maza da ake ce wa Esquire, kafin ya ranci kudi $8,000 domin ya fara wallafa Playboy a shekarar 1953.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment