Yanzu Na Daina Rigima Da Kowa Inji Shahararren Jarumin Nan - Adam A. Zango - NewsHausa NewsHausa: Yanzu Na Daina Rigima Da Kowa Inji Shahararren Jarumin Nan - Adam A. Zango

Pages

LATEST POSTS

Monday, 24 July 2017

Yanzu Na Daina Rigima Da Kowa Inji Shahararren Jarumin Nan - Adam A. Zango


ADAM A. Zango jarumi ne wanda ya ke kan sahun gaba na 'yan fim. Hasali ma dai in ka debe Ali Nuhu babu dan wasa kamar sa. Wasu ma sun dauka ya kere Alin a fagen jarumtaka. Kai, za ma a iya cewa in dai harkar fim ce, to Zango ya yi wa Ali tazara saboda a yayin da ya ke yin duk abin da Ali ke yi, shi Ali akwai abin da Zango ke yi wanda ba ya yi: waka. A fagen wakar ma, Zango ya na cikin sahun gaba. Ya yi fayafaye (album) masu tarin yawa, na kallo da na ji.
To amma duk da nasarorin da ya samu, Adamu ya na daga cikin 'yan fim da ake wa wani kallo. Da bakin sa ya taba fada wa jaridar Leadership Hausa cewa kashi 90 cikin dari na 'yan fim ba su son shi. Shin me ya sa? Haka kuma ya taba yin sabani da mujallar Fim har abin ya kai gaban 'yan sanda, aka rabu dutse a hannun riga. Amma yanzu an shirya, sai jajantawa!
A shekerar da ta gabata ne, Adam A. Zango ya lashe gasar Jarumin Jarumai na wanda mujallar Tozali ta ke shiryawa a duk bayan shekara biyu. Jamila Umar Nagudu ta lashe gasar zama Jarumar Jarumai a bikin, wanda aka yi a katafaren wajen taro na International Conference Centre, a Abuja ran Asabar, 8 ga Oktoba, 2016.
Bayan taron, mujallar Fim ta tattauna da Zango inda ya bayyana farin cikin sa. Haka kuma ya yi tsokaci kan rantsuwar kaffara da ya yi kan masu cewa akwai 'yan luwadi da 'yan madigo a industiri, da batun film billage, abubuwan da ya koya a tafiye-tafiyen da ya yi a wasu kasashe, da batun batawar sa da kafar yada labarai ta Mujallar Fim da sauran su. Adam Zango ya bayyana cewa yanzu bai rigima da kowa saboda halin rayuwar mutane da ya karanta.
© Rumbunkannywood

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment