Rashin Adalci ne A Dawo Da Rahama Sadau A Kannywood inji Nafisa Abdullahi - NewsHausa NewsHausa: Rashin Adalci ne A Dawo Da Rahama Sadau A Kannywood inji Nafisa Abdullahi

Pages

LATEST POSTS

Sunday 2 July 2017

Rashin Adalci ne A Dawo Da Rahama Sadau A Kannywood inji Nafisa Abdullahi

HAUSATOP.com dai ta samu labarin cewa Sani Danja yana daga sahun gaba na masu nuna goyon bayan dawo da jaruma Rahma Sadau. Domin acewarsa masana’antar kannywood ta sami koma baya tun bayan da aka kori Rahma Sadau.

Domin Rahma jarumace mai tarin masoya a Arewaci da kudancin kasar nan. Wasu mutane sun daina kallon hausa fim sabida sun rasa Rahma Sadau. Kuma ba abin burgewa bane ace uba ya kori yarsa daga masana’anta.
Duk da yake Rahma tayi laifi kuma ta amsa tayi laifi, ya kamata a yafe mata. Domin mu ma muna yiwa Allah laifi kuma ya yafe mana. Inji Sani Danja.

Amma daga bangaren mata Nafisa Abdullahi ta jefa kuri’ar kada adawo da Rahma Sadau. Acewarta Sabida idan aka dawo da ita an nuna son kai. Domin ashekarun baya an kori jarumai irinsu, Kubura Dako, Safiya Musa, Maryam Hiyana, Ummi Nuhu da sauransu, amma har yanzu ba’a dawo da su ba. Har wasu suka yi aure. Inji Nafisa Abdullahi.

To ana nan ana saka kuri’a Rahma Sadau ta dawo ko kada adawo da ita

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment