A Dajin Sambisa Ya Dace A Gina Kurkuku Na Barayin Gwamnati - Magu - NewsHausa NewsHausa: A Dajin Sambisa Ya Dace A Gina Kurkuku Na Barayin Gwamnati - Magu

Pages

LATEST POSTS

Saturday 8 July 2017

A Dajin Sambisa Ya Dace A Gina Kurkuku Na Barayin Gwamnati - Magu



Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa a Dajin Sambisa ya kamata a gina gidan kurkukun da za a rika garkame duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa.

Ya ce bin wannan mataki ya zama dole don nesanta barayin gwamnati daga cikin mutane yana mai cewa a halin yanzu akwai wasu manyan mutane da ke kokarin gurgunta ayyukan EFCC a kokarin da take yi na yaki da rashawa inda ya kuma kara jaddada muhimmancin hadin kan bangaren shari'a kan samun nasarar wannan yunkurin.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment