Daga Habu Dan Sarki
Wani matashin yaro mai kimanin shekaru 19 mai suna Eric Labari, wanda dake karamar hukumar Mangu a Jihar Filato ya shiga hannun jami'an tsaro a Jos, bayan da wani yaro da aka kama da bindiga kirar gida ya fallasa harkar da suke yi.
Bayan da jami'an tsaro na sojojin rundunar hadin gwiwa ta Operation Safe Haven suka kafa wani matashin yaro mai suna Benshak Nandong dauke wata bindiga da aka yi ta da fasahar gida, sun tuhume shi don sanin wanda ya kera masa da kuma yadda ta isa hannun su. Shi kuma ya bayyana musu yadda wannan matashi Eric yake samsana'o'da bindigogin da suke amfani da su wajen aikata laifuka.
Bayan gano lungun da Eric Labari yake sarrafa masana'antar kera bindigogi a garin Mangu, jami'an rundunar ta Operation Safe Haven sun kai shi Jos, inda suka bincike shi, don sanin inda ya koyi wannan sana'ar.
Abin da suka gano daga Eric shi ne an kore shi a makarantar da yake karatu, wato makarantar koyar da sana'o'i ta garin Bukur, inda ake koyar da kere-kere da sarrafa karafa, saboda ya gagara biyan kudin makaranta.
Wannan dalili ne, a cewar sa wata dama da ta sa ya shiga amfani da basirar da Allah ya yi masa, don ya samu ya tara kudin da zai koma makaranta.
Babban kwamandan rundunar hadin gwiwa ta OPSH Manjo Janar Rogers Nicholas ya yi takaicin halin da wannan yaro ya samu kansa a ciki, wanda ya ce Allah ne kadai ya san yawan mutanen da suka yi amfani da makaman da yake kerawa.
Har kawo hada wannan rahoton, Eric Labari yana tare da jami'an tsaro ana gudanar da bincike kafin a mika shi ga jami'an 'yan sanda, wadanda za su tura shi kotu gaban kuliya manta sabo.
©Zuma Times Hausa
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment