Na Yi Mamakin Irin Tarbar Da Jonathan Ya Samu Yayin Zuwansa Kano Yin Ta'aziyyar Danmasanin Kano - NewsHausa NewsHausa: Na Yi Mamakin Irin Tarbar Da Jonathan Ya Samu Yayin Zuwansa Kano Yin Ta'aziyyar Danmasanin Kano

Pages

LATEST POSTS

Sunday 9 July 2017

Na Yi Mamakin Irin Tarbar Da Jonathan Ya Samu Yayin Zuwansa Kano Yin Ta'aziyyar Danmasanin Kano

Na Yi Mamakin Irin Tarbar Da Jonathan Ya Samu Yayin Zuwansa Kano Yin Ta'aziyyar Danmasanin Kano

Daga Rabi'u Biyora

Shi hoton na farko yana nuna irin kalar tarbar da tsohon shugaban kasa Ebele Jonothan ya ssmu lokacin daya kawo ziyararsa ta karshe a shekarar 2015 kafin zabe a jihar kano, Tsohon shugaban ya samu tarba ne daga dandazon jamaian tsaro tun daga filin jirgi har zuwa guraren da zai ziyarta a Kano, saboda tsabar bakin jinin da yake dashi a wajen al'umnar arewa musammam kanawa a time din.

Lamarin ya kai matsayin da hatta wanda aka ga yana nuna kaunarsa ga ebele, al,umma suma dsukar wannan mutumin a matsayin bara gurbi wands baya kishin jamaarsa, a wasu guraren har duka akeyiwa wanda ya nuna alamar yana kaunar Ebele Jonathon ko jam'iyyar PDP.

Sauran hotunan kuma na dauke da bayani ne akan ziyarar da tsohon shugaban kasa Goodluck ebele yayi a wannan satin a jihar Kano, inda ya zo don yin ta'aziyya ga iyalan Dan Masanin Kano da kuma al'ummar Kano, kamar yadda rahoto ya bayyana tsohon shugaban ya samu tarba ta musammam tun daga saukar sa a filin jirgi har zuwa cikin birnin Kano, inda dandazon al'umma suka taru suna yi masa lale da zuwa jihar Kano.

Bayan da na kalli bidiyon ziyarar ta Tsohon shugaban, sai kwakwalwata ta shiga tunani akan shin menene dalilin faruwar hakan a wannan lokacin, tayaya Tsohon shugaban ya samu irin wannan tarbar a wajen wasu Kanawan kuma anya hakan kuwa bashi da alaka ds rashin iya gudanar da mu'amula irin ta wasu masu rike da mukaman na wannan lokacin kuwa.

Ni dai na tabbata Kanawa da yawa suna tare da shugaba Muhammadu Buhari kuma sun kasance cikin yi masa addu'ar fatan alheri a kowanne lokaci.

Tabbas da dukkan alamu dandazon mutanen da Ebele ya samu a wannan lokacin, ba zai rasa nasaba da halin ko in kula na wasu 'yan siyasar da suka samu dama a jam'iyyar APC ba, maimakon su mayar da hankali wajen samar da ayyukan alheri ga mutane tare da temakawa shugaba Buhari wajen rage masa nauyin dake kansa, amma hakan ya gagara sai kawai suka mayar da hankali wajen tara abun duniya da kuma gujewa al'ummar da suka bayar da lokacinsu wajen dora su akan mulkin.

ZAHIRIN GASKIYA NA YI MAMAKIN GANIN BIDIYON A SHAFIN TSOHON SHUGABAN KASA EBELE.




Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment