A karo na biyu: Amina Amal ta sake saka wannan hoton kuma mutane sun sake yin Allah wadai - NewsHausa NewsHausa: A karo na biyu: Amina Amal ta sake saka wannan hoton kuma mutane sun sake yin Allah wadai

Pages

LATEST POSTS

Sunday 5 August 2018

A karo na biyu: Amina Amal ta sake saka wannan hoton kuma mutane sun sake yin Allah wadai

A karo na biyu: Amina Amal ta sake saka wannan hoton kuma mutane sun sake yin Allah wadai
A kwanakin bayane, cikin watan Azumin Ramadana, jarumar fina-finan Hausa,

Amina Amal ta taba saka wannan hoton nata a dandalinta na sada zumunta da muhawara, hoton ya jawo cece-kuce sosai inda da dama, ciki hadda wasu daga cikin masana'antar fim din hausa ta Kannywood suka yi Allah wadai dashi.

A wancan lokaci, Amina ta kare kanta inda tace tana kan wani aikine da aka bata.
A karo na biyu, jarumar ta sake saka wannan hoto a dandalinta na sada zumunta inda ta bayyana cewa tuna bayane.

Wannan karin ma mutane basu kyale ba, da dama sunyi Allah wadai dashi.

Ga wasu daga cikin ra'ayoyin mutane akan wannan hoton kamar haka:






Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment