Labari me taba zuciya na matashin da aka haifa babu kafa - NewsHausa NewsHausa: Labari me taba zuciya na matashin da aka haifa babu kafa

Pages

LATEST POSTS

Monday 20 August 2018

Labari me taba zuciya na matashin da aka haifa babu kafa

Allah me yin yadda yaso, wani sai yayishi da cikakkiyar halitta da lafiya, wani kuma yayishi da kudi amma ya kwace lafiyar, wani kuma yana cikin rayuwar za'a canjamai fasali, wannan bawan Allahn me suna Zion Clark dan kasar Amurkane da aka haifeshi babu kafa saidai kuma wannan be hanashi yin hobbasa dan cimma burin rayuwarshi ba.

Bayan kasancewar Zion bashi da kafa, kuma ya tasone a gidan riko, yanzu dai yana makarantar sakan direne kuma yana yin wasan kokawa wanda dama shine burinshi.

Labarin Zion ya taba zukatan mutane da dama domin kuwa duk da kalubalen da ya fuskanta a rayuwarshi be yadda ya zama nauyi akan mutane ba, ya tashi tsaye dan ganin ya zama abin alfahari ga jama'arshi.






Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment