An kera kumbo na farko Wanda zai iya shiga cikin Duniyar Rana - NewsHausa NewsHausa: An kera kumbo na farko Wanda zai iya shiga cikin Duniyar Rana

Pages

LATEST POSTS

Saturday 11 August 2018

An kera kumbo na farko Wanda zai iya shiga cikin Duniyar Rana

An kera kumbo na farko Wanda zai iya shiga cikin Duniyar Rana

Cibiyar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA, ta kaddamar da kumbonta da aka kera kan dala biliyan daya da rabi, da zai zama na farko da ya kai ga duniyar Rana.

Kumbon wanda NASA za ta harba shi zuwa zuwa sama daga jihar Florida a yau Asabar, zai gudanar da bincike ne kan wasu sirrika na tsakiyar rana, da ake kira da 'Corona', wanda masana sukai ittifakin, zafinsa ya ninka na wajen rana sau 300.

Kumbon wanda aka sanyawa suna The Parker Solar Probe zai kuma taimaka masana sararin samaniya da ke duniya, wajen hasashen lokacin da kakkarfar guguwar da ke tsananin gudu a zagayen rana ka iya ketowa doron duniyaduniya .

Kumbon dai gina shi da kaurin inchi hudu da rabi, da ke karfin bashi kariya daga karfin zafin rana mafi tsanani da ake ji a doron duniya da ya ninka sau 500, wato kwankwacin zafin digiri 1, 371 a ma’aunin Celcsius.

Ana sa ran da zarar kumbon ya kusanci Rana, gudunsa zai karu zuwa saurin tafiyar kilomita dubu 700, 000 cikin awa guda, abin da zai bashi damar zama abin da dan adam ya kera mafi sauri a tarihi.
RFIhausa.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment