Rushe masallacin China ya jawo takaddama tsakanin Musulmai da gwamnati - NewsHausa NewsHausa: Rushe masallacin China ya jawo takaddama tsakanin Musulmai da gwamnati

Pages

LATEST POSTS

Saturday, 11 August 2018

Rushe masallacin China ya jawo takaddama tsakanin Musulmai da gwamnati

Rushe masallacin China ya jawo takaddama tsakanin Musulmai da gwamnati

Daruruwan musulmi a yammacin China na takaddama da hukumomi domin hana rusa masallacinsu.

Jami'ai sun ce masallacin da a ka gama gininsa kwanan nan ba shi da takardun izinin gini a Ningxia.

Sai dai musulman sun ki amincewa, inda daya daga cikin mazauna garin ya ce ba za su "yarda gwamnati ta taba masallacin ba."
China na da musulmi miliyan 23, kuma musulunci ya karbu a yankin Ningxia tsawon karni da dama da suka wuce.

Amma masu fafutikar kare hakki sun ce akwai karuwar nuna kiyayya ga Musulmi a China daga hukumomi.

An gina masallacin ne a wani salo na gabas ta tsakiya, inda ya ke da hasumiyoyi da kubbobi masu tsayi da dama.

Ya a ka fara boren?

Ranar 3 ga watan Agusta, jami'ai su ka buga wata sanarwa da ke cewa za a rushe masallacin da karfi da yaji saboda ba a bayar da izinin tsarawa da gina shi yadda ya kamata ba.

An rarraba sanarwar a shafukan intanet tsakanin 'yan kabilar Hui, kamar yadda kamfanin dillancin labarai ta Reuters ta ruwaito.

Mutane da yawa sun bukaci sanin dalilin da ya sa hukumomi ba su hana gina masallacin ba, wanda a ka gama shekaru biyu da su ka wuce, in dai har ba a bayar da takardun izinin gina shi ba, kamar yadda wata jaridar kasar Hong-Kong ta ruwaito.

Rahotanni sun nuna cewa an yi zanga-zanga a wajen masallacin ranar Alhamis kuma a ka ci gaba a ranar Juma'a. Hotunan da su ka bazu a shafukan sada zumuntan China sun nuna taron mutane mai dimbin yawa a wajen masallacin.

Har yanzu dai ba a tabbatar ba idan za a fara rushe masallacin ranar Juma'a kamar yadda a ka tsara, ko kuma idan an cimma matsaya.

Kafar watsa labaran kasar China ba ta ce komai ba har yanzu.
BBChausa.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment