July 2017 - NewsHausa NewsHausa: July 2017

Pages

LATEST POSTS

Monday 31 July 2017

Hira Mai Ratsa Zuciya Daga Majalisar Annabi (SAW)

Wata rana Manzon Allah (SAW) yana zaune tare da Sahabbansa, sai ya fara tambayar su daya bayan daya, sai ya fara da Sayyidina Abubakar 'yantaccen wuta

 Yace: "Yaa Abubakar! Me kake so a duniya?

 Sai Sayyidina Abubakar yace: abinda na fi so a duniya_
 1: zama a gaban ka, 
 2: kallon ka, 
 3: ciyar da dukiya ta gare ka

Sannan Manzon Allah ya koma wajen Sayyidna Umar dan Khaddabi mai abin mamaki

Manzon Allah (Saw) yace: yaa Umar! Me ka fi so a duniya?

 Sai Sayyidna Umar yace : abinda na fi so_
 1: a mini umurni da kyakkyawan aiki ko da a boye ne, 
 2: a mini hani da mummunan aiki ko da a bayyane ne, 
 3: da kuma fadin gaskiya ko da tana da daci. 

_Sannan manzon Allah ya koma wajen Uthman dan Affan, yace masa: "yaa Uthman! Me kafi so a duniya?_

 _Sai Uthman dan Affan yace: abinda na fi so a duniya_
 1: ciyar da abinci ga mabukaci,
 2: yada sallama, 
 3: yin sallah cikin dare a lokacin mutane suna bacci. 

  _Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma ta wajen Aliyyu dan Abi Daalib, yace masa: "yaa Aliyyu! Me ka fi so a duniya?_

  _Sai Sayyidna Aliyyu yace: abinda na fi so a duniya_
 1: Azumi a lokacin rani, 
 2: Karrama bako, 
 3: yakar abokan gaba da takobbi. 

 _Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma wajen Abaa zarril Gifaari, ya ce masa: "yaa Abaa Zarri? Me ka fi so a duniya?_

  _Sai Abaa Zarri yace: abinda na fi so a duniya_
 1: yunwa,
 2: jinya, 
 3: mutuwa. 

  _Sai manzon Allah (Saw) yace: "sabida me yasa kake son su?_

Sai Aba zarri yace: 
 *ina son yunwa ne don zuciya ta tayi laushi,
 *ina son jinya ne don zunubi na yayi sauqi, 
 *ina son mutuwa ne sabida saduwa da ubangiji na

 _A wannan lokacinne Mala'ika Jibrili ya sauqo zuwa majalisar Manzon Allah (domin hirar ta su ta birge shi ), sai yace: ni kuma ina son abubuwa uku a duniyar ku_
 1: isar da sako,
 2: bayar da amana, 
 3: son nakasassu. 

 _Daga fadin haka kuma sai ya tashi zuwa sama Sannan ya sauko a karo na daban sannan yace Allah madaukakin sarki yana karanta muku sallama Hirar manzon Allah da sahabbai tayi dadi, harma Allah yana gaishe su sannan Allah yace yana son abubuwa uku a duniyar ku_
 1: harshe mai ambatonSa, 
 2: zuciya mai tsoronSa, 
 3: jikin da aka jarrabce shi da balaa'i kuma yayi hakuri#.

_Tsarki da godiya sun tabbata ga Allah Girma da tsarki sun tabbata Allah_

Adu'o'i guda uku kada ku manta su acikin sujjadarku..

 "Ya Allah ina rokonka kyawawan halaye".
"Allah ka azurta ni da tuba zuwa gareka tabbatace"

"Ya ALLAH mamallakin zuciyata ka tabbatar da ita akan addininka"

Lalle wannan ya cancanta ku tura zuwa ga waninku domin ya amfana.

Dauki darasin ka a cikin wannan hadisi, ka aikata shi, za ka yi nasara. 

Majalisar Manzon Allah makarantar mai imani ne, yi kokari ka fita a sahun farko na daliban makarantar.

Jikanyar Sarkin Musulmi Muhammadu Tambari Ta Yi Zarra A Karatun Digir-Digir Akan Injiniyanci Na Jami'ar Leeds Dake Ingila!













Dr Zainab Adiya ta Kammala digirin digirgir na sanin makamar Injiniyanci na Sinadarai a daya daga cikin manyan Jami'oi duniya masu girma ta Leeds dake garin Landan a Ingila. 

Dr Zainab Adiya ta kasance daga cikin mata yan Najeriya wadda kuma jikanyar Sarkin Musulmi Muhammadu Tambari. 
Dr Zainab Ibrahim Sarkin Gobir Adiya ta zama cikin jerin dalibai wadanan jami'ar Leeds dake Ingila ta girmamma saboda kwazo da binciken ta,  tana cikin wadanda suka samu karbar shaidar kammala digir digir na zama Dakta a fannin Ilmin injiniyancin sinadarai.

Dr Zainab Adiya ta kasance cikin yan Afrika kalilan da suka yi fice a wannan karni a fannin binciken nazarin Sinadarai, samar da iskan masana'antu da hada wasu Sinadarai na hasken rana tare da iska a jami'ar Leeds. 

Ta rubuta kasidodi na bincike har guda biyu da aka buga a wasu mujjalun duniya masu girma da kima akan lamarin sinadarai dabam dabam da ake kira iskan 'Hydrogen Energy'.

Haka ma yanzu haka tana akan wallafa wasu kasidu akan bincike da tayi na wasu fannoni biyu na inganta samar da sinadarai na oxygen a jami'ar Leeds dake Ingila. 

Dr Zainab Adiya wadda take jikanyar Sarkin Musulmi Muhammadu Tambari ce daga jinin Sarkin Gobir Adiya, tana da kujerar din din a kwamitin mussaman na zabe Kungiyar Dalibai yan Najeriya dake kasar Ingila baya ga kasancewa wakiliyar yankin Afrika a sha'anin inganta karatu da bincike na jami'ar Leeds. 

Haka ma Dr Zainab Adiya tana da kujera Cibiyar Inganta Sinadarai ta Amurka (AICHE) da takwararta ta Ingila mai kula da samar da bincike inganta Sinadarai da makamashi ta Ingila (ICHEME)  DA cibiyar nazarin sinadarai masu amfani ga hasken rana da bunkasa iskan masana'antu ta Ingila mai suna (UKCCS).

Mahaifinta Alhaji Ibrahim Sarkin Gobir Adiya wanda jinin Sarkin Gobir Adiya daga zuri'ar Sarkin Musulmi Tambari ne tare da sauran yan uwa da abokan arziki suka shaidi bikin karbar kyaututtuka da saukar karatun na Dr Zainab Ibrahim Adiya a garin Landan dake Ingila a makon da ya gabata.

New Revisited MTN Data Plans, Prices and Activation Code


If you've noticed; MTN NG has revisited their data plans list, made changes and increased the volume of some sets of data bundles. Now, you can get 50MB for N100 instead of 30MB (before), and 150MB for N200 instead of 100MB (before).

 These plans are all valid for 1 day.
In addition, you can now get 150MB for N300 which is valid for 7 days. I will quickly list out MTN's new data plans, prices, validity as well as the activation code. Kindly follow me along.

MTN just started the data revisiting with the daily plan, hopefully, they will soon review and increase the volume of the monthly part of their data bundle. This is what i just hope for


Lastest MTN Data Plans, Prices and Activation Code

Daily Plans
50MB
N100
24 Hrs
Text 104 to 131

150MB
N200
24 Hrs
Text 113 to 131

Weekly Plans
150MB
N300
7 Days
Text 102 to 131


Other MTN Data Plans Awaiting for Review :

Data Plan Price Validity Code
1GB + 500MB (*bonus data) Monthly Plan
N1,000 30 days

Text 106 to 131
2.5GB + 1GB (*bonus data) Monthly Plan
N2,000 30 days

Text 110 to 131
5GB Montlhy Plan N3,500 30days

 Text 107 to 131
10GB Monthly Plan N5,000 30 days


Text 116 to 131
22GB Monthly Plan N10,000 30 days

Text 117 to 131
50GB Bi-Monthly plan N20,000 60 days


Text 118 to 131
85GB Quarterly Plan N50,000 90 days


Text 133 to 131
500MB + 250MB (*bonus data) Weekly Plan


ku kasance da ®www.hausaloaded.com a ko da yaushe.

Always stay with ®www.hausaloaded.com 

Sunday 30 July 2017

Baya Ga Sana'ar Man Fetur, Ba Sana'ar Da Ta Kai Fim Samun Kudi, Cewar Adam A. Zango

Baya Ga Sana'ar Man Fetur, Ba Sana'ar Da Ta Kai Fim Samun Kudi, Cewar Adam A. Zango

Daga Aminu Dankaduna Amanawa

Fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan Adam A Zango ya bayyana cewa, baya ga sana'ar man fetur, ba sana'ar da ta kai sana'ar fim samun kudi.

Adam A Zango ya bayyana haka ne, a zantawarsa da Gidan Rediyon BBC.

Jarumin ya kara da cewa fim din Gwaska na daga cikin fina-finan da ya samu kudade a dukkanin fina-finnan da ya aiwatar, Kana ya bayyana wakar "Gumbar Dutse" a matsayin wakar dake zama bakadamiyar sa daga cikin wakokinsa.

facebook/Rariya

Saturday 29 July 2017

Hotunan manyan masallatai 10 ma fi kyau a duniya !-bbchausa

Masallacin wani wuri ne na bauta ga mabiya addinin Islama, inda al'ummar Musulmi ke taruwa su yi sallah cikin jam'i.
Akwai gine-ginen masallatai masu kayatarwa a duniya wadanda wata kila ba ku taba sanin da su ba, don haka muka kawo muku wasu daga cikinsu.
1. Masallacin Haramin Makkah da ke Saudiyya

Masallacin Al Haram Mosque - Makkah, Saudi ArabiaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMasallacin Al Haram a yanzu ya mamaye kimanin murabba'in mita 400,800, wanda ke daukar mutane miliyan hudu a ciki da wajensa lokacin Hajji.

Al-Qur'ani ya bayyana wannan masallacin a matsayin na farko da aka gina a ban kasa domin dan Adam ya bauta wa Allah.
Wannan masallacin, mai suna Al Haram, wato "Mafificin Masallaci" shi ne ya fi ko wanne daraja a duniya baki daya, yana da dadadden tarihi, ya fi ko wanne masallaci daraja da girma da kayatuwa.
A zagaye yake d a gine-ginen manyan otal-otal masu kyau da tsari wadanda idan kana daga cikisu ma kana iya hango harabar masallacin da cikinsa.
2. Masallacin Annabi SAW da ke Madinah a kasar Saudiyya

Al-Masjid an-Nabawi - Medina, Saudi ArabiaHakkin mallakar hotoKINGDOM OF SAUDI ARABIA MINISTRY OF INFORMATION
Image captionMafi darajar wuri a wannan Masallaci shi ne daga tsakiyarsa, inda kabarin Annabi Muhammad SAW ya ke

Wannan masallacin da aka fi sani da masjid An Nabawi, watau "Masallacin Annabi," shi ne masallaci na biyu mafi daraja da kyau da girma bayan na Makkah.
Annabi SAW da kansa ya gina masallacin a lokacin da ya yi hijira daga Makkah zuwa Madina shekara 1439 da ta gabata.
A ciki kabarin fiyayyen halitta yake da na manyan abokansa biyu kuma sahabbansa Abubakar da Umar Allah ya kara musu yarda.
Gidan Annabi SAW a yanzu haka duk ya shiga cikin masallacin.
Ana yi wa masallacin lakabi da 'Koriyar Hubba ta Dan Abdullahi.'
3. Masallacin Kudus da ke Jerusalem a Isra'ila

Al Aqsa Mosque - Jerusalem, PalestineHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionTarihi ya nuna cewa a baya, Annabi Muhammad SAW na jagorantar sallah ne a yayin da ake fuskantar wannan masallaci, kafin daga wata na 17 na hijira, Allah ya umurce shi da maya da alkiblar zuwa Ka'aba, da ke Makkah

Masallaci na uku mafi girma da daraja a ban kasa.
Ana kiransa da Al-Aqsa kamar yadda ya zo a Al-Kur'ani mai tsarki ko kuma Baytul-Muqaddas.
An gina Masallacin Al-Aqsa ne a garin birnin Kudus da ke kasar Isra'ila.
Masallacin shi kan sa an gina shi ne a wani yanki na Al-Haram ash-Sharif, wato "Mafificin mafaka mai tsarki", wanda su Yahudawa suke kira Temple Mount, wanda shi ne mafi tsarki su kuma a wurinsu.
Ta Baitul Mukaddas ne Annabi SAW ya tafi Mi'iraji.
4. Masallacin Hassan na Moroko

Hassan II Mosque - MoroccoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMasallacin na kallon tekun Atlantika, inda aka shimfida kasa sa da gilashi, ta yadda ake iya ganin cikin ruwa

Wannan masallacin yana birnin Casablanca ne a Moroko, kuma shi ne masallaci mafi girma a kasar, haka kuma na bakwai a jerin masallatai masu girma a duniya.
Hasumiyarsa ita ce wadda ta fi tsayi da kimanin mita 210.
An kammala ginin masallacin ne a shekarar 1993.
Masallacin Sultan Omar Ali Saifuddin a Brunei

Sultan Omar Ali Saifuddin Mosque - BruneiHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionAn zagaye Masallacin da bishiyoyi da furanni da dama, domin kamanta ni'imar Aljannah Firdausi

Masallacin Sultan Omar Ali Saifuddien, wani masallacin 'yan sarauta ne da ke garin Bandar Seri Begawan, babban birnin masarautar Brunei.
Ana yi wa masallacin kallon wanda ya fi ban sha'awa a yankin Asiya, kuma wata matattara ce ta masu yawon bude ido a Brunei.
An kammala gininsa a shekarar 1958, kuma yana daya daga cikin gine-gine da ke nuna bajintar taswirar gine-gine a duniya.
6. Masallacin Zahir da ke Kedah a Malaysia

Zahir Mosque - Kedah, MalaysiaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionDuk shekara ake gudanar da musabaka a cikin wannan Masallaci

Masallacin Zahir, shi ne masallacin jihar Kedah, wanda ke kasar Malaysia, wanda ke tsakiyar garin Alor Star.
An gina masallacin a shekarar 1912, da tallafin Tunku Mahmud, dan Sultan Tajuddin Mukarram Shah.
Wannan masallaci babba ne sosai kuma yana da kayan kawa na zamani.
7. Masallacin Faisal da ke Islamabad a Pakistan

Faisal Mosque Islamabad - PakistanHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMasallacin Faisal da ke birnin Islamabad a Pakistan shi ne mafi girma a kudancin Asiya, kuma shi ne na hudu da ya fi girma a duniya

Wannan masallacin shi ne mafi girma a kudu maso gabashi da kudancin Asiya, kazalika shi ne na hudu cikin mafi girman masallatai a duniya.
A shekarun 1986 zuwa 1993 shi ne masallacin da ya fi ko wanne girma a duniya, kafin masallacin Hassan na biyu da ke Casablanca a Morocco, da kuma bunkasa Masjid Al-Haram na Makkah da aka yi daga baya, wadanda duk suka doke shi.
8. Masallacin Taj ul da ke Bhopal a Indiya

Taj ul Mosque - Bhopal, IndiaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMasallacin na da babban lambu a tsakiyarsa, inda aka dasa wani babban tankin ruwa

Ma'anar sunan wannan masallaci, "Sarkin duk masallatai", kuma yana garin Bhopal ne a Indiya. Ana gudanar da karatun Qur'ani ma a masallacin, da rana. Masallacin shi ne mafi girma a nahiyar Asiya baki daya.
9. Masallacin Badshahi a Lahore, Pakistan

Badshahi Mosque of Lahore - PakistanHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMasallacin na daukar masu ibadah dubu 55 lokaci guda wajen sallah, kuma daga waje yana iya daukar masallata dubu 95

Sarkin daular Mughal, Aurangzeb ne ya kaddamar da Masallacin Badshahi, ko kuma "Masallacin sarauta" da ke Lahore, a shekarar 1673, wanda shi ne masallaci mafi girma na biyu a Pakistan da kudancin Asiya.
Haka kuma shi ne masallaci na biyar mafi girma a duniya. Masallacin ya yi fice a kyau, wanda ya fito da irin kasaitar daular ta Mughal.
10. Masallacin Sultan na Singapore

Sultan Mosque, SingaporeHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionAn mayar da wannan Masallacin wani gini na tarihin Singapore a hukumance daga ranar 14 ga watan Maris din 1975

Ana yi wa wannan masallacin da ke layin Muscat da ke gundumar Glam Rochor a Singapore, kallon mafi daraja tsakanin dukkan masallatan kasar. asallacin Sultan ya dade ba tare da an sauya masa komai ba tun da aka gina shi, sai wasu 'yan gyare-gyare da aka yi a harabarsa a shekarar 1960, da wasu kare-kare da aka yi a shekarar 1993.

©bbchausa.com

Abin da Ya Sa Nafisa Abdullahi ta Kama Gida Kaduna


Abin da yasa Nafisa Abdullahi ta kama Gida Kaduna
Jaruma Nafisa Abdullahi ta na daya daga cikin jarumai mata a Kannywood da suka dade ana damawa da su.

Jarumar ta yi mana bayanin dalilin da yasa ta kama gida a Kaduna, da kuma wasu abubuwan da su ka shafi rayuwar ta.
Ga yadda hirar ta mu ta kasance.
Ga ki kinga jiya kuma kinga yau kuma har yanzu ba'a daina yayinki ba Masoya na Son fina-finanki minene Sirrin?
Sirrin shine Allah na rike da ni, kasan komai a duniyar nan idan kaga mutum yana yin Sa, Idan bai nufeshi ba da yin sa ba, to ba zai taba yi ba, kuma ko da yanayin Abun idan Allah bai rikeshi ba sai kaga abun ya zama wani iri. Abinda zance kawai Allah ke rike dani.

Ko akwai wani Darasi da kika dauka a shigowarki masana'anatar Fim?
Dole mutum yana da darasin dauka, idan ka shigo masana'antar fim, ko kuma idan zaka shigo, kawai dai mutum ya tabbatar da Abinda ya kawoshi zaiyi, idan Fim din kazo ta ya zamto da gaske Fim din kazo, idan kuma ba Fim kazo yi ba ka shigo masana'antar, ba dai zan tsaya badai zan tsaya ina bayanin yanda Abubuwan suke kasancewa ba.


Wadanne nasarori kika samu daga lokacin da kika shigo Harkar Fim zuwa yanzu?
Na samu nasarori gaskiya da dama, kusan zan Iya cewa babbar nasarar duk da dai kasan wani yana yin Fim din ne saboda abinda ya keso ne, wani lokacin kuma za kayi ne don ka fadakar da mutane, To Alhamdulillahi sakona yana isa ga Jama'a kuma suna amafani dashi, kaga shima wannan babbar nasarace banda abun Duniya da dama wadanda na samu.
To wane kalubale kuma kike fuskanta?
Kalubale dai bai wuce kasan yadda mutane sun saba ganina na fito abun tausai, to idan ya zamto Na sanya kananan kaya matsatstsu to har yanzu akwai wadanda ke daukar Fim kamar dagaske ne, shima wannan Babban kalubale ne, sai daga lokacin da suka daina ganina da abun, suka fahimci Fim suke kallo. To daga nan Babban kalubalen da nake fuskanta zan daina fuskantar sa.


Kwanakin baya a shafinki na Instgram munga kina maidawa masu aikin Jarida Raddi ko akwai wani Abu da ya hadaki dasu?
Ba wani abu ya hadani dasu ba, kasan wani lokacin akwai irin kananan abubuwan da mutum ya kan fada Wanda bai kamata a daukeshi babban abu ba, kamar maganar da akayi wadda tasa har nayi wannan maganar itace nayi magana kan mata masu bleaching mutum ya tsaya yanda Allah yayishi, ba sai yayi wani abu ba kafin namiji ya soshi, to ni na yarda da hakan. Idan ina da saurayin da yake son mace fara ba zance dole sai na zama fara ba kafin ya soni, idan sona yake dagaske zai soni ne yanda Allah ya yoni ba yanda yake so ya ganni ba. Kaga irin wannan maganar ba zaka daukeshi irin babbar matsala bane, kuma wani lokacin akwai abubuwa da dama wadanda suke faruwa da wasu jaruman maza da mata Wanda ya kamata ace an daukesu anyi magana a kansu, Amma wani lokacin ba'ayi. Kuma bance 'Yan jarida na da matsala ba. Amma akwai wadanda basu daukar abun alheri sai sharri suke dauka, Amma ba duka 'Yan jaridan suke haka ba. Dalilin da yasa nayi maganar kenan Amma ba wani Abu bane ya hadani dasu ba.

Wane Buri kikeso ki cimmawa? ganin cewa duk wani abu da ya kamata ace mace ta samu a harkar nan ke ma kin samu.

Eh maganar da ka fada hakan gaskiya ne, to Amma ni a matsayina na 'Yar wasa akwai abubuwan da Na keso Wanda mu a masana'antar mu ta hausa tunanin wasu bai kai ga wajen ba, bayan akwai abubuwan da nake nema wadanda ban samu ba a harkar, akwai aure a raina kaga lokacin da wasu abubuwan za Suzo idan Allah ya taimaka bana nan. Kaga kenan zan Iya cewa ban cika cimma burina ba tunda har yanzu banyi abun da nakeso nayi ba.

Mi kika fi so a rayuwarki Wanda ke sanyaki farin ciki?
Idan kaga ina cikin farin ciki da raina, irin na hadu da kananan yara 'Yan shekara 2 zuwa 3 masu kaunata. Irin wannan abun ba karamin farin ciki yake sanyani ba, ban saniba ko suma sauran suna jin haka don nidai gaskiya inason yara kanana da sauransu.
Mi kuma yafi baki haushi a Rayuwarki?
Gaskiya akwai abubuwa wadanda ke bani haushi wanda ba sai na tsaya ina cewa kaza da kaza ne suke ban haushi ba, nidai banason negative Abu Wanda zai jawomin tsangwama koma minene gaskiya bani sonshi.

Ko akwai wata Sana'a da kikeyi bayan harkar Fim?
Inada Sana'a mana inada shirin bude Shago Na sayarda kayayyakin sawa na suttura, Amma yanzu bai fara aiki ba.


Ance kin Kama gida a kaduna minene gaskiyar Labarin?
To! Ikon Allah! Ya zama batu kenan? To bari na tambayeka zaman hotel ba issue bane? Yanzu idan naje kano, Abuja, Zariya da sauransu a hotel nake zama, Gidan iyayena a jos yake bana aiki a jos kuma idan naje jos din baifi inyi kwana 3 zuwa 4 ba, na Dade da yawa sati guda, kaduna ne kawai nafi zama kuma a wurin nake aiki, idan zaman hotel dina ya zama issue mi ya kamata nayi ba In kama gida ba, kuma Gidan ma wanda ba koda yaushe nake zama ba, domin ina zuwa wurare da dama, ko kuna tunanin duk Inda nake zuwa zan sayi gidane? Ai bazai yiwuba Allah bai kaddaramin wannan matsayin ba tukunna. To idan na kama gida ai ba wani Abu bane ko ni Na fara? Kaga kenan ba abun magana bane. Da kama gida da zaman hotel wanne yafi ai kaga gwara kama gida.

Minene gaskiyar labarin cewa an sanya maki biki Amma ba ki fadi da Wanda aka sanya maku ba, sai lokacin bikin ya matso zaku sanar?
Nan dai ban saniba, bansan ko masu maganar ne suka sanyamin ranar ba, babu wannan maganar gaskiya, Amma inada manema kuma inada Wanda Na keso, Kuma insha Allahu Wanda nakeso din ne zan aura.

Ko Dan Fim ne zaki Aura?
To minene aibun Dan Fim? Mi zai hana Na auri Dan Fim, Ba Dan Fim zan aura ba, inada Wanda zan aura Na fitar dashi Amma ba Dan Fim bane.

Ance bakison ana maki maganar Adamu Zango shin gaskiyane?
To yanzu da kayi min maganar Adamu zangon mi nayi maka? A gayamin wane dalili ne ba zanso a yimin maganar Adamu Zango ba, hasalima idan ana aiki idan ba'a yimin maganar shi ba, ni zanyi wa mutane maganar sa, to wannan zancen mutane ne, mutane ma akwai Su da bata lokacinsu.

Kin taba nadamar shigarki harkar Fim kuwa?
Idan kaga mutum yayi nadamar yin abu, to rashin dadin abun yafi dadinsa yawa, to ni a nawa bangaren dadin ya linka rashin dadin nesa ba kusa ba. Kaga kenan babu yanda zance nayi nadama. Banyi nadamar shigowata hausa Fim ba, Inda ace za'ayi banda duniyar nan da muke ciki, idan aka tashi halittomu kila abun da nakeso nayi kenan harkar Fim. To banyi nadama ba.

Daga karshe wane sako ko Albishir kike dashi ga masoyanki?
Sakona garesu shine suci gaba da kaunta, kamar yanda sukeyi kuma nima ina kaunarsu nagode Allah yabar zumunchi.

Shin Mata 'Yan Fim Karuwai ne Ko masu fadakarwa?


(Gaskiyar magana) Kwana biyu da ya wuce, na yi rubutu game da abinda ya shafi
Adabin Bariki. Na fadi nau'ika na karuwai da rabe raben su. A cikin masu comment akwai
wadanda su ka yi ta tambaya ta, Mata 'yan wasan Hausa fa, suma dole a sako su a jerin rabe
raben karuwan .A kwai wacce ta turo min sakon, gaskiya na yi rashin adalci in har ban sa ka su a jerin karuwai ba.

Ma'anar da na bayar ta karuwa ita ce, wacce ta bar gaban Mahaifanta bisa wani dalili ta
kama daki da zummar kasa hajar da Allah ya hore ma ta. Wasu na ganin Mata 'yan wasan
Hausa ma sun bar gaban Mahaifansu, kuma har sun kama gida .
Da farko niyya ita ce ginshikin kowanne aiki, duk yarinyar da ta baro gaban iyayenta da
niyyar shiga wasan Hausa, ba ta na barowa da niyyar kasa hajar da Allah ya hore ma ta ba ne. Idan ka na ganin ai idan ta kama gida, maza na kai ma ta ziyara, wanda da wannan dalilin ka ke ma ta kallon karuwa.

Me za ka ce da wadanda kan zo karatun jamia, mahaifansu su kama mu su gida su zauna kafin su kammala karatu?
Ya kuma za ka kira maaikaciya da aka yiwa canjin aiki garin da ba na ta ba, ta je ta kama gida? Hujjar ka su na fita location da Maza har a kwana ana shooting, wanda a tunanin ka masha'a ake. Me za ka ce da malamar asibitin da ke kwanan duty tare da Maza?
Me za ka ce da Yar sanda Mace da ke kwana tare da Maza a dutin dare? Ko ka na ganin wasan Hausa ba sana'a ba ce? Ka na da hujjar kiran 'yar wasan Hausa da sunan Karuwa? Ok ina hujja. Wani ya turo min sako, wai in je in duba scandal na Hiyana, wannan karara ya nuna tsantsar rashin adalci da har za'a dauki hukuncin mutum guda a hukunta mutum dubu da shi.

Me za ka ce da matan da kasuwancin saye da sayarwa ke kai su kasashe, su je lafiya su
dawo lafiya? Ko duk karuwai ne a mahangar ka. Domin idan suka je su kan kama daki a Hotel ne su zauna har su gama alamuran su...
Mata 'yan wasan Hausa ba karuwai ba ne, idan kuma ka ce karuwai ne, saboda sun kama gida sun zauna. To fa duk wata daliba ko ma'aikaciya da ta kama gida ta zauna sunanta Karuwa kenan. Idan kuma dalilinka ta na cudanya da Maza, to fa duk wata Daliba ko Maaikaciya sunanta Karuwa a mahangarka.

Wani ya tambaye ni game da mata mawaka, wadannan Case din su mai sauki ne, da damar
su , su na gaban Mahaifan su ne ko shakikan su. Ko da sun kama gidan ne ba sunan su Karuwai ba.
Rubutuwa : Auwal Garba Danbarno