April 2018 - NewsHausa NewsHausa: April 2018

Pages

LATEST POSTS

Saturday 28 April 2018

video: Kalli yanda wani ya nemi kotu ta rab,a auren sa sabo da kyawun matar sa

video: Kalli yanda wani ya nemi kotu ta rab,a auren sa sabo da kyawun matar sa
danna rubutun dake kasa domin kallon yanda videon ya kasance

Download now

video: An taba yimin fade inji jaruma rahama sadau

video: An taba yimin fade inji jaruma rahama sadau

danna rubutun dake kasa domin kallon videon yadda abin ya kasance

Download now

Monday 16 April 2018

Maketatan Mutane Ne Suka Talauta Al'ummar Nijeriya - Inji Buhari

Maketatan Mutane Ne Suka Talauta Al'ummar Nijeriya - Inji Buhari

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa Maketatan shugabanni suka talauta al'ummar Nijeriya ta hanyar sace arzikin kasa.

i wannan ikirarin ne a lokacin da 'yan Nijeriya mazauna kasar Birtaniya suka kai masa ziyara a birnin Landon inda ya jaddada cewa gwamnatinsa ta yi kokari wajen maido da Nijeriya kan tafarkin ci gaba idan aka yi la'akari da yanayin da ta karbi mulki daga hannun PDP.

Ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da shirinta na kwato kudaden sata duk da yake ba zai yiwu a gano dukkan kudaden da aka wawure ba inda ya nuna takaicinsa kan yadda aka sace kudaden Nijeriya wanda har sun kasa tsara yadda za su yi rufa-rufa.
©rariya

Friday 13 April 2018

Saudiyya Ta Yi Nasarar Soke Wasannin Sharholiya Da Aka So Shiryawa A Kasar


Bayan taron gaggawa da ya gudana tsakanin Yerima mai jiran gado kasar Saudiyya da membobin majisar koli ta
manyan malamai a gidan ministan al’amuran addini Sheikh Saleh bin Abdul’aziz gwamnatin ta soke shirin kida da wasa da mata wanda za a gabatar a Riyad. Sannan kuma ta soke taron da mawakiyar nan Majidatu Alrumy 'yar kasar Lebanon za ta gabatar a jami’ar Gimbiya
Nuratu a Riyadh.

Ta kuma soke taron mawakin nan Khazeem Saheer dan kasar Iraq. Haka kuma ta rufe wurin shakatawa a garin Jazan sakamakon cakuda maza da mata a wajen taron wata gala.

Thursday 12 April 2018

Mawakan Yanxu Mun Saki Al'adun Mu - Inji Maryam Fatimoti

MARYAM Saleh (Fantimoti) mawakiya ce da ake yi mata lakabi da Maman Mawaka. Hakan babu mamaki saboda tsawon lokacin da ta shafe a harkar waka, domin kuwa za a iya cewa kusan duk mawakan da ke waka a yanzu da ma wasu wadanda su ka gabace ta a Kannywood sun yi yayin su sun gama, amma ita har anzu ana damawa da ita. Ta yi wakoki a fannoni daban-daban kamar na soyayya, na yabon Manzon Allah (S.A.W), na siyasa, da sauran su. 

Wani abu game da Maryam shi ne a duk lokacin da ake ganin kamar an daina yayin ta, sai kuma a gan ta ta fito da wasu sababbin wakoki da ake sakawa a cikin finafinai. Tun daga fitowar fim din 'Mansoor' wanda ya ke dauke da wakar ta, sai kuma aka koma kan ta, kowa na so ya rera masa wakar fim din sa.

Wakilin mu, MUKHTAR YAKUBU, ya tattauna da Fantimoti a Kano a game da yanayin da ta ke ciki, musamman a bangaren waka. Ta fede mana biri har wutsiyar sa kan sirrin waka:

FIM: Maryam Fantimoti, ki na cikin mawakan da su ka dade a cikin wannan masana’anta ta Kannywood, ko da yake tsawon lokaci ba a jin ki sosai. Wannan ta sa ake ganin kamar kin ja baya a harkar waka. Yanzu kuma sai aka fara jin muryar ki. Wannan ya sa ake ganin kin dawo kenan daga hutun da ki ka tafi.

FANTIMOTI: To, assalamu alaikum. Wannan maganar da ka fada za a  iya cewa haka ne, domin ka san ita waka ta na tafiya ne da zamani, domin ni lokacin da na shigo masana'antar akwai raino. Ka ga ni Ali Nuhu ne ya karbe ni kuma ya gwada ni da wannan wakar mai suna ‘Fantimoti’, wadda har zuwa yau na ke amsa sunan ta. Don haka  lokacin  akwai yarda  da amana, ba kamar yanzu ba. 

To lokacin da na yi wannan wakar Ali Nuhu ya kai wa marigayi Tijjani Ibraheem sai ya ce, “Wannan muryar babu irin ta, don haka an samu canjin Zuwaira Isma’il!” Ka san ni muryar Zuwaira na ji na shigo waka lokacin da su ka yi wakar ‘Dawayya’ ita da Misbahu M. Ahmad. To ita ta jawo ni, don na ga ni ma fa mawakiya ce a Islamiyya, don haka ni ma zan iya. Amma ni kuma sai na zo da salo na tatsuniya; da na rubuta na kawo wa Ali Nuhu sai ya ce ai ni murya ta ita ce makami na. Don haka tun daga nan zan iya ce maka ban kara waiwayar biro ko takarda ba don na rubuta waka, sai dai duk inda ka gan ni kawai rera ta zan yi.  

To, da yake akwai kulawa ta magabata sai na ci gaba da samun nasara, don ka ga bayan Yakubu ya raine ni sai Mudassiru ya dora. Allah Ya saka musu da alheri; ba zan iya mantawa da su a tarihin rayuwa ta ba. 

FIM: Akalla shekara nawa kenan daga wancan lokacin  zuwa yanzu?

FANTIMOTI: E to, shekarun da dan tafiya ba laifi, domin na shigo masana’antar fim tsakanin 1999 ko 2000, don haka ka ga ai na dade a cikin harkar. 

FIM: A tsawon wannan lokaci, kin yi wakoki kala-kala. Bayan wakar 'Fantimoti' da ta fito da ke, za ki iya tuna wasu fitattun wakokin ki?

FANTIMOTI: Wato lokacin da na zo masana’antar gaskiya an fi yin waka a kan abin da ya danganci fim din, ana yin waka daidai da yadda sakon labari ya ke, don haka labarin fim din ake dauka a yi waka, wanda kuma a yanzu ba haka ba ne. Don ba zan manta ba, akwai wakar da na yi ta fim, da Maryam ta zo yin wakar a fim din sai da ta yi kuka na gaske a fim din saboda tausayin da ya ke cikin wakar. To yanzu  waka ta juya soyayya kawai, amma mu a da ba haka ba ne. 

FIM: Wakoki ku na da sun fi daukar dogon lokaci ana yayin su fiye da na yanzu. Me ya jawo haka?

FANTIMOTI: E to, ya danganta. Ka san ita waka ta na da matakai, domin idan Allah Ya hore maka waka matakin ta na farko shi ne murya, sai kuma basira. Idan ka na da murya ba ka da basira, za kai waka kuma za ka ci abinci. Sai kuma balaga, wato saka maganganun da zai fito a ciki. Sai kuma shirya baitocin. Sai kuma daukaka da karbuwa, yadda zai zama kowa ya san ka.

FIM: Wato kenan wannan shi ne ya bambanta mawakan da da na yanzu?

FANTIMOTI: E, gaskiya ne. Ka san lokacin da su Yakubu da su Mudassiru su ke waka gaskiya ba za a yi waka ba sai da ma’ana. Wannan ya sa ta dalilin raino na da su ka yi yanzu da manyan mutane na ke mu’amala. Saboda manyan mutane su na so su ji abubuwa na al’ada a cikin waka, kuma a yanzu waka mun saki al’ada.

FIM: Bayan tsawon lokaci ki na wakokin finafinai, sai kuma ki ka karkata akala wajen wakokin yabon Manzon Allah  (S.A.W.), kuma sai ya zama a wannan bangaren ma ki ka shahara kamr da man a nan ki ka fi kwarewa. 

FANTIMOTI: Wannan gaskiya ne, amma abin da ka fada ba haka ba ne. Lokacin da mahaifi na ya kai ni Islamiyya shekara ta takwas, to a lokacin a kan tebur malamai ya ke dora ni na yi kasida a cikin ajin mu, don haka tun a lokacin aka koya min son Manzo da kuma yin yabo a gare shi. Hakan ya sa na samu mukami a makarantar, don malami zai zo da kasida ya na biya mana, amma sai ya ji na haddace. Tun daga nan na fara iya yabon Manzon Allah (S.A.W.), amma yanzu abin bayyana ya yi. 

FIM: Yaya za ki kwatanta wakoki na yabon Manzon Allah da kuma na finafinai da ki ke yi? Wanne ne ya fi sauki?

FANTIMOTI: E, a wajen rerawa  daya ne, amma a wajen da bambancin ya ke shi ne wakokin yabon  Manzon Allah gaskiya sai ruhi ya amsa. Idan  ruhi ya amsa kuma ka yi ladabi, to idan aka samu wannan shi ne za ka ji yabo ya karbu. 

FIM: Akwai wani lokaci da ake korafi kan masu wakokin yabo, ana cewar ba su cika yin lafazi na isar da sako a cikin wakokin su ba. 

FANTIMOTI: Wannan haka ya ke. Wato idan Allah Ya yi baiwar rera waka, to shi gida na yabo dole sai dai ka je ka yi  ladabi a ba ka. Amma idan ka ce za ka yi don ka na da murya, to akwai matsala. Ka’ida shi ne: ka je malamai su ba ka. Kamar yanzu idan ka ji wakar ‘Mukarrima’ za ka san cewa ta fi karfin kai na, ba ni aka yi yi, wato waka ta da na ke cewa: “In ba ka gane me mu ke nufi ba ku ce da su mu na nufin Ma’aiki.” To ka san abin ya fi karfin kai na, don haka malami na, maulana Malam Hafiz Abdallah, shi ne ya ba ni wannan kasida na rera. 

Don haka duk lokacin da za ka yi wake na yabon Manzon Allah (S.A.W.) ka je ka yi ladabi ko ka je wajen masu abin, Ahlul Baiti - jikokin Manzon Allah - su ba ka. Lamarin da ake fada da izini domin su fa gaske ne ko a lahira bare a duniya. Don haka idan su ka ba ka lamuni, in ka yi yabon sai an saurare ka. 

Amma don kawai ka iya wakar fim ka ce za ka yabi Manzon Allah, to akwai matsala. Sai dai ka yarda malamin ka ya ba ka. Don a kasashen da su ka ci gaba za ka ga marubuta waka daban, masu rerawa daban. Ba kamar mu nan ba, mutum ya ce shi ne kida, shi ne rubuta waka, shi ne rera waka. 

FANTIMOTI: Wakar ki ta fim din ‘Mansoor’ ta kara dawo da ke wakokin finafinai. Ko yaya ki ka kalli yadda tsarin wakar ya ke a yanzu?

FANTIMOTI: A wannan yanayi dai ba zan iya cewa komai ba domin ba da kowa na ke rera waka a cikin yaran da su ke tashe a yanzu ba, domin zan iya cewa kai ni ban taba yin waka da su ba! Don ban yi waka da Nura M. Inuwa ba, ban taba yin waka da  Umar M. Shareef ba. Amma na yi waka da Ado Gwanja, Hussainin Danko, Rarara, Nazifi Asnanic, Sani Hassan, Mahmud Nagudu, duk na yi waka da su. 
To abin dai da ya faru su mawakan ne yanzu da su ke cewa da ni Maman Mawaka, an ba ni lambar yabo an ce da su ba za su iya biya na kudi ba, na raina musu waka. To ni  abin da zan warware musu, ni har abada a harka ta ta waka na dauki mawaki ko yau ya fara waka abokin sana’a ta ne; zan taimake ka, za ka taimake ni. Kuma na gode wa Allah da Ya raba ni da girman kai. Don haka su ajiye wannan lissafin. In ka na so a yi maka wakar ma ka zo za a yi maka ka rike kudin ka, don mu ba abin da Allah bai yi mana a cikin ta ba. 

FIM: Ko wadanne irin nasarori ki ka samu a harkar waka?

FANTIMOTI: To, nasarorin su na da yawa. Nasara ta farko ita ce zama da dukkanin mawaka lafiya. Na samu nasara ta fahimtar iyayen gida na a harka ta waka. Na samu nasara ta daukaka ta ba iya kasa ta ta tsaya ba, tunda cikin ikon Allah na fita aiki kasashen makotan mu kamar Nijar, Chadi, Kamaru, Ghana, Togo.

FIM: Wanne irin kalubale ki ka fuskanta a harka ta waka?

FANTIMOTI: E to, ka san ita rayuwa ba a raba ta da kalubale, don tun daga gidan ku da aka haife ka ba ka rasa kalubale. Amma kalubalen da ya fi damu na shi ne rashin hadin kan mawaka. A matsayin mu na ’yan’uwan juna ya kamata mu hada kai mu yi aiki tare. Wannan shi ne abin da ya kamata  mawaka su yi.

FIM: Menene sakon ki na karshe?

FANTIMOTI: To, shi ne dai maganar hadin kai. Ina kara kira ga mawaka mu hada kai mu yi aiki tare yadda za mu zama masu daraja sana’ar mu

Mujallar Fim Ta Wannan Watan Ta :Gwagwarmayar Da Jaruma Sadiya Adam Da Angon Ta Sanusi Ahmad Su ka Shiga kafin Iyayen Su, Su kyale su Yi Aure


1. Hira da Maryam Isah (Ceeter) a kan ci-gaban da ta samu a Kannywood tun bayan mutuwar auren ta.

2. Gwagwarmayar da jaruma Sadiya Adam da angon ta Sanusi Ahmad su ka shiga kafin iyayen su su kyale su su yi aure a makon jiya.

3. Ni yanzu tsoron aure na ke ji, inji Fati KK. Hira da jarumar a kan halin da ta ke ciki bayan mijin ta ya sake ta da 'ya'ya biyu kwanan nan. Shin za ta dawo harkar fim ne ko yaya?

4. Labarin rasuwar wasu 'yan fim guda biyu.

5. Yadda jarumi Bello Mohammed Bello (General BMB) ya iza wutar rikicin 'na fi ka, ni ma na fi ka' wanda ake yi tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango.

6. Furodusa Sani Sule Katsina inuwar giginya ne, inji jarumi Aminu A. Daggash wanda ya yi aure a makon jiya.

7. Yadda aka bata wa mutane rai a taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya da aka yi a Katsina.

8. Akwai sauran labarai masu gamsarwa a cikin wannan mujallar.

Bani da ƙawa a Masana'antar kannywood - Inji Jaruma Umma Shehu

Shahararriyar jaruma wacce tauraronta ke kan haskawa a dandalin shirya fina-finan Hausa, Umma Shehu ta bayyana alakarta a farfajiyar Kannywood.

A cewar Umma bata da wata da ta rika a matsayin kawa a masana’antar saboda tana gujewa duk wani matsala ko abu da zai tunzura ta.

Jarumar ta jaddada cewa ita sana’arta kawai ta sanya a gaba saboda haka bata da lokacin kulla ko wace alaka ta kawance.

Idan dai bazaku manta ba a kwanakin baya ana ta ba’a ga jarumar bayan wani hira da tayi da Aminu Sheriff Momo a wani shirin talbijin sakamakon wani tambaya da ta kasa amsawa wanda ya shafi addini.

Jarumar ta kuma jaddada cewa ita batayi fushi ba akan abunda ya faru a tsakanin su.

Wednesday 11 April 2018

Hirar Fim Magazine : Haidar Adam A Zango Ya Zamo Mawakin Hip hop Mai Lakabi Da "Star boy"

Babban ɗan fitaccen jarumi Adam A. Zango, mai suna Ali Haidar Zango, ya fara waƙar hip pop.
Za a riƙa yi masa laƙabi da "Star Boy".
Ali, wanda aka fi sani da suna Haidar, da kan sa ne ya bayyana hakan a shafin sa na Instagram, inda ya sanar da mabiyan sa cewa waƙoƙin sa guda biyu su na nan fitowa da sunan 'Godiya' da kuma 'Rayuwa'.
Ya kuma tura da saƙo inda ya bayyana cewa mahaifin sa ne ya gano basirar da Allah ya ba shi.

Haidar ya sha alwashin ba zai ba mahaifin nasa kunya ba a wannan aiki da ke gaban sa.
Mujallar Fim ta gano cewa har an kammala shirye-shiryen ɗaukar bidiyon wani ɓangaren na waƙoƙin matashin mawaƙin.
Baban sa ya aika da wani guntun bidiyon waƙar Haidar ɗin a shafin sa na Instagram wadda ba ta wuce minti ɗaya ba.

A tattaunawar sa da mujallar Fim, Adam A. Zango ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ba a kammala aikin bidiyon waƙoƙin guda biyu ba, amma da zarar an gama za a sake su baki ɗaya, na gani da kuma na saurare.
Mutane da dama dai da man sun zura ido su ga yadda ɗan fitaccen jarumin zai kasance idan ya girma, kasancewar tuni dai an san makomar 'ya'yan wasu fitattun jarumai irin su Ali Nuhu da Sani Danja, wanda kowa ya san 'ya'yan su sun daɗe da fara fitowa a cikin finafinan Hausa.

Wasu sun riƙa hasashen inda ɗan gidan Zango zai karkata; shin mawaƙi ko makaɗi zai zama idan ya girma, ko kuwa shi ma jarumi zai zama kamar yadda sauran 'ya'yan jarumai su ke zama jarumai su ma?
Sai dai shi Haidar an ga ya canza layi, inda ya bayyanar da kan sa a matsayin mawaƙi.
Ana ganin hakan ba abin mamaki ba ne, kasancewar baban nasa shi ma fitaccen mawaƙi ne.
Tun da farko Adam A. Zango da kan shi ya tura hotunan Haidar a Instagram, inda ya gabatar da shi ga mabiyan shafin sa su sama da 567,000. Haka kuma ya yi wa yaron addu'ar fatan alheri.

Ɗimbin yaran Zango ɗin, irin su Maryam Giɗaɗo, sun kwafi hotunan na Haidar sun wallafa a nasu shafukan na soshiyal midiya.
Haka kuma an buɗe wa yaron shafi nasa na kan sa a Instagram a ranar 5 ga Afrilu, 2018, wanda a cikin kwana biyar kaɗai har ya samu mabiya mutum 27,400.
Tun bayan rasuwar matashin mawaƙin hip pop Ameer Isah Hassan, wanda aka fi sani da Lil Ameer, an riƙa samun bayyanar yara ƙanana waɗanda su ka bazama cikin waƙoƙin na Ingausa.

Yanzu haka dai an samu 'ya'yan 'yan fim guda biyu waɗanda su ke hip pop, wato Sani TY Shaban da Ali Haidar Zango.
Wani abin la'akari kuma shi ne dukkan yaran kowanne ana yi masu laƙabi da wani suna kamar yadda al'adar hip hop ta ke. A yayin da ake kiran Sani TY Shaban da "Freii Boi", shi kuma Haidar laƙabin sa shi ne "Star Boy".

Labari Mai Dadi A Kannywood : Auren Sadiya Kabala Yazo

A RANAR Asabar ɗin wannan makon, wato 14 ga Afrilu, 2018, za a ɗaura auren ɗaya daga cikin jarumai mata da ke Kaduna, wato Sadiya Kabala.
Za a ɗaura auren ta da sahibin ta mai suna a masallacin Juma'a na Al-Mannar da ke Kaduna da misalin ƙarfe 1:00 na rana.

A jerin tsarin bikin wanda mujallar Fim ta gani, an nuna cewa za a fara shagalin auren a ranar Alhamis ɗin nan a lambun shaƙatawa na Ƙofar Gamji.
Bayan ɗaurin auren kuma za a yi dina a wani otal mai suna Silver Sand da ke Titin Katuru, Unguwar Sarkin Musulmi.
To Allah ya sa a ce gara da aka yi, amin.

Na Yi Nadamar Yin Soyayya Da Timaya, Inji Ummi Zee-Zee

Fitacciyar tsohuwar jarumar finafinan Hausa, Ummi Zee-Zee ta bayyana cewa babban kuren da ta tafka a rayuwarta kuma take dana-sanin yin hakan shi ne soyayyarta da shahararren mawaki Timaya.

Zee-Zee ta bayyana haka ne cikin wata hira da tayi da jaridar Daily Nigerian, inda ta yi raddi game da wani jita jita da ake yadawa na cewa wai ta sauya zuwa addinin Kirista saboda tarayyarta da Timayan.

A cikin hirar, Zee-Zee ta bayyana cewar tana matukar girmama marigayi Dan Ibro da marigayiya Aisha Dan Kano, sa’annan tace ita mutumce mai yawan karanta Al-kur’ani da Hadisan Manzon Allah don kara samun haske a Musulunce.

Da aka tambayeta game da shirin aure, Zee-Zee ta tabbatar da cewar a yanzu haka ta shirya yin aure, kuma tana rokon Allah ya tabbatar mata da burinta daga yanzu zuwa karshen shekara.

Daga karshe ta tabbatar da cewar ita mai kudi ce, don haka ta daina fitowa a fina finan Kannywood, inda tace “Nawa za’a biya ni?”, ta kara da cewa tana da arziki sosai, don haka idan ma wani yayi mata kyautan wasu 'yan miliyoyi ba zata gode masa ba, don kuwa ta fi karfinsu.

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Hausawa kance komai kyauwon ɗa ya gadi uba nai to yau haidar adam a zango shima ba'a barshi a baya ba inda shima ya fitar da sabon album dinsa mai suna "Take over" wanda ya kamala shooting na wannan album inda wakokin album din kamar haka :-



1. Godiya

2.  Rayuwa

3. Take over.

Album din ya samu director by msk sai kuma co-sponsored by the white housa family. 

Wanda wannan yaro ya fara nuna tashi fasahar wanda a nan gaba kadan hausaloaded.com zaka kawo muku wannan wakokin sai ku kasance da mu. 

Shekarata Uku Ina Tara Kudin Da Zan Sayawa Buhari Fom Din Takarar 2019'


Daga Rabi'u Biyora

Sunansa Yahaya Abubakar dan asalin jihar Kano. Matashin ya bayyana cewa tun shekarar 2015 yake ajiye kudade a asusunsa dake 'First Bank' saboda ya siyawa shugaba Buhari fam din takara.

Yace yanzu lokaci ya yi da zai kwaso kudaden gaba daya don cikar burinsa, tun da shugaba Buhari ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara.

Abinda Nake Yi Bayan Na Daina Fitowa A fina-finai - Sadiya Gyale (Cikakkiyar Hire)

Sadiya Gyale, wannan suna ne da ya jima yana yin tashe a cibiyar shirya Fima-fimai wacce aka fi da kira da, ‘Kannywood.’ Kamar sauran tamkar ta, Sadiya Gyale, ta daina fitowa a cikin shirye-shiryen Fima-fiman, bayan ta kwashe shekaru masu yawa da za a iya cewa kusan tun farkon kafuwar cibiyar shirya Fima-fiman ta Kannywood. Ta yi zamanin da fuskanta mafiya yawan mutane ke son gani a cikin Fim din, masu shirya Fima-fiman da masu bayar da umurni duk ribibinta suke yi. Kamar yadda masu sha’awan kallon Fima-fiman ke shaukin jin sunanta da kuma ganin fuskanta a cikin Fima-fiman.
To wace ce Sadiya Gyale, tana ina ne kuma a halin yanzun, bayan barin ta cibiyar shirya Fima-fiman ta Kannywood, me take yi ne a halin yanzun, wace shawara kuma take da ita ga ‘yan fim din na yanzun, musamman mata? Duk amsoshin wadannan tambayoyin da ma wasun su suna cikin abin da za ku karanta a wannan hirar na ta.

A sha karatu lafiya: Muna so ki fada mana cikakken tarihin rayuwar ki?

Assalamu alaikum, kamar yanda ku ka sani, Suna na Sadiya Muhammad (gyale), an haife ni a Lagas ne, a watan Satumba shekarar 1985, iyayena duka Fulani ne, na yi karatun Firamare da Sakandare a Kano, na gama Sakandare a T/wadan Dankadai, na shigo’Industry,’ a shekarar 2003. Alhamdulillah, mun yi lafiya mun gama lafiya, muna yi wa sauran fatan alheri.

Bayan kin bar fitowa a Fima-fimai, akwai wani aikin ko sana’an da ki ka koma yi ne, ko kuma makaranta ki ka koma?

Bayan na daina fitowa a Fima-fimai, ina sana’o’i kala-kala, na saye da sayarwa, da noma duk ina yi.

Mun ga kin samu shaidar yabo, ko za ki yi mana bayani kan yadda aka yi ki ka samu?

Wata kungiya ce ta makaranta Mujaallar fim, su ne suka karrama ni, da ma sun taba karrama ni, ban samu damar halarta ba.

Malama Sadiya, ya ya batun aure, yaushe za ki kara kiran mu mu rakashe?

Insha Allah muna ta addu’a, Allah Ya kawo miji nagari mafi alheri.

Ko Kina da sha’awan zama mai bayar da umurni ko mai daukan nauyin shirya Fima-fiman ne, na kanki bayan kin yi aure?

Daman can nakan dauki nauyin shirya Fima-fiman, kuma ko na yi aure ma zan ci gaba da hakan.

Ta ya ya aka yi ki ka samo lakabin sunan “Gyale”?

Na samo sunan gyale ne a fim din gyale, fim din gyale shi ne fim di na na farko, wanda na fara yi, wannan ne ya sa ake kira na da Sadiya gyale.

Kin yi fima-fimai da dama, wanne ya fi kwanta ma ki a rai?

Akwai fima-fiman da suka kwanta min a raina sosai, kuma ina alfahari da su irin su, Gyale, Sanafahana, Kugiya, Armala, Gudun kaddara da dai sauransu.

Wane fim ne ya fi ba ki wahalar yi?

Fima-fiman din da suka ba ni wahala suna da dan yawa.

Ko akwai wani ‘role’ da aka taba ba ki a fim ki ka ki karba ki hau?

Ehh, akwai wadanda na ki karba saboda wasu dalilai.

Ko akwai wata jarumar fim da ta zama abar koyi gare ki a duniyar fim (Indiya, Amurka, China ko fima-fiman kudanci)?

Babu ita, ba wata jaruma da nake koyi da ita.

Wane fim ne na karshe da ki ka yi?

Ba zan iya tuna sunan fim din da na yi na karshe ba, amma na san fim din Falalu dorayi ne.

Ko akwai furodusa da daraktan da ki ka fi son yin aiki da su?

Ehh, akwai su da yawa, ba za su lissafu ba, wadanda nake jin dadin aiki da su.

Me ya sa?

Kila saboda haduwar jinni ne.

A ganinki wasu abubuwa ne suka sauya a masana’antar fim a yanzu, idan aka kwatanta da lokacin ku?

Abubuwa da yawa muna samun labarin sun sauya, amma tun da ba cikin harkar nake ba yanzu ba zan iya cewa komai ba.

Su wane ne gwanayen ki a fagen fim?

Gwanaye na suna da yawa mata da maza, wadanda su ke burgeni.

Wace shawara za ki baiwa ‘yan mata masu shiga fim a yanzu da masu sha’awan shiga?

Ina masu fatan alheri, kuma ina ba su shawara da su rike sana’ar fim, don mu har gobe muna ganin amfanin ta, muna kuma cin albarkacin ta. Allah Ya karawa wannan sana’a albarka da daukaka ina alfahari da ita.

Ko za ki fada mana wasu irin saye da sayarwan ki ke yi, da kuma fima-fimai nawa ki ka dauki nauyin shiryawa?

Abubuwa ne da yawa, kayan yara, kayan maza da na mata, har da kayan noma da noman kan shi.

Yanzu idan aka kira ki, don ki fito a fim, za ki karba ki je ki yi ?

To ya danganta da irin fim din da zan iya fitowa ne a halin yanzu

Mun gode da lokacin da ki ka ba mu.

Ni ma na gode.

Kyan da ya gaji uban sa: Dan Ronaldo ya kwaikwayeshi



auraron dan kwallo, Cristiano Ronaldo kenan a wadannan hotunan yake kokarin kwaikwayar irin abinda mahaifinshi yayi na cin kayatacciyar kwallo, Ronaldo dai yaci Juventus kwallo wadda ta dauki hankulan Duniya. To ga dukkan alamu danshi zai gajeshi.

A jiya, Lahadine gurin atisaye dan Ronaldon yayi wannan bajinta, kamar yanda Daily Mail ta kasar Ingila ta ruwaito.

Sunday 8 April 2018

KOYAR DA KIMIYAR AURE Abubuwan Da ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE Zata Koyar Guda (41) - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa



Wannan makaranta ta ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE ta shirya tsaf domin koyar da kimiyar zamantakewar aure, ga bangarori guda uku na maza mata
Zawarawa maza da mata 
Samari da Yammata
Mazan aure da matan su. 
Domin kara inganta rayuwa ta maaurata wadannan kwasa kwashe sun hada
1- Manufar yin aure
2 Hikimar yin aure
3 Falalar yin Aure
4-Hukuncin yin aure
5 - Yadda ake neman aure
6 - Irin matar da ake so a aura
7- Irin mijin da ake so a aura
8- Yadda ake zuwa zance da yadda ake yi
9_ Yadda ake bincike kafin aure da abubuwan ake bincikawa guda biyar
10- Mata guda 42 da suka haramta mutum ya aure su saboda nasaba ko shan nono ko surukuta.
11 Rukunan Daurin aure.
12 - Sadaki da hukunce hukuncin sa
13 Wanene Waliyyi da sharuddan zama Waliyyi da kashe kashen waliyyai na aure
14 Sigar daurin aure da yadda ake yin ta.
15 - Shedun aure da siffofinsu.
16- Sanya sharudda a cikin aure.
17 - Yadda ake bukukuwan aure a musulunci, da aladun da suka shigo cikin aure marasa kyau. 
18- Yadda ake walima da shagalin aure.
19- Ladubban tarewar amarya da Ango.
20 Hakkokin mata akan miji
21 Hakkokin miji akan mata.
22 Ladubban kwanciyar aure
23 Abubuwan da suke kara soyayya tsakanin maaurata.
24 Yadda ake gyara matsalolin aure idan sun taso.kafin akai ga saki 
25 Abubuwan da suke kawo albarka a gidan aure
26 Abubuwan da suka halatta, da wadanda suka haramta tsakanin maaurata a lokacin da mace take al'ada
27 Abubuwan da suke kawo mutuwar aure
28 Hukuncin hana daukar ciki, ko zubar da ciki, da Tsarin iyali a musulunci.
29 Sharuddan da mutum, zai cika kafin ya kara aure.
30 Wanda ya kasa daukan nauyin iyalinsa. 
31 Hukuncin wanda ya kauracewa iyalinsa. bisa zalunci ko larura ko horo. da sanin lokacin da shari'a ta iyakan ce. 

32 Mutuwar aure, da hukunce hukuncan sa,
33 Hakkokin matar da aka saka, 
34 Wa yake da hakkin rike yaya bayan mutuwar aure? 
35 - Yadda ake kul'i (mace ta nemi rabuwa) da abubuwan da suke jawo shi. 
36- Hukuncin komai bayan saki. 
37- Idda da hukuncin ta a musulunci 
38 - Hukuncin Ila'i Rashin kusantar iyali da rantsuwa ko saka sharadi. 
39-  Hukuncin Zihari kamanta jikin mahaifiyar sa da matarsa. Ko sauran mahramansa. 
40 Hukuncin lia'ni idan mutum yana zargin matarsa da zina. 
Reno da tarbiyya tun daga daukar ciki har zuwa haihuwa da yaye, 
Hakkokin yaya akan iyaye da hakkokin iyaye akan yaya. 
41 Yadda ake Takaba idan. Miji ya mutu.

KOYAR DA KIMIYAR AURE Abubuwan Da ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE Zata Koyar Guda (41) - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa



Wannan makaranta ta ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE ta shirya tsaf domin koyar da kimiyar zamantakewar aure, ga bangarori guda uku na maza mata
Zawarawa maza da mata 
Samari da Yammata
Mazan aure da matan su. 
Domin kara inganta rayuwa ta maaurata wadannan kwasa kwashe sun hada
1- Manufar yin aure
2 Hikimar yin aure
3 Falalar yin Aure
4-Hukuncin yin aure
5 - Yadda ake neman aure
6 - Irin matar da ake so a aura
7- Irin mijin da ake so a aura
8- Yadda ake zuwa zance da yadda ake yi
9_ Yadda ake bincike kafin aure da abubuwan ake bincikawa guda biyar
10- Mata guda 42 da suka haramta mutum ya aure su saboda nasaba ko shan nono ko surukuta.
11 Rukunan Daurin aure.
12 - Sadaki da hukunce hukuncin sa
13 Wanene Waliyyi da sharuddan zama Waliyyi da kashe kashen waliyyai na aure
14 Sigar daurin aure da yadda ake yin ta.
15 - Shedun aure da siffofinsu.
16- Sanya sharudda a cikin aure.
17 - Yadda ake bukukuwan aure a musulunci, da aladun da suka shigo cikin aure marasa kyau. 
18- Yadda ake walima da shagalin aure.
19- Ladubban tarewar amarya da Ango.
20 Hakkokin mata akan miji
21 Hakkokin miji akan mata.
22 Ladubban kwanciyar aure
23 Abubuwan da suke kara soyayya tsakanin maaurata.
24 Yadda ake gyara matsalolin aure idan sun taso.kafin akai ga saki 
25 Abubuwan da suke kawo albarka a gidan aure
26 Abubuwan da suka halatta, da wadanda suka haramta tsakanin maaurata a lokacin da mace take al'ada
27 Abubuwan da suke kawo mutuwar aure
28 Hukuncin hana daukar ciki, ko zubar da ciki, da Tsarin iyali a musulunci.
29 Sharuddan da mutum, zai cika kafin ya kara aure.
30 Wanda ya kasa daukan nauyin iyalinsa. 
31 Hukuncin wanda ya kauracewa iyalinsa. bisa zalunci ko larura ko horo. da sanin lokacin da shari'a ta iyakan ce. 

32 Mutuwar aure, da hukunce hukuncan sa,
33 Hakkokin matar da aka saka, 
34 Wa yake da hakkin rike yaya bayan mutuwar aure? 
35 - Yadda ake kul'i (mace ta nemi rabuwa) da abubuwan da suke jawo shi. 
36- Hukuncin komai bayan saki. 
37- Idda da hukuncin ta a musulunci 
38 - Hukuncin Ila'i Rashin kusantar iyali da rantsuwa ko saka sharadi. 
39-  Hukuncin Zihari kamanta jikin mahaifiyar sa da matarsa. Ko sauran mahramansa. 
40 Hukuncin lia'ni idan mutum yana zargin matarsa da zina. 
Reno da tarbiyya tun daga daukar ciki har zuwa haihuwa da yaye, 
Hakkokin yaya akan iyaye da hakkokin iyaye akan yaya. 
41 Yadda ake Takaba idan. Miji ya mutu.

Illolin Hassada Da Maganinta - Dr Jabir Sani Maihula


1) Hassada shine mutum yaji zafin wata ni'ima da Allah yayiwa wani bawan sa, koda baiyi fatar gushewar ni'imar ba. [Ibn Taymiyya da wasu malamai]
2) Hassada halin yahudawa ce [ Qur'an 2: 109, 4:54, 48:15]
3) Hassada tana kama wanda akayiwa ita, komai imanin sa; ta kama Annabi Yusuf (A.S), kuma Allah ya umurci Annabi (S.A.W) daya nemi tasri daga sharrin mai hassada [Qur'an 113:5].

4) Karanta azkar na safe da yamma, da karanta Fatiha, da karshen suratul Bakara, da ayatul Kursiy da suratul Falaq da Nas ya na kariya da ga hassada da bala'oi [hadissai da yawa]
5) Boye ni'ima ga wadan da ka ke tsammanin zasuyi ma hassada yana kareka daga hasada ya yardar Allah [quran 12:5].

6) Annabi (S.A.W.) yahana hasada, cikin hadissai dayawa cikin su akwai [ Muslim 2559]
7) Mai hassada yana fada ne da Allah, domin Allah shi yake yin ni'ima ga wanda yaga dama, kuma Allah shiyafi sanin wanda ya cancanta. [Malamai]
8) Mai hassada kullum yana cikin bakin ciki da bacin rai wanda ba lada akai [ laa tahzan, A'ed alQarny].

9) Hadisin da ya shahara na "Hasada tana cin ayyukkan..." bai inganta ba.
10) Allah yayi mana tsari daga hassada, yasa kada muyiwa wani, kuma ya tsare mu daga masu yi mana.

Saturday 7 April 2018

Gwamna Masari Ya Yi Ganawar Sirri Da Fati Muhammad (karanta kuji)


Rahoton Katsina Post Hausa 

Shararriyar Yar fim din nan Mai suna Fati Muhammad ta je Katsina​ inda tayi wata ganawar sirri da gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari. 'Yar wasan wadda yanzu ita ce babbar jakadiyar tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar wanda yake neman tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam iyyar Adawa ta PDP.

Bincike ya tabbatar da cewa yar fim din ta kwashe kwanaki a wani otal din Katsina inda kuma wani daga cikin ma su taimakawa Gwamnan ya rika dawainiya da ita. Haka ma dai mun samu cewa daga karshe ta samu ganin Gwamnan amma babu wanda ya san me suka tattauna a tsakanin su.

Majiyar ta mu har ila yau ta bincika ta kuma tabbatar cewa ganawa bata ofis bace, shi yasa ma ba a ga Fati Muhammad din a ofis ba, amma ganawa ce ta kashin kai.
“Zuwan na Fati Muhammad Katsina yafi alaka da siyasa bana wasan fim bane.” Kamar yadda muka samu.

Domin duk ‘yan fim din Katsina babu wanda ya san ta shigo, kamar yadda bincike Taskar labarai ya tabbatar. Wani Dan fim yace zirga zirgar Fati Muhammad yanzu tafi dangantaka da siyasa fiye da harkar fim Kuma kwananan shafin ta na Facebook ya yi kaurin suna wajen sukar salon mulkin shugaba Buhari, wannan yasa ganinta a Katsina don ganin Gwamnan zai ba kowa mamaki.

Jaridar Katsina Post Hausa sun Aikawa Fati sakon wayar Hannu har zuwa rubuta rahoton nan bata bada amsa ba wani jami’in gwamnatin Katsina yace shi bai san zancen ba.

Fitsararrun 'Yan Mata Dake shigowa Sana'ar Fim Ne Ke Jawo Mana Zagi' - Jamila Nagudu


A wata hira da tayi da BBC hausa, tauraruwar fina-finan Hausa, Jamila Nagudu ta bayyana cewa wasu bata garin 'yan matane dake shigowa masana'antarsu ne daga waje ke sawa ana yi musu kudin goro ana zaginsu.

Jamila tace zaka ga yarinya ta taso a unguwa bata ganin girman iyayenta da manyan mutane kuma sai tazo masana'antar fim ta samu sa'a a dauketa To anan ma sai ta cigaba da wannan hali nata sai mutane su rika ganin kamar duk 'yan fim haka suke.

Jamila ta bayyana cewa ta taba yin aure kuma tana da da daya.

Jamila ta bayyana cewa "tana taka duk wata rawa da aka bata da kyau ne saboda sai mutum ya dage ya nuna kwazo sannan za'a kirashi jarumi, mutum ba zai taba zama jarumi ba haka kawai",

Ta kara da cewa duk wani abu da aka ga tana kuka akanshi a fim ta tabbata idan ace me kallone aka yiwa irin wannan abu to shima zai iya yin kukan.

Jamila ta kara da cewa yawanci yanzu ba sa'anta a masana'antarsu dan da yawa suna kiranta da anti ko Hajiya,

A karshe tace ta godewa Allah da irin abubuwa da daukakar da ta samu, inda ta bayyana cewa ba kowane jarumine ya samu irin abinda ta samu ba a sana'ar fim.

Me za kuce akan hakan?

Kalli Adama Indimi tare da tauraron fina-finan Amurka

Kalli Adama Indimi tare da tauraron fina-finan Amurka  

irin dan kasuwa, Adama Indimi kenan a gurin wani shagali na haduwa da mutane da aka shirya inda take tare da tauraron fina-finan Kasar Amurka, John Boyega wanda ya fito a fim din Star Wars da wasu sauran fitattun fina-finai.

Adama ta nuna farin cikin haduwa dashi

Kalli Mutum ya hadiye burushin da yake wanke baki da shi


Likitoci a kasar Kenya sun yi nasarar cire burushin wanke baki daga cikin wani mutum bayan da ya hadiye shi.

David Charo ya ce ya hadiye burushin ne bisa kuskure ranar Lahadi, lokacin da yake wanke bakinsa.

Ya shafe kwana biyar yana yawo tsakanin asibitocin yankin a kokarin da yake ne neman magani.

ibitocin sun ki karbarsa suna masu cewa ba su da kwarewar da za su iya yi masa tiyata.

Bayan da abin ya ci tura ne aka mika shi ga Dokta Ramadhan Omar a wani asibiti mai zaman kansa, wanda ya yi nasarar yi mata tiyata.

Hoton wurin da aka dauka ya nuna yadda burushin ya makale a cikin Mista Charo.

Jama'a da dama sun nuna dimuwa kan labarin a shafukan sada zumunta.

Rahatanni sun ce a yanzu Mista Charo na ci gaba da murmurewa a asibitin da ke birnin Mombasa.

Wadansu bayanai sun nuna cewa ya shafe shekara 20 yana amfani da shi.
© bbchausa.

Kalli hoton dan-dan Adam A. Zango

Kalli hoton dan-dan Adam A. Zango

Dan tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Ali, Haidar Adam A. Zango kenan a wannan hoton nashi da ya sha kyau, muna mishi fatan Alheri.

Kalli kwalliyar juma'a ta Amina Amal '

Kalli kwalliyar juma'a ta Amina Amal '

Jarumar fina-finan Hausa, Amina Amal kenan a wannan hoton nata da ya kayatar, tasha kyau, son kowa..

Kalli yanda aka yiwa wani mamaci makara me siffar Zaki

Kalli yanda aka yiwa wani mamaci makara me siffar Zaki

Wani attajirin mutum ne da ya mutu a jihar Enugu dake kudancin Najeriya aka mai makara me siffar Zaki dan binneshi da ita, lamarin dai ya dauki hankulan mutane sosai inda da dama suka bayyana hakan da almubazzaranci.

Hadiza Gabon na son yin abota da wannan kyakkyawar budurwar, gurguwa


Wannan wata kyakyawar baiwar Allah ce gurguwa da tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon tace tana son yin abuta da ita, bayan saka hoton wannan baiwar Allahn a dandalinta na sada zumunta da muhawara, mutane sunyi ta yabawa da kyawun da Allah ya mata..

Kuma itama ta cewa Hadizar tuntuni dama ita abokiyartace saidai yanzu abutar tasu zata yi karfi su shaku.
Muna musu fatan Alheri

Kalli yanda wani Ango ya bayar da Amaryarshi

Kalli yanda wani Ango ya bayar da Amaryarshi

Wannan hoton wani Angone da Amaryarshi a gurin bikinsu da Angon ya zage yana cin abinci da hannu, irin yanayin fuskar Amaryar da alama bataji dadin abinda ya faru ba, irin ya bayar da ita dinnan.

Hoton ya dauki hankula.

Saidai ko a gaskene kokuwa shirin fim ne shine be bayyana ba amma ya kayatar.

Salman Khan zai yi shekara 5 a gidan yari saboda kashe dabbar daji da yayi shekaru 20 da suka gabata

Salman Khan zai yi shekara 5 a gidan yari saboda kashe dabbar daji da yayi shekaru 20 da suka gabata: Ya zubar da hawayen nadama

Wata kotu a kasar India ta yankewa jarumin fina-finan Bollywood Salman Khan, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar saboda ya yi farautar gwanki da ba kasafai ake samunta ba ba bisa ka'ida ba.

Kotun, wadda ke zamanta a Jodhpur, ta kuma ci tarar jarumin rupee 10,000 kwatankwacin dala 154. Salman Khan dai ya kashe wasu nau'in gwanki da ake kira blackbucks guda biyu a yammacin jihar Rajasthan a yayin da ake daukar fim din Hum Saath Saath Hain a shekarar 1998.

Kotun dai ta wanke sauran jaruman da suka fito a fim din tare su hudu.

Jarumin mai shekara 52, zai iya daukaka kara a kan hukuncin da kotun ta yanke masa.

Rahotanni sun ce dole ne Salman Khan ya zauna a gidan yari na wasu kwanaki.

Wannan ne dai karo na hudu da ake shigar da karar jarumin a kan farautar dabbobi a lokacin da ake daukar fim dinsa na Hum Saath Saath Hain a shekarar 1998.

An wanke shi a kararraki ukun da aka shigar a baya.


A shekarar 2006, wata kotu ta tuhumi jarumin da laifuka biyu na farauta, inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar.

To amma da shekara ta zagayo, wata babbar kotu a Rajasthan, sai ta yi watsi da hukuncin.

Ainahin shari'ar dai al'ummar yankin Bishnoi ne wadanda suke bauta wa dabbar da ya yi farautar ne suka shigar da ita.
Gwamnatin kasar dai ta daukaka kara a kan wanke jarumin a kotun koli.

An dai tuhumi jarumin da wasu mutum bakwai da kisan dabbobin daji da suka hada da gwanki a arewacin jihar Rajasthan.

Ya matsayin Salman Khan ya ke a India?
Salman Khan, na daya daga cikin jaruman Bollywood da suka yi fice, da kuma farin jini a wajen jama'a, ba ma a kasar kadai ba, har ma da wasu kasashen duniya.

Jarumin ya fito a fina-finai fiye da 100.
An fi sanin jarumin da fina-finan soyayya da ma na fada.

Ya kuma samu lambobin yabo da dama.
Sama da mutum miliyan 36 ne suke binsa a shafinsa na Facebook, inda ya ke da mutum miliyan 32.5 a shafinsa na Twitter.

Tausayin da aka ce ya ke da shi ga jama'a musamman tsofaffi da marayu, ya kara masa farin jini musamman a wajen

talakawa.
bbchausa.

Wasu kafafen watsa labarai na kasar Indiya sun ruwaito cewa Salman Khan ya zubar da hawayen takaici da nadama bayan da kotu ta bayyana hukuncin dauri da tara a gareshi.

Haka wasu mata biyu 'yan uwanshi dake cikin kotun suma sun rushe da kuka dan taya dan uwan nasu alhini.

Lauyanshi dai ya daukaka kara zuwa yanzu

Kyan da ya gaji ubansa: Dan Adam A. Zango ya zama mawaki

Kyan da ya gaji ubansa: Dan Adam A. Zango ya zama mawaki

Hausawa na cewa kyan da ya gaji ubansa, haka ta faru da dan tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Ali, Haidar Adam A.

Zango ya shirya wakoki guda biyu kamar yanda ya bayyana, ya kara da cewa kwanan nan zai sakesu.

Mahaifinshi dai Adam A. Zango shima sanannen tauraron fina-finan Hausane kuma mawaki.

Kalli inda ruwa kala biyu suka hadu a wani bangaren Najeriya

Kalli inda ruwa kala biyu suka hadu a wani bangaren Najeriya

Wannan wani kayataccen hotone inda ruwa kala biyu suka hadu, hoton yayi kyau.
Punch.

Kalli yanda wani limamin addinin gargajiya ke sawa jarirai Albarka a kasar Indiya

Kalli yanda wani limamin addinin gargajiya ke sawa jarirai Albarka a kasar Indiya

Wannan hoton ya nuna irin yanda wani limamin addinin gargajiya yake sakawa jarirai Albarka kenan ta hanyar takasa su da kafarshi a wani yanki na kasar Indiya kamar yanda kafar Aljazeera ta ruwaito, lallai Allah daya gari ban-ban.

An Bayarda Belin Salman Khan


Wata kotu a kasar India ta bayar da belin jarumin fina-finan Bollywood Salman Khan, wanda ta yanke wa hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari.

 Ranar Alhamis Din Da Ta Gabata ne kotun ta yanke wa jarumin hukuncin bisa samunsa da laifin yin farautar gwankin da ba kasafai ake samunsa ba, ba bisa ka'ida ba.

Kotun, wadda ke zamanta a Jodhpur, ta kuma ci tarar jarumin rupee 10,000 kwatankwacin dala 154.

Salman Khan dai ya kashe wasu nau'in gwanki da ake kira blackbucks guda biyu a yammacin jihar Rajasthan a yayin da ake daukar fim din Hum Saath Saath Hain a shekarar 1998.

Kotun dai ta wanke sauran jaruman da suka fito a fim din tare su hudu.

Tun da fari dai, lauyan jarumin mai shekara 52, ya gabatar wa kotun hanzarin mutumin da yake Wakilta A cewarsa, daurin shekara biyar zai haifar da koma-baya a sana'arsa ta fim.

Rahotanni sun ce dole ne Salman Khan ya zauna a gidan yari na wasu kwanaki.

An Yanke Wa Jarumin Bollywood Salman Khan Hukunci Shekara Biyar A Gidan Yari

Al-Mustapha Ya Bayyana Yanda Anka Kashe sani Abacha

Al-Mustapha Ya Bayyana Yanda Anka Kashe sani Abacha

Ya ce tun ranar wata lahadi bakwai ga wata shida na shekarar alib dubu daya da Dari Tara da casa'in da takwas (7-6-1998) lokacin da Tsohon Shugaban kasa Sani Abacha ya gaisa da wani daga cikin masu tsaron shugaban kasar Palestine Yaseer Arafat a filin sauka da tashi na jirgin sama dake babban birnin tarayya Abuja hada hannun su keda wuya shikenan yanayin tsohon shugaban kasar ya canja
Tsohon mai tsaron lafiyar,

 tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha yayi karin haske akan yadda shugaban nasa ya rasa ran shi. Hamza Al-Mustapha ya karyata zacen da ake na cewar wai Abacha Tufa (Apple) yaci ya mutu.

Ya ce tun ranar wata lahadi bakwai ga wata shida na shekarar alib dubu daya da Dari Tara da casa'in da takwas (7-6-1998) lokacin da Tsohon Shugaban kasa Sani Abacha ya gaisa da wani daga cikin masu tsaron shugaban kasar Palestine Yaseer Arafat a filin sauka da tashi na jirgin sama dake babban birnin tarayya Abuja hada hannun su keda wuya shikenan yanayin tsohon shugaban kasar ya canja.

Da gari ya waye likitan da yake duba shi yazo yayi mishi Allura ya kuma bashi shawara akan ya samu ya kwanta ya dan huta, da misalin karfe 9 na dare baki suka fara shigowa wurin shugaban, wanda ya shigo daga karshe shine Janar Jeremiah Timbunt Usteni wanda a lokacin shine ministan Abuja, sunyi ta hira dashi har zuwa karfe 3:35 na dare.

Da misalin karfe biyar 5 na Asuba sai daya daga cikin masu tsaron gidan shugaban kasar ya rugo a guje gidana yace maigida yana cikin wani hali mai ban tsoro saboda haka in zo ana bukatar gani na cikin gaggawa,

 a wannan lokacin sai nayi tunanin ko dai ana so ayi mana juyin mulki ne? Sai nace wa matata taje ta dauke wa Sojan hankali tace ya jira ni, ni kuma sai nabi ta kofar baya na je inda shugaban kasar yake; ina zuwa sai na tarar dashi yana Huci, numfashin sa na fita sama-sama,

 a lokacin bazai yiwu in taba shi ba kamar yadda tsarin dokar aikin mu yake. Banyi kasa a gwiwa ba sai naja da baya na kame na kwala mishi kira da karfi da nufin ya bani dama in taba shi, sau biyu ina yin haka amma baice dani komai ba.

Daga wannan lokacin sai na gane akwai babbar matsala sosai nan da nan na kira babban likitan shi Dakta Wali ya bayyana a cikin mintuna da basu wuce 8 ba, take ya yiwa maigida Allurori guda biyu daya a kirji shi daya kuma a kusa da wuya shi; ba a jima ba Likitan ya bayyana mini cewar gaskiya sai dai muyi hakuri domin maigida ya riga mu gidan gaskiya.

Daga wannan lokacin na umarci Dakta Wali ya jirani naje gidana don shirya wa dukkan matsala da zan iya fuskanta saboda mutuwar maigidan. Saboda haka a zance na gaskiya babu wata magana dake nuna cewar Tsohon Shugaban Kasa Sani Abacha guba yaci a Apple ya mutu; inji Manjo Hamza Al-Mustapha.
Sources :naij.com

Al-Mustapha Ya Bayyana Yanda Anka Kashe sani Abacha


Ya ce tun ranar wata lahadi bakwai ga wata shida na shekarar alib dubu daya da Dari Tara da casa'in da takwas (7-6-1998) lokacin da Tsohon Shugaban kasa Sani Abacha ya gaisa da wani daga cikin masu tsaron shugaban kasar Palestine Yaseer Arafat a filin sauka da tashi na jirgin sama dake babban birnin tarayya Abuja hada hannun su keda wuya shikenan yanayin tsohon shugaban kasar ya canja
Tsohon mai tsaron lafiyar,

 tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha yayi karin haske akan yadda shugaban nasa ya rasa ran shi. Hamza Al-Mustapha ya karyata zacen da ake na cewar wai Abacha Tufa (Apple) yaci ya mutu.

Ya ce tun ranar wata lahadi bakwai ga wata shida na shekarar alib dubu daya da Dari Tara da casa'in da takwas (7-6-1998) lokacin da Tsohon Shugaban kasa Sani Abacha ya gaisa da wani daga cikin masu tsaron shugaban kasar Palestine Yaseer Arafat a filin sauka da tashi na jirgin sama dake babban birnin tarayya Abuja hada hannun su keda wuya shikenan yanayin tsohon shugaban kasar ya canja.

Da gari ya waye likitan da yake duba shi yazo yayi mishi Allura ya kuma bashi shawara akan ya samu ya kwanta ya dan huta, da misalin karfe 9 na dare baki suka fara shigowa wurin shugaban, wanda ya shigo daga karshe shine Janar Jeremiah Timbunt Usteni wanda a lokacin shine ministan Abuja, sunyi ta hira dashi har zuwa karfe 3:35 na dare.

Da misalin karfe biyar 5 na Asuba sai daya daga cikin masu tsaron gidan shugaban kasar ya rugo a guje gidana yace maigida yana cikin wani hali mai ban tsoro saboda haka in zo ana bukatar gani na cikin gaggawa,

 a wannan lokacin sai nayi tunanin ko dai ana so ayi mana juyin mulki ne? Sai nace wa matata taje ta dauke wa Sojan hankali tace ya jira ni, ni kuma sai nabi ta kofar baya na je inda shugaban kasar yake; ina zuwa sai na tarar dashi yana Huci, numfashin sa na fita sama-sama,

 a lokacin bazai yiwu in taba shi ba kamar yadda tsarin dokar aikin mu yake. Banyi kasa a gwiwa ba sai naja da baya na kame na kwala mishi kira da karfi da nufin ya bani dama in taba shi, sau biyu ina yin haka amma baice dani komai ba.

Daga wannan lokacin sai na gane akwai babbar matsala sosai nan da nan na kira babban likitan shi Dakta Wali ya bayyana a cikin mintuna da basu wuce 8 ba, take ya yiwa maigida Allurori guda biyu daya a kirji shi daya kuma a kusa da wuya shi; ba a jima ba Likitan ya bayyana mini cewar gaskiya sai dai muyi hakuri domin maigida ya riga mu gidan gaskiya.

Daga wannan lokacin na umarci Dakta Wali ya jirani naje gidana don shirya wa dukkan matsala da zan iya fuskanta saboda mutuwar maigidan. Saboda haka a zance na gaskiya babu wata magana dake nuna cewar Tsohon Shugaban Kasa Sani Abacha guba yaci a Apple ya mutu; inji Manjo Hamza Al-Mustapha.
Sources :naij.com

Friday 6 April 2018

An Yanke Wa Jarumin Bollywood Salman Khan Hukunci Shekara Biyar A Gidan Yari

An Yanke Wa Jarumin Bollywood Salman Khan Hukunci Shekara Biyar A Gidan Yari


Wata Kotu a Kasar Indiya ta yankewa shahararen jarumin finan-finan Indiya Salman Khan hukuncin zaman shekaru biyar a gidan yari saboda laifin kashe wasu dabobi wadanda basu da yawa a duniya a wata farauta da yayi.

Lauya mai shigar da kara, Mahipal Bishnoi ya shaidawa manema labarai a birnin Rajasthan da ke Jodhpur cewa: "Kotu ta yanke ma Salman Khan hukuncin shekaru biyar a gidan yari da kuma tarar rupees 10,000 ($150)."

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Lauyan ya cigaba da cewa a yanzu ana shirye-shiryen kama jarumin mai shekaru 52 a duniya don tisa keyar sa zuwa gidan yari na garin Jodhpur.

Sai dai Salman Khan ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa dashi kuma yana da damar daukaka kara a wata kotun.

'Yan'yan Rabi'u Rikadawa sunyi saukar Qur'ani


A yaune 'Ya'yan tauraron fina-finan Hausa, Rabi'u Rikadawa, Fatima da Al-Amin sukayi saukar karatun Qur'ani a makarantar Isilamiyarsu, Mahaifin nasu ya saka hotunan 'ya'yan nashi yana tayasu murna.

Muna musu fatan Allah yasa karatun nasu ya amfanesu da sauran Al'umma baki daya.


Kannywood: Shararriyar jaruma Maryam Booth ta rabawa marayu kayan sallah

             
  Image © Mujallarmu.Com

Jaruma Maryam Booth tayi rabon kayan sallah ga marayu kananun yara maza da mata a Nasarawa dake kano,jarumar ta raba shaddoji da yadika masu din ki da ado na zamani.

Dandalin Arewafresh.com ta samu labarin cewa awajen rabon ne wakiliyar majiyar mu Maryam Hotoro ta sami sukunin

 zantawa da jarumar kamar haka:
Maryam kin rabawa marayu kayan sawa, kuma da alamu wadan nan yara marayune, wanne hange ki kayi wanda yasa ki ka rabawa marayu kayan sallah amadadin ki ba masu iyaye? Wannan

 tambaya tana da saukin amsawa.
Domin amsarta yana cikin tambayarki. Duk yaron yake da iyaye to tabbas yana da tabbacin samin kayan sallah, amma maraya bashi da tabbas.

Dan haka naga gwara in ba marayu zaifi kyautuwa.

Me za kice da yan uwanki jarumai akan irin wannan abin alkairi da ki ki gudanar a yau? Abinda zance shine, su ma Allah ya basu ikon gudanar da wannan abin alkairi.

Duk da yake da yawan jarumai maza da mata suna irin wannan abin alkairin, nima da wasu nayi koyi irinsu A Zango, Sani Danja, Ali Nuhu.